mujallar bidiyo - yuli/agusta 2001

45
BIDIYO Yuli/Agusta 2001

Upload: dinhhanh

Post on 08-Dec-2016

1.612 views

Category:

Documents


3 download

TRANSCRIPT

Page 1: Mujallar Bidiyo - Yuli/Agusta 2001

BIDIYO Yuli/Agusta 2001

Page 2: Mujallar Bidiyo - Yuli/Agusta 2001

BIDIYO Yuli/Agusta 2001

BidiyoYuli/Agusta 2001

---------------------------------------------------------------Edita: Ashafa Murnai Barkiya

Manazarta: Halima Adamu Yahaya, Ali Kano, Musa Gambo,Mohammed Nasir, Bashir Yahuza, Danjuma Katsina, Bashir

AbusabeHotuna: Bala M. Bachirawa

Jami’ar Kasuwanci: Jamila MohammedAna shiryawa da bugawa wata biyu-biyu a kamfaninInformart, Hadiza House, 2nd Floor (Concern Office),

Zaria Road by Dangi Roundabout, Kano, NigeriaP.O. Box 10784, Kano

E-mail: [email protected] mallaka (m) Informart

Hotunan da ke bango, godiya ga: Sarauniya Films, FKDProductions, da Zik Entertainment. Tsara Bango: Sanusi BurhanDaneji, City Business Centre, Kano

M A N U F A R M U

furodusoshin finafinai) mujallar Bidiyo madubi cea wurinsu.

Saboda bunkasar finafinan Hausa aka ga yadace wannan mujalla ta ba da tata gudummuwata hanyar isar da sako ga jama’a. A cikin wannanfitowa masu karatu za su debe kewa ta hanyarkaranta sharhin wasu daga cikin finafinan da sukafito a watan da ya gabata.

Akwai kuma takaitattun bayanai dangane dawasu daga cikin finafinan da ba su fito ba, ammasuna kan hanya. Masu karatu za su ji dadin karantawasu labarai na abin da ke wakana a wurin daukarshirin wasu finafinai (wato location a Turance).

Dadin dadawa kuma, Bidiyo ta yi kokarin fitoda wasu wakokin finafinai don jin dadinku. Gawanda ya gaji da karatu, sai ya bude shafinmu nabata-hankalin dare domin ya wasa kwakwalwarsa.

A karshe ya kamata musamman furodusoshi dadaraktoci su fahimci cewa duk wani sharhi da akayi a kan wani fim, an yi shi ne da zuciya daya, danufin kawo gyara.

Muna so masu karatu su aiko mana da ra’ayinsua kan irin wannan mujallar. Shin ta dace? In tadace, ina suke ganin ya kamata a gyara? Munamaraba da wasiku wadanda za su sa mu a hanya,ko wadanda za su yi tsokaci a kan wani fim damutum ya kalla, har yake ganin yana da ra’ayi akai.

Ita wannan fitowar tamu, ta farko ce. Shi kuwako me aka fara shi, kila a ga wata kasawa a cikinsa.Muna tabbatar muku cewa za mu ci gaba da ingantamujallar a kowace fitowa, tare da taimakon Allah.

DAGA TEBURIN EDITA

Ashafa

Assalamu alaikum.Wannan sabuwar

mujalla mai suna Bidiyotana dauke ne da wasumuhimman bayanai daza su iya kara haskakawa mai karatu hanyarshiga cikin duniyarfinafinan Hausa. Sukansu wadanda ke cikinduniyar (wato ’yan wasa,ma’aikata, daraktoci da

1

KU ZO MU GINA WANNAN MUJALLAR!Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin {ai.Wannan mujalla ba}uwa ce. Sabuwa ce gal. Wannan

shi ne bugunta na farko. Ta fito tare da addu�a da kumafatan ta ci gaba da fitowa a bayan kowa]anne watannibiyu.

Maganar da take }unshe da ita, ba ba}uwa ba ce.Tatsuniyar Gizo dai ba ta wuce ta {o}i. Mujallar Bidiyo,kamar yadda sunanta ya nuna, za ta ri}a gabatar da sharhine da wasu �yan bayanai a kan shirin fim, musamman mana Hausa. Amma fa kada a ]auka kamar sauran mujallumasu ba da labaran shirin fim take. A�a, ita za ta bambantada su ta fuskar al}iblarta da tsarinta. Yayin da sauransuke }o}arin ba da labarai na abubuwan da ke wakana afagen fim (wato misali idan an yi wani taro, ko wani ya yiaure, ko wata ta ce abu kaza, da sauransu), ita Bidiyo za tafi ba da }arfi ne ga su kansu finafinan, ba masu yin su ba.Wato za ta ri}a yin tsokaci a kan yadda ake shirya fim, dafinafinan da aka yi ba su fito ba, da wa]anda suka fito, dawata siga da suke da ita.

A wajen sauke wannan nauyi, za ta ri}a fa]a wa maikaratu yadda aka yi wani fim da yake kallo, da labaranwasu abubuwa da suka faru a wurin shirya fim ]in.Sa�annan akwai sharhi da ra�ayoyi a kan finafinan dasuka fito kasuwa har aka kalle su. Sa�annan za mu ri}ayin karambanin nuna wa masu shirya fim yadda ake shiryafim a }asashen da suka ci gaba, don su kwaikwayi waniabu, su gyara aikinsu, tunda an ce da na-gaba ake ganezurfin ruwa. Burinmu shi ne a kalli mujallar Bidiyo amatsayin �yar jagora ga �yan fim da �yan kallo. Dominkuwa za ta ri}a bayyana yadda ya dace mai shirya fim(walau furodusa ne ko darakta ko ]an wasa) ya shirya fim]in, kuma ta shawarci mai kallo a kan fim ]in da ya daceya kalla don ya more ku]insa da lokacinsa, ya ilimantuko ya wa�azantu.

Mun san wannan aiki ne wurjanjan, mun kuma sancewa aikin yana bu}atar }warewa kafin a yi shi. Duk dahaka, za mu dogara da ]an ilimin da Mai-duka ya ba mua wannan harka ta aikin jarida da nazarin fim, tare da abumafi muhimmanci � wato taimakon Allah � wajen yinaikin. Za kuma mu dogara ga su wa]anda za mu yi waaikin, wato ku masu shirya fim da ku masu kallon fim,wa]anda ku ne muke son ku karanta wannan mujalla aduk lokacin da ta fito.

Mun }udiri aniyar ba za mu gaza ba. Ba za mu ba dakunya ba, insha Allah. Don haka muke fatan za ku ha]akai da mu don ganin mun gina mujallar har ta bun}asa.Yanzu dai mun share fili, mun sa harsashi, mun ]ora bulo.Sai ku zo a yi aikin ginin tare da ku.

Muna sane da cewa akwai mujallun da kuke karantawadon samun labarai a kan abubuwan da ke faruwa a fagenfim na Hausa. To amma a cikin ido ake tsawurya. ItaBidiyo dai ta bambanta da su. Duk da yake dai fitowarmuta farko ta gwaji ce, za ta iya nuna maka inda mukafuskanta. Tunda kuwa an ce Jumma�ar da za ta yi kyautun daga Laraba ake gane ta, kila da wannan fitowar afahimci cewa wannan Larabar mai kyau ce. Bu]ewa]annan shafukan ka gani. Bambancin a bayyane yake.

Sai mun ha]u a fitowarmu ta gaba.

Page 3: Mujallar Bidiyo - Yuli/Agusta 2001

BIDIYO Yuli/Agusta 2001

finafinai a kasuwa. Manyanfurodusoshi da ke kushe chamama

ra�ayinsu ne,amma ni ban gawata illa gachamama ba. Inason ta, ina kumagoyon bayanchamama, inakuma fatar alheri

ga masu yin ta.� Shi ma Hafizu, ya ta~ayin chamama. A haka daraktan ya kadabaki ya ce da gaske yana taimaka wamasu yin ta inda ya bayyana misali dafim ]in Aikata Alheri.

Shi kuwa Aminu Shariff, ya ce masukushe chamama suna yin kuskure ne. Ara�ayinsa, ba chamama ne matsalar ba.�Inda Gizo ke sa}ar shi ne cunkosonda ake samu na finafinai a kasuwanni,domin a rana ]aya sai a fitar da fimhu]u zuwa biyar. Wannan ne matsalar,ba chamama ba. Ba ruwan chamama.Domin chamama nawa ke yin nasara tabar finafinan da ake gani za su yi waniabu?�

A ganin Momo, shi fim sa�a ce dagaUbangiji. �Ko da chamama ko bachamama idan Allah ya yi za ka samu,za ka samu. Idan ko ba haka ba komilyan nawa ka kashe ba za ka samuba. Domin kowa rabonsa yake ci.� Yace ai ko chamamar ma gware suke yi dajunansu kamar yadda manyan finafinaike gware da juna, sannan kuma ko amanyan finafinan ai akwai wa]andaake kira chamama. �Domin akwai wanifim da ya fito kwanan baya da ake cewachamama ce, amma ya zama zakarangwajin dafi,� inji shi.

Bincikenmu ya nuna cewa da wuyaa samu wanda ke tallafa wa harkarchamama kamar Aminu Shariff. A kanwannan cewa ya yi, �Akwai mutane dadama; ni kaina na ba da ku]i suka yichamama, na taimaka masu suka samujari. Sannan kuma da yawa ni ke rubutamasu labaran, musamman na bandariya,� inji Momo.

A kan kome ya sa furodusoshiirinsa ba sa sanya sunan kamfanoninsuidan suka yi chamama, sai Aminu yace, �Yawanci, kamar yadda na fa]amaka, taimaka masu muke yi domin}anana da ke shigowa harkar ba su daku]in da za su iya yin manyan finafinai.Amma suna da sha�awar yin. To sunabu}atar taimako, domin duk wani maiyin chamama burinsa ya yi babban fimsai dai matsalar ku]i. Ba ma sa sunankamfaninmu ne. Saboda finafinan banamu ba ne, taimako kurum muke

R A H O T O

Ibro sarkin chamama ... cikin shirin Tabin Aljan

SHIN Fim [inChamama naBarazana ga

Manyan Furodusoshi? A duniyar finafinan

Hausa, wannan tambayartana da muhimmanci,musamman a wannanzamanin inda finafinaisamfurin chamama suketa }ara }arfi. Ita daikalmar chamama, tananufin irin finafinan Ibroko na Wudil wanda akekashe ku]i ka]an a yi sucikin }an}anen lokaci.Yawanci suna ba dalabaran karkara ne; babumotoci da gidaje masutsada. Wasu sun ]aukiirin wa]annan finafinankwashi-kwaraf, sunacewa ba su da inganci. Arana ]aya ana iya gamairin wannan wasa, akasin sauranfinafinai wa]anda akan kwashi makoguda ana ]aukarsu.

Binciken mujallar Bidiyo ya ganocewar mutane ke ba da ku]i su Ibro kowasu dillalan Ibro su ]aukar masu fim]in chamama su ba su kaset ]in.Binciken ya kuma nuna irin wa]annanmutanen ba sa yarda sa sunansu kosunan kamfanin da aka san su da shi.Menene ainihin matsalar chamama?Kuma yaya za a yi a gyara al�amarin?Amma kafin nan, menene chamama aidon furodusoshi?

A kan wannan, darakta/furodusanfinafinan Jumur]a da Dijangala dakuma wani da zai fito kwanan nan maisuna Hauwa, Sir Hazifu Bello, cewa yayi, �Abin da ake nufi da chamama bawai fim ]in Ibro ba ne, ana nufin fim]in da aka kashe ma }aramin ku]i.�

Shi kuma furodusan fim ]in U}ubada wani mai fitowa nan gaba ka]an,Taqidi, ]an wasan da tauraronsa ke

haske a yanzu, Aminu Shariff (Momo),ya ce wasu sukan ]auki chamama ne akan fim wanda aka shirya da ku]i}alilan, yayin da wasu ke ganinsa a fim]in da babu �yan wasa manya manya acikinsa ko kuma wanda ba a samumanya-manyan abubuwan daingantaccen fim ke bu}ata ba. Watauma�ana fim ]in da aka yi wa maneji. Akan }orafin rashin sa sunan kamfanoninasali a kwalin fim ]in chamama kuwa,Hafizu ya ce, ko a sa ko kar a sa, kashicasa�in cikin ]ari na furodusoshin Kanoda chamama suka fara. Hafizu, wandamagoyin bayan chamama ne, ya ce idanaka duba tarihin fim a duniya, kafin fim]aya babba ya fita sai }anana goma sunfito. Saboda haka su masu yinchamama, a cewarsa, kamar makoya ne,�kuma ba domin makoyi ba da gwaniya ji kunya.�

Shawararsa a kan wannan ita ce:�Bai kamata a }i jinin chamama ba, saidai yaya za a gyara tsarin fito da

2

M E C E C E I L L A R F I N A F I N A N

Page 4: Mujallar Bidiyo - Yuli/Agusta 2001

BIDIYO Yuli/Agusta 2001

Sir Hafizu Bello Aminu A. Shariff (Momo) Ibrahim Hassan Adamu

3

badawa.� A kan ko chamama na dakushe}arfin manyan finafinai, Momo ya ce,�Duk wani furodusa da ya ce chamamana dakushe harkar shirin fim a Kano,}arya yake yi, sai dai hassada da ba}inciki. Ko kuma gunagunin cewa shi maichamamar ya fi shi samun alheri.�

Daga }arshe ya yi kira ga masu}orafin da su lura da cewa shi chamamakumfar omo ne, domin tsawon lokacinda yake yayi }arami ne, ba kamarbabban fim ba wanda sai a yi shekarama ana cin gajiyarsa. Ya ce yadda dukchamama ya ha]u ba ya wuce wata ]ayako biyu ana cin kasuwarsa.

Ra�ayin furodusan Ragayar Dutse(wanda ba chamama ba ne), wato BalaAhmed, ya bambanta da na sauranwa]anda suka gabata, domin in dadominsa ne, to da ya yanzu an dainachamama kwatakwata. A ganinsa, abintaikaici ne yadda duniya ake ci gabada sauri a kan harkokin rayuwa a ceana sai da irin wa]annan finafinai. Yace ba wai yana nufin a daina fim ]in}auye ba. A ra�ayinsa, kamata ya yi a cean tsaya ana tsara fim ana yin shi dajigo mai ma�ana wanda zai koyar dawani darasi. �Yaya za ka ]au kyamaraka fara shooting ranar Asabar zuwaLahadi ka ce ka gama har kuma ka kirashi fim?� Ya yi tambaya. A ra�ayinfurodusan, yana so ne ya ga cewa munkai matsayin lokacin da in ka yi fim yazama na kamar wanda ya gama gini neko kuma wani gagarumin aiki. �Ina soin ga cewa mun kai lokacin da in kagama za ka kirawo manya-manyanmasana harkar a zo a gani a ba dashawarwari sannan ka zo ka ha]a party,musamman na fim ]in, domin ka cimmawani buri mai girma a wajenka. Hakaake yi a duk }asashen da suka ci gaba,�

inji shi. Haka kuma Bala ya yi tir da

wa]anda ya kira �marasa kishin cigaban sana�ar fim da ke sayenchamama� amma sai su }i sanya sunankamfaninsu in za su fito da fim ]in akasuwa. �Ka ga wannan laifi ne kenanhar ga Allah. Kuma kamar mai sayar datumatir ne wanda yake sayar da ru~a~~ega jama�a ko kuma mutumin da ke algusa kan abin da yake sayarwa.� Ya }arada cewa duk wani fim, ko a ina aka yishi, in har ba ya ilimantarwa, to sunansachamama.

Furodusan ya danganta chamamaga ]aya daga cikin ummul-haba�isindakatar da fim a Jihar Kano kwananbaya �domin ana yin su ne cikingaggawa ba tare da tsari ba, har ma takai abin ya yi yawa ana sa wasu ]abi�umarasa kyau a ciki baya ga illar jawocushewar finafinai a kasuwa da take yi.�

Shi kuwa Alh. Jibrin Mohammedna El-Duniya, wanda kamfaninsa ya yifinafinai da dama da ake yi ma kallonchamama da suka ha]a da Gani GaWane, Dadaron Ibro, Ba a Ba Ka Labari,Rashin Sani, da sauransu, cewa ya yishi fim sa�a ne kuma kamar man fetur akasuwar duniya, daraja-daraja ne.�Saboda haka kowa ne fim da darajarsa;in mutum ya yarda da kansa ba ya jinkome.�

Hamsha}in dillalin kaset ]in nan,Alh. Musa Na Saleh, ya musanta zargincewa yana yin chamama. Amma yabayar da tabbacim cewa yana taimakawa wasu masu yin chamama, wato abinda za ka iya gani a matsayin �an }i cinbiri an ci dila.� �Domin da haka ne zasu zama manyan furodusoshi.� Ara�ayinsa chamama ba ta da watabarazana ga manyan furodusoshi.

Da aka tuntu~i Alh. Hassan Adamudomin jin ta bakinsa dangane da ra]e-ra]in da ake yi cewa shi ma ya yi irinwa]annan finafinan na chamama, maimagana da yawunsa, ]ansa Ibrahim yamusanta zargin, ya ce ya zuwa yanzuba su yi fim ko da }waya ]aya ba.�Amma muna da niyyar yin fim nakanmu shekara mai zuwa in Allah Yakai mu,� inji shi.

Furodusan A�isha na Iyan Tamakuwa, watau mutumin da ake kiraDokta, cewa ya yi wata sa�a hali kesanya a yi chamama. Sai ya ce ammashi bai ga wata barazana da chamamake kawo wa su manyan furodusoshi ba,duk da cewa shi ma ya ta~a jarrabachamama.

Bala Anas, darakta kuma furodusanfim ]in Kallo Ya Koma Sama da wanisabo da zai fito, wato Salma-SalmaDuduf, cewa ya yi bai ga wata illa dachamama za ta iya yi wa manyanfurodusoshi ba, �Sai dai domin tanacunkushe kasuwanni kawai.� Kumahanyar fita a ganinsa ita ce a }ayyadefitar finafinai barkatai.

Shi kuwa wani mai harkar fim wandaya nemi a sakaya sunansa cewa ya yi,�Chamama ba ya koyar da komai saishashanci, shirme da rashin ]a�a.� Yanamai bayar da misali da Jahilci Ya FiHauka, wanda ya ce bai kamata a cefim ne da za a kalla a al�ummar }waraiba. �Ko a cikin �yan wasa ba kowa neke ra�ayin chamama ba.�

Bincikenmu ya gano cewa chamamatana da duniyarta, domin tana damarubuta labaranta, da furodusoshinta,da daraktocinta, da �yan wasanta. Wasusukan shiga manyan finafinai, to ammaakwai wasu, irin su Hajiya JamilaHaruna, wa]anda ba sa shiga chamama.

kashi 90 cikin dari na furodusoshin Kano da chamamasuka fara – Hafizu Bello

Page 5: Mujallar Bidiyo - Yuli/Agusta 2001

BIDIYO Yuli/Agusta 2001

suke yi. Wannan shi ne ya sanya mu mamuke ]aukar shirinmu a }auye damuhalli irin na karkara domin irinhakan ne al�adarmu, abin da muka gada,da shi muke alfahari. Kuma mu Indiyamuka sani da wa}e-wa}e da raye-raye.Kuma mu kanmu Hausawa akwai wa}e-wa}enmu na gargajya, akwai raye-rayenmu. Saboda haka a finafinamu zaka ga wa}o}inmu; in ta kama mu yi daraye-rayenmu za ka ga na gargajiya ne.

Bidiyo: Wasu na ganin finafinannaku na chamama ba su da ingancisosai.

Ibro: E to, wanda ya ]auki finafinanchamama a matsayin marasa inganci shine bai san abin da yake yi ba. Ina kiraga jama�a da idan mutum bai fahimciabin da muke nufi a finafinanmu da akece wa chamama ba, to ya je ya kai watsofaffi su gani. Za su san mun tunamasu wani abu a baya. Mu munala�akari da al�ada tagari ta Bahaushene, irin wadda har yanzu ake yi a mafiakasarin karkararmu. Wannan ban yitsammanin abin barazana ne ga kowaba.

Ita Jamila, ta kira chamama a matsayinfim ]in gan]e-gan]e ne, ta ce, ita ba tayin chamama.

Ko ma yaya ta kaya, chamama daiga alama ba za a bar yin ta ba yanzudomin akwai ]imbin masu ra�ayinta akarkara, wata}ila domin tana nuna irinyadda rayuwarsu take. Su kuma masuyin ta sun fi gane mata domin ko bakomai, ba ta da wuyar ha]awa dominmasu yin ta ha]e suke guri ]aya, kumaba ta bu]atar wurin location mai tsada.Hasali ma dai kamar diramar da~e ce.

To yadda dai ta kaya kenan tsakanin

masu so da masu kushe chamama dominkamar yadda Hausawa kan ce ne, da maibara da mai tashe duk tsaba suke nema.Don haka, bisa dukkan alamu, za muiya cewa harkar finafinan chamama tazauna da gindinta ganin cewa wasumasu kushe abin su ne kuma keaikatawa a ~oye. Bugu da }ari kuma,su masu sayar da kaset babu ruwansuda yawan ku]in da ake kashe wa fimkafin ya fito. �Mu aikinmu shi ne musayar da kaset. Ba ruwannmu dachamama ko wanda ba chamma ba.�Haka wani mai sayar da kaset ya fa]a.

Dukkansu dai kuma wasu na ganintun da don riba ake, to babu dalilin yinnukura da juna. Su kuwa �yan kallo,babu ruwansu, wanda duk ya fitakasuwa idan ya yi kyau sai su saya.

Irin wannan ra�ayin ya yi daidai dana Nasiru Muhammad Muduru, wandake sayar da kaset na rukoda a kasuwar{ofar Wambai da ke Kano. A nasara�ayin, su �yan kallo ne, watau baburuwansu da irin wu}ar da mutum ya yiyankansa. Kowa ya yi yanka za su ci,muddin ya yi Bismilla.

Don haka �yan chamama sai gu]a.

Muna la�akari da al�ada tagari ta Bahaushe ne

Bidiyo: Jama�a, musamman manyanfurodusoshi, suna ganin finafinanku nachamama suna barazana ga manyanfinafinai wa]anda ake kashe wama}udan ku]i. Shin da farko dai mamenene sirrin chamama?

Ibro: Babban sirrin chamama ai abune mai sau}i. Mu mun mayar da hankaline ga karkara, watau }auye. Ka san dukkowa asalinsa kenan sai wanda ba yada asali, sai wanda ba ya da uba. Sabodahaka maras asali shi ke kiran kansa ]anbirni. Amma in kana da asali to duk indaka ji an zagi ]an }auye, to ka tsaya kayi ya}i sai inda }arfinka ya }are.Saboda haka mutum ko ]an cikin tuburane shi asalinsa daga }auye ne. Wannanta�amali da muke da mutanen karkara,wa]anda su ne mafi yawa a }asar nan,ya sa aka fi son mu, kuma ake ganinkamar muna barazana ga manyanfinafinai. Kuma mu har gobe tunaninmuna chamama ne. Idan ka duba kamar�yan Nigerian Films shirye-shiryensu zaka ga duk a kan al�ada da addininsu

Ibro, Sarkin Chamama, ya kare tsarin finafinan karkara

�...Maras asali shi ke kirankansa ]an birni. Amma in kana daasali to duk inda ka ji an zagi ]an}auye, to ka tsaya ka yi ya}i saiinda }arfinka ya }are.�

WAKILINMU ya nemi jin tabakin Mohammed MunzaliMohammed, wanda aka fi

sani da suna Ahlan Yoko. Shi ne ke dakamfanin shirya finafinai na �AhlanYoko Production� wanda ke da alhakinshirya mafi yawan finafanan da ake kirada suna chamama. Ban da wa]anda yashirya wa mutane, wasu daga cikinfinafinansa sun ha]a da Ko Da Me KaZo; Akaranbana; Sirrin Chamama; KarTa San Kar; Ibro Tela; Bodari; MaradaDa Shari�a; Ibro Kaftin, da sauransu.Saboda ri}arsa a wannan fagen ne harake kiransa �Super Chamama.� Gayadda suka yi baki da baki da

wakilinmu a Kano:

Bidiyo: Ahlan, akwai wa]ansu finafinaida ake kira da suna chamama kumawasu daga cikinsu kai ne ka shirya su.Shin daga ina sunan chamama ya samoasali?

Ahlan: Kalma ta chamama ai ba wataaba ba ce, wasu ne dai suke ganin watamuguwar kalma ce ko wacce take in anfa]e ta, ba ta da wata ma�ana. Sannanmu da muka san chamama, to abu newanda yake yana da kyau, amma maigajeren ku]i. Saboda }arancin ku]inda ake kashe masa, shi ya sa manya-manyan da suka yi nasu suke kashe

�Daga }in chamama sai ~ata�Ahlan Yoko, jagoran furodusoshin chamama, ya ce a yi hattara

4

Page 6: Mujallar Bidiyo - Yuli/Agusta 2001

BIDIYO Yuli/Agusta 2001

ku]i, sai ka ga ya danne nasu. Misalifim ]ina na Maraba Da Shari�a, lokaci]aya ya fito tare da fim ]in A�isha.

Bidiyo: To a}alla kamar daga nawane ake kashewa idan za a yi chamama?

Ahlan: {yale maganar abin da akekashewa. Shi chamama fim ne wandaba a kashe masa ku]i sosai. Wannangaskiya ne. Amma yadda mutane suka]auki chamama, sun ]auke ta kalma cewula}antacciyar abu. Amma kada kamanta, duk furodusan da ka sani, dagachamama ya tashi. Sai dai idan ya mi}esai ya yi butulci ya ga ya fi }arfin yinchamama sai dai ya yi babba. Ammaalhamdu lillahi daga }in chamamayanzu an fara kauce wa layi. Sai ka gayanzu furodusa ya je ya ]auko fim ]inAmerika ko na Indiya ya zauna }iri-}iri ya fassara shi, ya wanke tsaf ya maida shi na Hausa da rana tsaka. To kakalli finafinan chamama tsaf, za ka gaal�adu ne na Bahaushe tsantsa, fim nena gargajiya.

Bidiyo: Ko }ungiyar furodusoshinfinafinai ta Arewa ta ta~a yi maku wani}orafi kan chamama?

Ahlan: Wannan magana haka, alalha}i}a haka ne. Ka san shi sha�ani, idanaka ce mutum ya zo yana neman ya ciabinci, kada ka hana shi, don ba ka sanyadda Allah zai yi ba. Kuma komai gabaake wa. Yanzu ]in nan wa]annanmutanen da kake gani sun zo ne don ayi masu chamama (ya nuna wa]ansumutane biyu da ke zaune cikinofishinsa). Amma ba su san yadda akeyi ba, shi ya sa suka zo nan a yi masu.

Bidiyo: Maganar manyanfurodusoshi nake yi maka.

Ahlan: Ba zan iya kira maka suna badon na san sai ka buga, ammafurodusoshi da yawa suna yi. Yanzu maakwai chamama guda biyu a hannuna,kuma na manyan furodusoshi ne. Nikaina da Azumi na je na yi wa wanibabban furodusa chamama amma a~oye. Lokacin da zai raba kwalin fim]in sai dai yaro ya sa ya raba masakwalayen. Kuma za ka ga ba su amfanida sunan kamfaninsu sai su aza sunanwani can daban a jikin kwalin kaset.

Bidiyo: To su masu sukar chamama,wato kenan ba}in ciki suke maku?

Ahlan: Ni ban fuskanci ba}in ciki bane suke mana. Ina fuskantar abu guda]aya: ba su so a yi chamama saboda susun yi sama, in dai aka ce sun yichamama za su ga kamar sun kare. Shine kawai dalilin da ya sa ba sa so a yichamama.

Bidiyo: Can baya ka ce fim ]in kaMaraba Da Shari�a an sake shi lokaci]aya da A�isha. To kana nufin ka ce sunyi tseren kasuwa da juna?

Ahlan: Alhamdu lillahi, ai yadda aka]ebi Maraba Da Shari�a da farko, ba a]ebi A�isha ba. A�isha daga baya ne aka

fara sayensa. Kuma Ko Da Me Ka Zo,lokacin da na sake shi, ai su uku ne akasaki a kasuwa, amma a lokacin babuwani fim da ake nema a kasuwa in baKo Da Me Ka Zo ba. Misali, dubi IbroTela, kullum na je kasuwa sai an ce inaIbro Tela? Kuma ita kanta cahamamaiyawa ce. Akwai wanda ake ]aukar suIbro su je sai sun yi fim ]in sai a }isaya. Ni kuma ]ibar �yan wasana zan yiin kashe ku]i, a yi min wasa. Ai shi yasa suke kirana �Super-Chamama�!

Bidiyo: Shin fim ]in Ibro A Makkanaka ne?

Ahlan: A�a, na abokina ne, Abdullahi

Jan Bulo. Ni Ibro Tela ne nawa. Kumawallahi ina tausayin duk wani babbanfurodusan da zai yi kuskuren fiddowani babban fim a kasuwa lokacin daza mu fitar da Ibro Tela ko Ibro A Makka.Duk lokacin da ya ji labarin za mu fitarda wani fim a kasuwa, to ya ha}ura danasa ko wane iri ne. Wallahi tallahi, kaji na rantse maka, ba na jin duk wanifim ]in da za a kai kasuwa lokacin dazan kai Ibro Tela. Ba abin da ba a nunamana ba wai don muna chamama. Idanan je wurin meeting sai ka ga ana waremu. Wani lokaci ma ba a fa]a mana za ayi taron wai don mu �yan chamama ne.

“...Ba su so a yi chamama saboda su sun yisama, in dai aka ce sun yi chamama za su ga

kamar sun kare” – Ahlan

MAIMUNA B. Ibrahimtana daga cikin manyan�yan wasa mata masufitowa a finafinanchamama. Ta shaidamujallar Bidiyo cewamasu sukar ingancinfinafinan chamama suna~ata mata rai matu}a.Dole ne ran wannanyarinya ya ~aci. Dalili shine ita ce tauraruwar mafiyawan finafinanchamama wa]anda Ibroke fitowa ko yakeshiryawa. A cewarta, babuda]i a ri}a kushesana�arka. ShigarMaimuna harkar fim ke dawuya ba ta zame ko�inaba sai ~angaren chamama.Ba}uwa ce a harkar,amma yanzu haka ta yifinafinai da damawa]anda suka ha]aBodari, Ha}}inMa}wabtaka, AdashenIbro, Kar-Ta-San- Kar,Kanwa da kuma Ibro Tela.

A bayanin da ta yi,Maimuna ta ce ita dai tanaalfahari da finafinan datake yi na chamama,

– inji Maimuna B. Ibrahim, Sarauniyar Chamama

Chamama ta kar~u ko an }i ko an so

�domin da chamama nake ci kuma naketaimaka wa �yan�uwa da abokan arziki.�

A kan haka ne take jawo hankalinmasu kushe finafinan da cewa, �To donme suke zuwa a ~oye Ibro na shiryamasu?�

A }arshe ta ce ko an }i ko an so,

chamama ta kar~u. Kwanan baya sukadawo daga Jihar Gombe inda suka sharekwanaki da dama suna yin wasankwaikwayo na da~e tare da Ibro. �Kanaji ko? Mu goma sha shidda ne muka je,kuma wallahi mun samo alheri maiyawa,� inji sarauniyar ta chamama.

Maimuna B. Ibrahim

5

Page 7: Mujallar Bidiyo - Yuli/Agusta 2001

BIDIYO Yuli/Agusta 20016

WANNAN labari ne naban tausayi da takaici

wanda, in ba ka yi hankaliba, sai ya sa ka hawaye. Acikinsa, an nuna wani Alhaji(Tahir Fagge) yana fama daciwon daji (ciwon }afa), har}afar ta zuganye, ta kwantarda shi, kullum sai kuka yakeyi. Matansa biyu ne masuhalaye mabambanta;uwargidan, Zaliha (ZainabAbubakar), matar kirki ce,yayin da amaryar, Amina(Hauwa Maina), ta ri}a}yamarsa saboda halin dayake ciki, tana nuna ba za taiya zama da shi ba. A }arshema ta rabu da shi.

Ita ko Zaliha, ta ci gaba dayin addu�a don Alhaji yasami sau}i, ga shi ko uwarsata tsane ta. Zaliha ta ci gabada ha}ilo kan Alhaji, tananema masa magani. Ta sayarda kayan ]akinta, kuma tayi }o}arin ta sayar daakuyarta amma iyayentasuka ce ai babu ita. Har barata yi, kuma ta yi }osai. Wataran ma garin neman maganisai basawa suka tare ta, ta shada }yar bayan wani mutuminkirki ya cece ta.

Daga bisani dai Alhaji yasami sau}i, har yana takawa,ya je ya gaida uwarsa(Tabature [andume). Uwar tagane kuskurenta a kan}iyayyar da ta nuna waZaliha, kuma ta ro}igafararta. Da zai tafi, sukagamu da Amina ta yi ba}i

Alhaji ya yanke jiki ya fa]i,ya mutu nan take.

A }arshe, Zaliha taku]ance yayin da iyayentasuka kai ta wata rugga sukanuna mata shanu sama dadubu, suka ce duk nata ne.Akuyar nan ce wadda ba asayar ba. Bayan wuya saida]i kenan.

Wannan fim ya tsaru. Annuna sakamakon hairan shine hairan. An nuna cewahalayya irin ta Amina ba abin

}irin ba kyan gani, duk talalace. Alhaji ya ce mata, �Keba mahaukaciya ba, ke baalmajira ba!� Don raininwayo, wai har ta nemi yamaida ita ]akinta.

[an Alhaji ma, Salmanu(Adamu G. Muhammed),wani lalataccen yaro, ya ganekuskurensa, ya ro}i gafaragun mahaifinsa. Uban yayarda, har suka yi salla tare.Ba zato ba tsammani, sai

da take janyowa sai nadamada da-na-sani. Za a iya koyondarasi daga dangantakarZaliha da surukarta, sannanzai kyautu mata su yi koyida Zaliha.

Mutuwar Alhaji babbarishara ce ga duka mai rai,cewa mutuwa ha~o ce. Ga shidai ya warke sarai, ammakuma ya yanke jiki ya fa]i.Wannan wa�azi ne.

Wani abin burgewa shi ne

rawar da �yar Zaliha, watoZakiyya (Fatima Maikano) tataka a fim ]in. Wa}arta ta�Daina Kuka Baba� tana jefamai kallo a kogin tunani cikeda ban tausayi.

Amma wa}ar da Zaliha tayi bayan wannan, murya]aya ce da ta Zakiyya.Kamata ya yi a canza muryaa nan. Duk da haka, wurin yanuna cewa ashe dai Zalihamace ce mai aji kafin bala�injinya ya auka mata har talalace a kamanninta.

Sannan an burge a wajensauya kamanni. Yadda akamaida Zaliha zuwamummuna, maras aji, an}o}arta. Haka ma yadda akamaida Aminawula}antacciya bayan ta bargidan Alhaji.

Amma akwai gyara indaIbro ya tu~e za a yi fa]a dashi. Mun ga ya tu~e, sai kumamuka gan shi da riga, ba muga lokacin da ya maida rigarba. Sannan a wannan wurin,darakta ya bari �yan kallon]aukar fim ]in, wa]anda basu cikin shirin, sun zo suna}walo idanu, suna ~ata tsarin,ga hayaniyarsu ta yi yawa.

Bayan haka, a wurinzaman makoki a gidanAlhaji, an nuno wasu matasuna murmushi. Idan ]anyune a wasan kwaikwayo aidarakta ba ]anye ba ne.

A fim ]in, wasu wuraren(scenes) suna yin tsawo. DonAllah a ri}a ta}aitawa. Dubidai wa}ar }arshe, �Na GodeAllah Yara Muna Murna,�wadda Zaliha ta yi, ta yitsawo duk da dacewarta. Fimne fa wannan, ba dandalinki]an kalangu ba!

-----------------------------------Sabon fim ]in da �Iman

Ventures� za su yi sunansaMUTUM?

A da can sun yi Samira,Zumu]i, Jinin Masoya, Dare[aya, da kuma Imani.

Kamfani: Iman Ventures, KadunaFurodusa: Abdullahi Maikano UsmanDarakta: Saminu Mohammed Mahmoud’Yan wasa: Tahir Mohammed Fagge, Zainab

Abubakar, Hauwa Maina, TabatureDandume, Ibro, Ibrahim Mu’azzam

Imani***

Fatima Abdullahi Maikano (Zakiyya a cikin shirin Imani)

Al}alancinmu

A cikin shafukan da ke tafe daga wannan, za a ga sharhi damanazartanmu suka yi a kan wasu finafinai da muka za~adomin fara wannan aikin. Mun bai wa kowane fim taurari.

Yawan taurarin da aka ba fim yana nuna darajar da mukaba fim ]in. Muna so a ce fim ya sami taurari biyar. Koakwai wanda zai sami hakan? Ga yadda al}alancin yake:

* * * * * (Tauraro biyar) - Gwarzon fim* * * * (Tauraro hu]u) - Da kyau }warai* * * (Tauraro uku) - An }o}arta* * (Tauraro biyu) - Ba yabo ba fallasa* (Tauraro ]aya) - Shirme kawai

Page 8: Mujallar Bidiyo - Yuli/Agusta 2001

BIDIYO Yuli/Agusta 2001

A WANNAN sabon fim]in, an nuno gidan wani

hamsha}in attajiri wandaaka ce ya mutu. Ana zamanmakoki, mutane sun taru anakar~ar gaisuwa. Shimarigayi bai san ya bar bayada }ura ba, domin kuwabayan an gama makoki saibabban ]ansa Murtala yashiga harka da dukiya; dama ga ku]i ga gidaje.Motocin da yake amfani dasu lambarsu ta daban ce, tafara daga Hamid 1 zuwa 12.

Ku]i sun ru]i Murtala, yayi ta ]aukar abokansa anazuwa ana holewa ana tashagali. Da ya bushi iska saikawai ya hada fati, a tara�yan mata. Sai tuma aka yirashin sa�a ba ya da abokankirki. A nan Iliyasu Tantiriya yi rawar gani domin shike zuga Murtala ya yi yaddaya ga dama; ko bai so yinwani abu ba, sai ya sa shi yayi. Idan kuwa suka shigajami�a, abin ba a cewakomai, sai yadda suka gadama. Harka dai ta ~aci, yaroya lalace. {anin babansa yarasa yadda zai yi da shi. Dafarko ya hana shi fita damota. Sai yaran suka ce idanka san wata ba ka san wataba. Sai Tantiri ya zo damotarsa ya rakice shi su tafida yake shi Murtala akwaiboza sai a tafi shagali.

Tantiri ya sanyo shi gaba,sauran abokai �yan a biyarima a sha ki]a sun rufamasu baya ana ta yin abinda aka ga dama. Sai waniabokinsa wanda ya tafi Turaikaratu ya dawo. Amadushiryayye ne kumakimtsatstsen mutum. Da yaiske baban abokinsa ya rasuya yi masa gaisuwa. Sai daiabin da Amadu ya lura da shishi ne rayuwar abokinsaMurtala ta canza, ya ga

kira. Murtala hu]ubarTantiri ta ratsa shi.

Ita ko budurwar da yake jida ita, Binta, sai ta }ara mi}ekafa ta fara juya shi, sai abinda ta ce tana so za a yi. Akwaima lokacin da suna cikinjami�a za a dawo sai ta ce bata son ya ]auki kowa amotarsa. Haka ko ]in aka yi,sai ku]i ya ba abokan sudawo gida. Ta ]aya ~angarenkuma, Amadu bai gaji ba,yana ta ba abokinsashawarwari nagari. Sai ta kaiga Murtala ba ya son su ha]uda Amadu don kar ya ba shishawara. Haka dai suka yi tayin wasan ~oyo.

A wani lokaci Murtalayana zaune }ofar gida shika]ai yana sha}atawa saiwasu yara almajirai sun zogidan sun yi bara za su fitosai ]aya ya taka ma ]aya

Murtala ya yi mafarkin waiya mutu. A cikin mafarkin yaga }anin babanshi na cewaya sha yi masa fa]a amma ya}i kimtsuwa, ga shi yanzu zaikoma ma Allah. An kai shi zaa rufe ne, ashe wanda ya yiginar kabarin yana cikinkabarin wai zai huta bayanan kawo yana tasowa saimutane suka ji tsoro sukawatse. Shi kuma mutumin(Balago) sai ya ce, �Tundadai aka yar da wannan gawarto mai ita ba ta }warai ba ta.�

Murtala ya firgita dawannan mafarki. Da ma gawa}ar da ya ji almajiran nansuna yi. Ai sai ya nemiabokinsa Amadu ya gayamasa shi yanzu ya yi nadamaa kan abubuwan da ya yiamma sai yana mai shakkunko Allah zai yafe masa.Abokinsa ya ce Allah

Kamfani: Sakkwatawa Communications, SokotoFurodusa: Lawali Tukur FaruRera Wakoki: Lawali Tukur FaruKida: Mande Sakkwato’Yan wasa: Murtala Mohammed, Baba Mohammed

Tahir, Iliyasu Abdulmumin (Tantiri),Jamima, Garus, Balago, Binta Amadu,Nasir Gumi, Kabiru Kankan, da sauransu.

dindindin, to Allah zaigafarta masa. Ha}i}a fim ]inya yi ma�ana domin ya koyamana ana tuba, amma fa tubahar abada, domin wanilokaci sai ka ga matasa sunshagala suna aikata masha�a,su suna hangen ko sun tubaza a kar~a. Sannan an nunamutum ya yi taka-tsantsan daabokan da zai yi. Idan za a}ulla abota a }ulla tagari.

A karo na farko an nunamuhimmancin almajiraidomin an nuna suna iyaagazawa ta wani fannindomin gyaruwar halin waniko wasu. Sun taimaka tundasu ne na farko da suka farajawo hankalin shi zuwa gatuba. Sannan kuma a karo nafarko an yi fim wanda aka yiki]an da wa}ar duk a cikinSokoto kuma suka yi tasiri,kai ka ce a �Iyan-Tama

}afa har suka kaure da fa]a.Daga bisani bayan sun barisai suka ~ige da yin wa}a.Allah sarki, wa}ar ta ratsaMurtala kuma sai ta ]an yitasiri a kansa domin sai yaga yaran nan kamar da shisuke, don sun ta~o abin daya shafe shi. Daga nan sai yafara tunani, yana nazarinabubuwan da ke wakana. Yaga duk cikin abokansa bamai ba shi shawara tagari saiAmadu.

gafurun rahimun ne, yanayafe wa mutum in ya tubaamma fa ba tuban mazuru ba.Daga }arshe dai mun gaMurtala ya kimtsu ya bi�yan�uwansa yana nemangafara, sannan ya ri}eabokinsa na }warai Amadu,ya yi watsi da su Tantiri.

Furodusa Lawalli TukurFaru ya shaida mani cewa fim]insu yana karantar da cewaduk abin da mutum ya yi koya aikata, muddin ya tuba ta

Almajirai a cikin shirin Tuba

Tuba**

yadda neman mata ya lalatashi. Ai sai ya shiga ba shishawarwari. Amma ina! an cewanda ya yi nisa ba ya jin

7

Page 9: Mujallar Bidiyo - Yuli/Agusta 2001

BIDIYO Yuli/Agusta 2001

Kamfani: Iyke More Investments Ltd. (2001)Furodusa: Prince Oscar Baker AnuruoDaukar Nauyi: Ikechukwu Omego NwankwoDarakta: Izu Ojukwu‘Yan wasa: Sani Musa (Danja), A’isha Dauda,

Husaina Adamu Gombe (Tsigai), AsiyaMuhammad, Iliyasu Mohammed,Abraham Moses, da sauransu

SHIRIN Macijiya shi nefim na uku da kamfaninIyke Moore ya yi. Na

farko, [an�adam (Butulu), nabiyu, Jamila. Finafinan suna dawasu ala}o}i. Macijiya yana bada labarin ta}addamar Sagir neda wata budurwa mai sunaHadiza. Sagir (Sani Musa) yata~a kashe wata macijiya a dajinda ke }auyensu inda yake zaunetare da �yan�uwansa. Ashe baisani ba, sarauniyar macizai ce.Wannan ya sa �al�ummar�macizai suka sha alwashin yinramuwa a kan danginsa. Ko kafina ankara, wata macijiya ta sarikakarsa a lokacin da take dawowadaga unguwa tare da }anensa,har ta mutu. Wani boka (IliyasuMuhammad) ya gaya wa Sagirabin da ake ciki. To amma kobayan da boka ya gane shugabarmacizan, bai gaya wa Sagir ba,domin akwai al}awari atsakaninsu. Saboda haka a cikinrashin sani Sagir ya ci gaba datarayya da Hadiza, bai sanmacijiyar nan ce da ta fito donramuwar gayya ba. Kuma yanada masoyiya Samira (Asiya Mu-hammad), har an sa masu rana.

Yayar Sagir, Zilai (UsainaTsigai) ta gane Hadiza da ta ganta a zahiri bayan ta gan ta amafarki. Ita da Samira sun yi}o}arin nuna wa Sagir ha]arinda yake ciki, shi kuwa bai yardaba. Damuwa da kuma kishi sun

a ransa. Shin macijiya za ta }arasakashe sauran abokan gabarta dasuka san sirrinta irin su Samirada boka? Shin za ta auri Sagir neko kashe shi za ta yi? Shin za tatsira da sharrinta ko kuwa za akashe ta?

Fim ]in ya }ara nuna cewafurodusoshi da daraktoci �yan}abilar Ibo suna }alubalantartakwarorinsu Hausawa ta fuskaringancin fim. Wannan ita ce ala}ata farko tsakanin fim ]in dasauran biyun na su Iyke Moore.Macijiya ya ha]u wajen kyanhoto da sauti da }warewa wajengudanuwar shirin fim. Tilas ayabi darakta Izu Ojukwu (wandaya yi finafinan Kudu na Turunciirin su Showdown).

Duk da haka,wasu na ganinakwai guntun kashi wurin masu

wa Musulunci saboda wai tilas ayi tsafi kafin macijin da ke cikinfim ]in ya yi wasa. Ga alama,wanda bai san yadda ake shiryafim ba ne ya fa]i haka. Dominmuna da masaniyar yadda aka yita ]aukar fim ]in ana sakewa donwasan da macijin ke yi ya daceda yadda ake so �yan kallo sugani. Ai macijin na wani mai wasada macizai ne aka ]auko haya;shi ya ri}a tafiyar da macijinsaana ]auka.

Babbar illar Macijiya ita ceyadda aka nuna fifikon bokancia rayuwar mutum. Kamata ya yia nuna fifikon bin Allah, baaljannu ba. Wannan babumamaki, domin ainihin labarin,ba na Hausawa ba ne, wani Ibone ya rubuta shi. Zai fi dacewaya fito a matsayin �Nigerian film�

A’isha Dauda (a matsayin Hadiza) da Sani Musa Danja (Sagir) a lokacindaukar shirin Macijiya

sa Samira ta tunkari Sagir kanhul]arsa da Hadiza, har sukasami sa~ani. Amma sun shiryabayan Yaya Zilai ta sa baki.

To, a garin le}e-le}en Samirada Zilai, sai suka tabbatar lallaiHadiza ce take riki]a macijiya.Saboda sanin sirrinsu da suka yi,sai ta sa su a gaba a kan sai ta gabayansu. Ya zuwa }arshenfaifan, macijiyar ta sari Zilai.

An nuna za a ci gaba a kashina 2. An bar mutum da tambayoyi

fim ]in. Akwai masu cewaInyamiran sun kafe wajen nunatsafi. Gaskiya, wannan maganarbanza ce domin labarin bai kaucewa al�adar Hausa ba. Akwailabarai da tatsunniyoyi barkataina Hausa tun kaka da kakanniirin na cikin Macijiya. Masutsoron tasirin �yan Ibo a fagenfim ne (musamman ~angarenkasuwanci) suke gunaguninnasarar da Ibo suke samu. Akwaiwanda ya ce wai fim ]in ya sa~a

(na Kudu). Anan, an yiangulu dakan zabokenan: watofim daHausa, tsarida kamala daInyamiranci.Wa z o b i y akenan!

S a n n a nSani Danja yafaye yawankazar-kazar afim ]in, harma da inda baa bu}atarhakan. Shinko shi ne�over act-ing�? Kumame ya saSagir yakecikin kaya

]aya a koyaushe? Ai duk da yakemafarauci, akwai lokacin da bafarautar yake yi ba. Kuma ma, baa nuno shi yana farautar ba; shidai kullum yana bin labi, ri}e dasanda. Sai ma ka rasa inda za shi.

Rawar da �yan matan nan keyi (macizai), ba rawar Hausawaba ce. Haka sautin da aka sa narawar. Kuma rubutun sunan fim]in, �Machijiya,� ba daidai ba nea nahawu. Kamata ya yi a rubuta�Macijiya.�

****

Mulitmedia� aka yi su.Wannan ya nuna cewaSakkwatawa sun fara tasowa.Sai dai mafi yawancinsu sun

gwammace su tafi Kano a yimasu duk da wannan cigaban da aka samu. Ko me

ya sa?Sannan an ce mana

Murtala yana shagali yanashirya fati amma ba mu gainda aka yi fatin ba. Yakamata a ce an ]an nunoyanda suke cashewa ko da a

cikin gida ne. Wasu kumasuna cewa furodusan kusanshi ya cinye rabin fim ]in;da shi aka yi fim ]in, shi nefurodusa, mai rubuta labari,kuma shi ya rubuta tare darera wa}ar.

8

Page 10: Mujallar Bidiyo - Yuli/Agusta 2001

BIDIYO Yuli/Agusta 2001

Aziza (Talatu Ibrahim) daAzizu (Salihu Yusi Muham-mad) wadda ta isa abar a yaba,kasancewar ta jawo gyaruwarwasu halaye na Aziza. Buguda }ari, mahaifi damahaifiyar Aziza, wadda take]iya ]aya a wajensu, sunnuna farin cikinsu game daba da gudunmawarsu gawannan soyayya. MahaifinAziza ne ya kawo mishkila alamarin, amma da yake maiido a ku]i ne, Aziza ta jawohankalinsa da naira, ya komahanya. Daga baya maganaraure ta tashi inda iyayenAziza suka yi ta shirinwannan biki.

Me zai faru? Kwatsam, saiwata gagarumar mishkila takunno kai, wato Aziza. ItaAziza sun je bakin ruwa don

Kamfani: Wazobia Film Production, Nguru (2001)Furodusa: Lawal Ali (Barrister)Darakta: Salihu Yusi Muhammad

DAN}ARI: SOYAYYAR MUTUM DA ALJAN?!SHIN ka ta~a ji ko ganin labarin soyayyar mutum daaljani? Kana ganin zai yiwu? Shirin Aziza shi ne amsa.

Kyakkyawa kuma }a}}afar soyayya ce ta }ullu tsakanin

Aziza (Talatu Ibrahim) tare da aljanu a cikin shirin Aziza

mamaki ta fuskar aljanu.Shin ko zuwa ya yi fadaraljanu ya gano? Oho!

sha}atawa, sha}atawar da zata zama farkon kwa~ewaral�amarin. A nan ne wataaljana ta ga Azizu, ta ga cewaya shiga zuciyarta. Ka san mezai faru? Kawai sai ta samuAziza a siffar mutane, wai itaa dole ta bar mata Azizu. Kaika ji tashin hankali.

Ha}i}a wannan lamari yayi matu}ar girgiza tunaninAziza da Azizu, musammanAziza wadda ta rin}aarangama da abubuwan ban-mamaki da na ban-tsoromasu girgiza tunanin]an�adam, duk ta dalilinwannan aljana ]iyar SarkinAljanu. An dai tsaya indaAziza ke shafe-shafenta irinna mata. Abin mamaki, sai taga kayan shafar sun ~ace, sunsake dawowa. Ta tashi afirgice tana }o}arin guduwa.Kwatsam, sai ta ha]u da]iyar Sarkin Aljanu.

Shin yaya Aziza na 2 zai}are? Oho! Mu dai muna jira.

Ha}i}a daraktan shirin,Salisu Yusi Muhammad, yayi amfani da basirarsa awurare da dama kamar~acewar aljani, yanayinaljanun, da ha]a abubuwan

Aziza

***

Tsokaci

A CIKIN trailer (watotallar fim a kaset) ta shirin

Mu Rausaya na 3, wanda�Sarauniya Films� da keGwammaja, Kano, za su fitarkwanan nan, mun ga furodusaAuwalu Mohammed Sabo yanarausayawa tare da malamin rawaShu�aibu Idris Lilisco. An ]auki

hoton bidiyon a lokacin daLilisco yake koyar da rawar �InGari Ya Waye� ta cikin Nagari 1.

Abin tambaya shi ne ko mumasu kallo za mu ga Auwalun afaifan Mu Rausaya ]in kamaryadda aka nuno shi a ]an]anonda aka yi mana? Za mu sha kallo,koda yake an ce kila furodusan

Ko Auwalu zai rausaya ]in?

Karramawar Sarauniya ga Maijiddawadda ke son a karrama ta haka,ta yi auren mana. Kuma aibiyayyar da Maijidda ta ri}a yiwa �yan Sarauniya, sai haka!

Sai dai nan gaba idan za sukarrama wata jaruma ko wanijarumi da ya yi aure, �yanSarauniya su lura: ba cewa akeHappy Marriage Life ba;Turancin daidai shi ne: HappyMarried Life. Ko an gabambancin? Kuma a sa sunan ]anwasan da aka karrama ]in a jikinkalandar saboda �yan baya su san

Bugu da }ari TalatuIbrahim, duk da yakesabuwar �yar wasa ce, ha}i}a

ta taka rawar gani a cikinshirin. Ya ci a ba ta lambaryabo.

zai sa a cire wurin da aka nunoshi yana rawa, saboda girma yazo. Idan ni ne Auwalu, zan barwurin ya fito, domin masu kallosu ga taskun da muka sha wajenfito da fim ]in nan na Nagari.Kuma ai ya rausaya a bikin aurenFati. Kash, sai dai da yake ba nine Auwalu ]in ba! Bari mu gani.

A GASKIYA, �SarauniyaFilms� sun kyauta da suka bugakalandar musamman don tayaMaijidda Abdul}adir murnarauren da ta yi kwanan nan.Kalanda dai ta yi kyau; ga hotora]au wanda aka ]auka a�Gurara Falls� da ke Jihar Neja.

Wasu sun yi surutun cewa�Sarauniya� sun nuna bambancida suka yi kalandar, wai Maijiddaka]ai suka yi wa irin wannankarramawar. Af, to ai komai anafara shi wata ran ne. Kuma duk

ko waye shi.

Taskar RayuwaRANNAN wasu yara suka

kalli Taskar Rayuwa na �MatasaFilm Production.� Sai suka ce wababarsu: �Mun ga wani wandaya fi Ali Nuhu iya rawa!�

Suna nufin jarumin fim ]in,Shu�aibu Idris Lilisco. Ayya, basu san cewa Lilisco malaminrawar Yaro Mai Tashe ba ne! Dama Hausawa sun ce }aramin sani}u}umi ne.

9

Page 11: Mujallar Bidiyo - Yuli/Agusta 2001

BIDIYO Yuli/Agusta 2001

A FIM ]in an ba da labarinyadda Idi (Abubakar B.

Zakari) ya koma Bauchi dazama daga }auyensu don yasami ku]in da za a biyasadakin masoyiyarsa Dije(Maijidda Abdul}adir). Yabar ta a cikin damuwa.

A Bauchi, Idi ya zamadireba a gidan Alhaji Habu(Tahir Fagge) kuma ya ha]uda �yan gidan, wato suHajiya (Lubabatu Madaki)da �yarta Sa�adiyya (FatiMohammed) tare da baroringidan, su [andugaji,Dumbaru da Salele (AlasanKwalle). Sa�adiyya ta dingayi wa Idi tsiya saboda ta]auke shi ba}auye, wandahaka ya sa wata ran har yatari aradu da ka ya mare ta.Wannan ya jawo hushinHajiya har ta nemi }ulla masasharri don a kore shi dagagidan. Abin da ba ta sani baita da masu }untata wadireban shi ne shi ma fa Idi]an gidan ne, domin Alhajiabokin ubansa ne wanda yatsero daga }auye, Allah Yayi masa arziki a birni.

A wani ~angaren an kawoDije daga }auye tana yi waHajiya barantaka a gidan.Sun da]e ba su ha]u da Idi agidan ba. Hatta sai da ya farariki]ewa zuwa yaro ]an}walisa, kuma Sa�adiyya tabayyana }aunarta a gare shi,sannan sai suka ha]u a falowata ran. A nan labarin yatsinke a kashi na 1 na shirin,a daidai kan fuskar Dije alokacin da mamaki ya cikata.

A kashi na 2 na fim ]in akawarware wannan bada}alar.

Kamfani: Sarauniya Films (2001)Labari: Lubabatu Moh’d SaboFurodusa: Auwalu Moh’d SaboDarakta: Aminu Moh’d Sabo’Yan wasa: Fati Mohammed, Abubakar B. Zakari,

Maijidda Abdulkadir, Abida Moh’d, TahirFagge, Lubabatu Madaki, Tukur S. Tukur,Ibrahim Mandawari, da sauransu

Sartse****

abubuwa na musgunawa akan Idi.

Duk da yake ba son aurenIdi da �yarta take yi ba,Hajiya ta tura kakar Dije,Mai Aya, }auye don a zobikin Idi da Sa�adiyya. A can,iyayen Idi da na Dije suka }iamincewa, domin akwaial}awarin aure a tsakanin�ya�yansu. Zuwan uban Dije(Isa Ja) da mai ri}on Idi(Ciroki) Bauchi don nemansasanta al�amarin ya sa akasami waraka. A can ne mukafahimci ashe shi Idi, ]anabokin Habu ne, wato Alh.Kabiru (Ibrahim Mandawari)da Marka (Hauwa Ali Dodo).Mun kuma ga dalilin~arawar Habu da Kabiru, da

Kwatsam, sai ga tsohonmasoyinta Rabi�u (AliNuhu) ya diro daga }asarwaje.

Ai fa shikenan. Gaba ta}are tsakanin Habu daKabiru, kuma aka yi bikinauren Idi da Dije inda�yan�uwa da abokan arzikisuka cashe.

Sartse ya ha]u. To ammaya bar ]iwarsa a bu]e awurare da dama. A Sartse 1an bar Alhaji ya zauna a garishekaru da yawa har yaku]ance kuma ya hayayyafa,bai tuntu~i iyalansa na}auye ba. Ba a sake nunoBiba ba tun da Idi ya faragirma.

Kuma me ya sa Dije tazauna a gidan Alhaji Habuta ]ewa amma ba su ha]u daIdi ba? Ai ko labari Idi zaiiya ji cewa akwai ba}uwaryarinya a gidan. Wannanwata dabara ce dai ta daraktada mai rubuta labari, ammadabarar ba ta shige ni ba.

A kashi na 2 kuma, masufim ]in sun yi rashinkyautawa irin wadda YakubuLere ya yi da suka sa Cirokiya soke shi da cewa shi �maifitsari a tsaye� ne (wato arneko?) kuma �sarkin rashinmutunci� ne. Wato sun yiramuwa kan yadda Lere yasa aka ba da sanarwarmutuwarsu a ha]arin jirginsama cikin Wasila 3. Abin daLere ya yi bai kyauta ba, sukuma Sarauniya bai dace suyi ramuwar gayya irinwannan ba domin ana lalatatsarin shirin fim ne dawannan dabarar.

Shin kuma menene aikinMai Aya a gidan Alh. Habu?Haka kuma mun sanDum~aru ce �yar aiki a gidan,amma tun da Dije ta zo sai takoma aikatau, kuma sai akadaina nuno Dum~aru kwata-kwata sai a wurin bikin aurenIdi. Irin wannan ya faru ga suAlasan Kwalle da[andugaji.

Kuma shin waye MalamShehu a wasan? Ciroki ne ko

Abubakar B. Zakari ... jarumin shirin Sartse

Idi ya ci gaba da hul]a daSa�adiyya don ya musgunawa Dije, saboda sun samisa~ani a kan zargi da rashinfahimtar juna. Can kumaDije ta soma soyayya daAbbas, wani dolo wanSa�adiyya, kuma ta ri}a yin

gaulan nan Abbas. Shi kansaAbbas ya ha}ura bayanubansa ya fa]a masagaskiyar lamarin Idi da Dije.Ita kuma Sa�adiyya, ta yiaddu�ar Allah ya kawo matamiji, musamman tunda gashi tana neman yin kwantai.

IDI: (ya tsaya, ya waiwayo) Dije ! Idan so cuta ne, ha}uri ma magani ne.DIJE: (ta waigo, ta yi masa kallon wula}anci) Idan ungulu ta biya bu}ata, zabuwa sai ta tafi

da zanenta. Haka so tsuntsu ne, idan ya tashi daga kanka, kan wani zai koma.� Sartse 2

d a l i l i nk o m a w abirni daHabu yayi.

A }arshed a iSa�adiyyata ha}urada son Idi,ta bar waD i j eabinta, shikuma yakoma warabin ransata asali,abin da yafaranta waM a r y a m( A b i d aMoh�d) raim a t u } ad o m i nganin itama ansakar matan a t amasoyin,w a t o

10

Page 12: Mujallar Bidiyo - Yuli/Agusta 2001

BIDIYO Yuli/Agusta 2001

Isa Ja? A tsarin sunaye a}arshen wasan, an nuna cewasunan Ciroki Malam Nasidi.To amma wajen da ake taronsasanta Alh. Kabiru da Alh.Habu, shi Habu ya kiraCiroki da sunan M. Shehu.Kuma shi ma Isa Ja, ya kiraCiroki da sunan MalamShehu a wurin da suka ha]ua kan layi suna maganarmatsalar auren �ya�yansu data tasho, ya ce, �Amma faakwai al}awarin da muka yida Shehu, maganar aure�(yana nufin Ciroki neShehun, bayan kuma a nanwurin ma Ciroki ya kira Jada sunan Shehu, da za su rabuya ce, �Ba komai MalamShehu!�

Ya dace kuma a ce Habuya yi mamakin jin cewa asheIdi ]an Kabiru ne a lokacinda ya fahimci hakan da aketaron sasantawa a falonsa. Shima Kabiru, ya dace a ce ya yimamakin jin cewa Idi yanazaune ne a hannun Habu.

Kuma ya aka yi Sa�adiyyata ba Rabi�u lemon kwalbawanda ake surkawa da ruwaba tare da ta surka ]in ba, shikuma har ya kur~a?Dukkansu }auyawa nekenan, ba su san ana surkawaba? Ko darakta ne...

Sannan lokacin da Rabi�uzai bar Sa�adiyya, an nunoshi ya bi cikin otal (corridor)yana tafiya. Duk wanda yasan �Tahir Guest Palace,� yasan wannan otal ne aka nuno.Ai a fim, bai kamata ]an kalloya gane location ba, ko da agidansu aka ]auki fim ]in.

A }arshe, inda aka nunoHabu da Kabiru suna ~atawa(a gaban Marka), an nuno susanye da kaya ba irin na �yan}auye ba. Dubi hular Kabiru,mai tsada ce kawai yalan}washe, kuma rigarsa harda karin guga bayan kuwashi talaka ne ti~is a lokacin.

Ba za mu ce Sartse bai tsiremu a zuci ba. Ya ha]u.Wanda ya ci kofinmu awasan shi ne [andugaji,domin ya nuna cewa shi}wallon shege ne. Kuma asheLubabatu ta iya wa}a? Dukda yake baiti ]aya kacal tarera, ta burge. Kila mawannan ne karo na farko data yi wa}a a fim. Saura a wanifim a ba ta wa}ar baki ]ayata yi.

SA{ON wannan fim ]inshi ne: duk abin da ka

shuka, to tabbas shi za kagirba. Ali (Ahmed Nuhu)saurayi ne da yake soyayyada �yan mata biyu, Salimat(Fati Mohammed) daShema�u (Abida Moham-med). Tun a kashi na farkomun ga yadda �yan matansuka nuna kwa]ayinsu nason su yi soyayya da Ali,amma ya watsa musu }asaa idanunsu. A cewarsa, saidai su zama abokanhul]arsa na makaranta.

Kwatsam, sai ga shi itaSalimat, Allah ya yi matakatari da ha]uwa da sabonsaurayi, Nazir (Ali Nuhu)inda ta kai su ga }ullasoyayya a tsakaninsu harda al}awarin aure. Ammafa kada a manta cewa agida akwai wadda ake so aha]a shi Nazir ]in da ita.Ita ce Zaliha (MaijiddaAbdul}adir), waddamahaifiyarta (HajaraUsman) ta nanika masa ita,amma shi gogan naka,hankalinsa bai kwanta da itaba, domin yana da waddata tafi da hankalinsa. Agefe guda kuma, Ali yashiga tsaka mai wuya, indaya ji yana mutu}ar }aunarSalimat. A nan take ta sanarda shi ai ta tsayar da miji.Ita kuma Shema�u bayanya bar ta da ~acin rai, ha]eda cizon yatsa, game datayin da ta yi masa nasoyayya, amma ya cealhamdulillah, rana tsakaya juyo gare ta ko Allah yasa ya dace. To amma sai tanuna masa ya makara donkuwa bai yi amfani dadamar da ya samu ba a baya.Don haka ita ta ]auke shia matsayin yayanta. Ali daiya yi ~atan-~akatantan � baSalimat, ba Shema�u.

Ko shakka babu, fim ]inya tsaru ta ~angarensoyayya, domin duk wani]an kallo mai sha�awarganin wasan soyayya,musamman matasa �yan}walisa, to in dai ya kalliMujadala, lallai zai gamsuda abin da yake son gani,a ~angaren soyayya. Kumada ma mafiya yawan matada �yan mata, irin fim ]inda suke so kenan. Bamamaki dalilin haka ne ya

Kamfani: FKD Production, Kano (2001)Babban Fu rodusa: Ali NuhuDarakta: Tijjani Ibrahim Bala’Yan wasa: Ali Nuhu, Ahmed Nuhu, Fati Mo

hammed, Abida Mohammed,Maijidda Abdulkadir, MaijiddaAbdulkadir, da sauransu

Mujadala 2****

jawo wa fim ]in kar~uwa.Amma wani abu da shi Aliya yi, bai kyauta wa masukallo ba, masu son suamfani abin da suke ganiba shi ne: bai kamata a ceyadda yake son yayansaba, kuma yake kar~ar dukwani abu da ya zo masa dashi na shawara, ya bijire washawarar tasa ba, na kadaya bar gida, saboda wani~acin rai. Kamata ya yitunda ya ce kar ya fita, toya ha}ura. Domin kuwa an

ce �bin na gaba bin Al-lah�. A nan, babu watacikakkiyar tarbiyya kenana tsakaninsu, duk da cewarbudurwarsa ya gani tare dawansa, kuma wanda ba zaiiya mujadala da shi ba akan ta.

Tilas a yabi darakta TijjaniIbrahim a kan yadda ya fitoda halayyar matasa �yanmakaranta a shirin.

Fim ]in ya fito dama�anarsa ta sunansa, saidai kuma kowane ]an�adam

Abida Mohammed a matsayin Shema’u

11

Page 13: Mujallar Bidiyo - Yuli/Agusta 2001

BIDIYO Yuli/Agusta 2001

ajizi ne, ko mu ce tara yakebai cika goma ba. Ajizancinda masu fim ]in suka yi shine:

1. Sun yi kuskuren nunamana tunanin Salimat daShema�u ya zo ]aya,lokacin da suke kwance akan katifa an nuno sun tafiwa}a tare. Ta yaya tunaninsuya zo ]aya? Tun farko basu tsaya sun ta~a tattauna

zancen ba a tsakaninsu,ballantana su je su yi wa}a.

2. Ba ya daga cikinal�adar maza, a kan budurwasu bar gida, ko da kuwa damahaifinsu suka ha]abudurwar ballantana]an�uwa.

3. Yadda �yan matanfim da suka yi shiga, amatsayinsu na �yan jami�a,ya sa~a wa addinin

Musulunci, da kuma al�adarHausa. Ko ba komai �yanmata �yan jami�a suna iyayin koyi da su in sun gani.

4. Raye-rayen fim]in akwai gyara, musammanyadda �yan mata suke taka]a jikinsu sai ka ce masutaryar Dujal.

Daga }arshe abin koyi aMujadala shi ne: Duk wani]an makaranta da ba zai

tsaya ya yi karatu ba saidai iskanci, ya tsokaniwancan ya tsaya da wancan,ya tsaya da wannan mace,}arshensa a kore shi dagamakaranta, kamar dai yaddata kasance a kan suSha�aibu Kumurci. Sabodahaka masu irin wannan sudaina don kada a yi musuirin ta su Kumurci da �yantawagarsa.

Kamfani: Mashahamatic Production, KanoBabbar Fu rodusa: Maryam Moh’d DanfulaniDarakta: Magaji Ibrahim’Yan wasa: Hindatu Bashir, Abdullahi Moham

med, Salisu Mu’azu, MaryamMoh’d Danfulani, da sauransu

Ajali***

SHI wannan fim na Ajaliyana nuna mugun

}arshen da ya faru ga attajiraNa�ima (Hindatu Bashir) alokacin da ta kashe mijintadon ta auri saurayin masoyi.Fim ]in dai ya }ayatar damasu kallo tun da fari, dominduk wanda ya kalle shi ya gayadda aka yi amfani dagidaje na alfarma da canjintufafi da aka samu. Sannanwajen warwarar jigon wasanan yi }o}ari, musamman tainda Alhaji Barau (KabiruMaikaba) ya auri ajalinsa.Haka Na�ima ita ma ta aurinata ajalin. Bugu da }ari,hu]ubar da aka yiwa Na�imadangane da zaman aure ta yidaidai.

Sai dai a gaskiya dukwanda ya kalli fim ]in zaicika da tambayoyi kan gi~ida suka yi yawa a cikinsa.Misali, idan muka dubayayin da Na�ima ta nemi}awarta Ru}ayya ta raka tashagon da Uzaifa (AbdullahiMohammed) ke sayar dakaya, mun ga sun rabu a kanza su je, amma sai muka gaUzaifa a gidan Na�ima ba muga yadda aka yi ya san ananemansa ba. Shin sun jeshagon ne? Ko kuma aika

masa ta yi ya zo? BayanAlhaji Barau ya mutu anrubuta �Bayan wata biyu...�to kuma sai ga Na�ima akasuwa shagon Uzaifa indahar ta fara sonsa. Shin batakaba take yi ba? Kumatakaba wata nawa ake yi?

mahaukata � a ha]a maza damata wurin kwana a ]aki]aya? Kuma shi likita da yakashe ma�aikaciyarsa Sadiyaba wani abu da ya faru?Wannan ]akin da ya ja ta yabar ta, nan ne kabarinta? Kokuwa ya sa an kai ta ga

�yan�uwanta? Ko kuwa sudanginta ba wani bincike dasuka yi a kai? Lokacin daSamira ta gudo daga gidanmahaukata da ta samiku~uta, a ina shi wannanyayan Farida ya gan ta, ko tayaya suka ha]u? Amma saiganinsa kawai muka yi da itaya shigo gidansu kuma harya ha]a ta da }anwarsa.Kamar da gaske noman ]ankoli, sai ga Ibro a bayankanta shi da abokinsa; to mesuka yi? An ce yawo, kumada rana ne balle mu ce yawondare da ma bisa al�ada ba shida amfani.

Kuma don samun sake harshi Ibron ya mari ]an sanda!Biri ai a hannun malamiyake gu]a, idan ya yi gaBamaguje ai sai kuka.Saboda haka a ina mai laifizai sami damar yi wa hukumatsaurin ido, kuma daga}arshe a sallame shi? A tunafa, wasan don fa]akarwa akeyi ba domin son rai ba ko bandariya, a�a sai don ma�ana dawa�azantarwa.

Sannan me ya kai Farida(Abida Mohammed)mashaya? Ita ba karuwa, ba�yar sandan ciki ba. Tundaga farkon fim ]in babuwata ala}a da take tsakanintada Uzaifa, amma sai ga ta tanayi masa wa}a. A wane dalili?Kuma ina Samira ta samibindiga?

Idan su furodusa MaryamMashahama za su amsawa]annan tambayoyin, tosai a ce fim ]in ya ha]u. Gadai wa}o}i a cikinsa masujan ra�ayi. Hindatu ta nunacewa masu fa]in ta yi girmada zama budurwa a fim saiuwa, ba su fa]i daidai sosaiba. Ta koya musu soyayyatsagwaronta. Sannanabubuwan da aka nuna alokacin fa]an da aka yi dabasawa, an nuna }warewa.

Kafin auren Uzaifa mun gainda ya je gida yana sanar damahaifinsa ya dawo.Kwatsam, sai muka ga an]aura aure. Ina babansa?Kuma wane lafazi ya yi a kanauren? Sannan kuma ya}aurace wa gida tun dagamaganar da suka yi damahaifiyarsa a kan auren.Abin tambaya a nan shi neiyayen sallama shi suka yine a kan auren ko kuwa?

Samira da ake kai tagidan mahaukata, da mahaka aka ce ana yi a gidan

Maryam Mo’d Danfulani (Mashahama)... ta yi ta-maza

12

Page 14: Mujallar Bidiyo - Yuli/Agusta 2001

BIDIYO Yuli/Agusta 2001

B ADALI na 2 ci gaba nedaga na ]aya, wanda ya

fito a shekarar da ta gabata.Fim ]in dai jama�a da damasun yi ta zaman jiran ganinfitowarsa, musamman dayake yawanci an ]aukalabarin rikicin da ya }ullu akashi na 1 ya }are.

Cikin wannan fim masukallo za su fahimci wa]ansuabubuwa guda uku. Na farkodai yadda rayuwar suDumbadus ke kasancewa agidan kurkuku. Na biyukuma zaman auren da AliNuhu ya yi tare da Abida. Nacikon uku kuwa shi ne yadda}arshensu Dumbadus kewakana.

Za a iya cewa Badali ya cisunansa ganin irinrigingimun da suka aukuwa]anda suka fara tafasa tuna Badali na 1, suka kuma}one a na 2. Ali ya yi }o}ariwurin nuna yadda ake zamada iyali, musamman yaddaya rungumi yara ya ri}e.

Fim ]in ya yi }o}arin nunamuhimmancin hukuma acikin al�umma. An yi wannanmanuniya ne ta hanyar yinamfani da jami�an �yan sanda(Sani Cansin da AbdullahiZakari �Ligidi�) wurinfarautar masu laifi. An kumayi amfani da gidan kurkuku.

Sai dai akwai wasuabubuwan dubawa. Ba za ace wurin warwarar jigonlabarin an yi tsumbure ba,mai yiwuwa tuya ce aka ri}ayi ana mantawa da albasa. Nafarko akwai rikitarwa yayinda aka nuno jami�in gidankurkuku a cikin daji tare daBasawan da aka kulle sabodakisan kai. A iya saninmu, baa fita da masu mugayenlaifuka ana sanya su yin aikin}arfi. Wa]anda akan fito dasu su ne wa]anda kwanakin

wa�adinsu a ]aure ya kusan}arewa. Haka nan kuma anafito da masu }anananlaifukan da ba su taka karasuka karya ba. Amma abinmamaki sai ga su Dumbadusa cikin daji sun ]auko itace

da �yan sandan suka nunalokacin da suka rutsa masucaca (ko karta) a cikin wanikwararo. To, idan ina zaunewurin cacar shin yaya zanshaida wa �yan sandan cewana san wa]anda suka aikatalaifin lokacin da suka nunamusu hotonsu? Kuma tun daba su rutsa masu cacar dabindiga ba, to da an yi rashinsa�a akwai wani daga cikinmasu laifin ]auke da bindigaa hannunsa, ai ka ga da labariya sha bamban.

Akwai wani tsokaci wurinda }aramin yaro Momo (wato

Kamfani: Al-Nasid Film Production, KanoBabban Fu rodusa: Rufa’i NasidiDarakta: Tijjani Ibrahim’Yan wasa: Ali Nuhu, Abida Mohammed, Sani

S.K., Hajara Abubakar ‘Dumbaru,’Abdullahi Zakari, da sauransu

** *

Badali 2dalilai. Domin a cikin fim]in an nuna yaro ne maibasira. Shi fa ke ragewa dakai wa Abida abinci lokacinda suke a ~oye. Ba kuma zaiyiwu a ce gaula ne cikin fim]in ba, domin yana fahimtarabin da yake kallo a talbijin.

Saboda haka rawar daHafiz ya taka a cikin Badali2, musamman inda yakenuna halin ko-in-kula haryake wasan }wallo, nan maabin tambaya ne. Kamata yayi a ce }aramin yaro ne ]anshekaru uku aka ba wannanmatsayin. Idan kuma lallai

Darakta Tijjani Ibrahim yana bai wa yara umarni a lokacin daukarshirin Badali 1

ni}i-ni}i, ganduroba ]ayatak yana biye da su sa~alo-sa~alo, ko wani }wa}}waranmakami babu a hannunsa.Da su Dumbadus sun ~allodaga gidan kurkuku, ai dafim ]in ya fi mashi. Yakamata daraktoci su ri}atambayar masana duk wanifannin da za su kwaikwayakafin su aiwatar da wasa.

Wani abin dubawa kumashi ne yadda jami�an �yansanda suka aiwatar dabinciken gudaddun masulaifin. Akwai kuskure a ri}aneman ri}a}}un �yanta�adda irin su Dumbadus batare da }wa}}waran shiri ba.A tuna fa, bayan sun gudohar iyalan wani magidanci(Ali Nuhu) suka kwashe}ar}af. Bai dace ba irin halin

Hafiz a cikin fim ]in ya ri}anuna jahilcin fahimtar suwa]anna basawa lokacin dasuka shigo za su sace su. Aiyaro kamarsa ]an shekarushida da rabi ya isa sanintantance mugu daga cikinnagari. Bai yiwuwa a ce waibai sani ba saboda wa]ansu

kamarsa nezai yi, to yazama doleyaron yak a s a n c egaula ne bawayayye ba.

Yana dakyau }warai anuna tasirinda fim ]in zaiiya yi gahukuma. Afakaice, yananuna bu}atarkawo gyarawajen tsarinaikin jami�antsaro. Ha}i}akuma Badali2 ya nuna} w a r e w a r]aukar hoto,

musamman yadda darakta yatsara yadda aka ri}a nunobasawan suna gudu yayin dasuka ku~uta daga hannunganduroba. Dole kuma ayaba tsarin da daraktan ya bina jerin carbin da ya yi dagawannan fitowa zuwa waccan(wato scene).

YADDA ABIDA TA DIRO DAGAK A N B E N E H A W A B I Y U

Ashe Abida taurin kai gare ta? Wanda bai sani ba kuwa, bariya ji yadda aka }arke da ita a lokacin da ake ]aukar fim ]inBadali na 2. An shirya cewa za a biyo su Abida daga kanbene hawa biyu. A cikin wannan ru]ani kuma har dirowa zata yi. Daga bene hawa biyu? Sosai kuwa, haka Abida ta naceta ce ai sai ta diro.

Furodusan fim ]in dai, Alhaji Rufai Nasidi, hankalinsaya tashi matu}a. Kafaffiyar yarinyar ta ce ai sai ta diro. Shi fadarakta Tijjani Ibrahim? Shi ma ya yi iyakar }o}arinsa amma

13

Page 15: Mujallar Bidiyo - Yuli/Agusta 2001

BIDIYO Yuli/Agusta 2001

abin ya faskara. Abida dai saida ta dira. To yaya aka }are?Lafiya lau ta tashi. Shi kuwabos Daula da ya dira sai dagwiwarsa ta gurje. Allahkiyaye. Nan gaba mun zuba

ido mu ga ko Abida za ta dirodaga cikin jirgi mai saukarungulu. Fim ]in dai ya fitocikin watan jiya. Yana nunayadda aka yi zaman auretsakanin Ali Nuhu da Abida

Mohammed, yadda akeganin makomar Sani GarbaS.K. da kuma rayuwarsu agidan yari da kuma yaddasuke ]auke su Abida dasauran yara su gudu bayan

sun gudo daga jarun. SuDumbadus dai har wa}a sukeyi a gidan kaso. Shin da]inzaman gidan wa}afin ne kowahala ce ta sa su yin wa}ar?Sai ka gani da idonka.

Kamfani: Sarari Ventures, KanoBabban Fu rodusa: Sani AbdurrashidDarakta: Zulkifli Muhammad’Yan wasa: Zulkifili Muhammad, Wasila

Isma’il, Kabiru Maikaba,Yahanasu Sani, Rabilu Musa(Ibro), Suleiman GamboAwaisu, Zulai Muhammad

***Alaqa

SHIRIN Alaqa ya dubiwasu al�amurra ne

wa]anda za a iya cewasababbi ne a fagen shirin fim.Na ]aya, sa~ani a tsakanin�yan uba. Na biyu, ciwonhauka wanda sanadiyyarsamakaru.

Alhaji Sagir (ZulkifiliMuhammad) da wansa Alh.Sa�idu ba sa ga-maciji dominshi wan yana nukura daarzikin da Allah ya yi wa}anen. Duk da }o}arin }anenna ya faranta masa, sai dawan ya bi ta hanyar boka(Ibro) aka haukatar da shi tahanyar turo masa ba}inaljani, wanda ya shiga cikinjikinsa, ya hana shi sa}at.Ciwon haukan ya raba Sagirda matarsa wadda yake ji daso (Wasila Isma�il), ya gududaga gida, ya bar garin, yalula har Katsina. Shi koSa�idu, sai ya tare a gidan}anen shi da matarsaabokiyar munafincinsa(Yahanasu Sani). Suka korimatar Sagir, suka }wace mata�ya da nufin wai ai su nedangin maigidan. Sukadinga matsa wa yarinyar nanA�isha har girmanta, sukamaida ita baiwa a gidan, itako �yarsu Ladi sai gata takeci. A lokacin, ciwon }aunaya kama Wasila kamar zaikashe saboda rabuwa damijinta.

An so a yi wa Sagir magani,amma abu ya faskara. Ya daiyi ta haukansa. Wata ran yagangaro wajajen garinsu, harA�isha (Zulai Muhammad) tagan shi amma kawunta

Sa�idu ya hana ta yi maganada shi. Sai ta gudu zuwaneman uban. A lokacin ne tagamu da yaro ]an }walisa(Sulaiman Gambo Awaisu).Sakamakon haka soyayya ta}ullu tsakaninsu, ta yadda kobayan ta koma gida sai sukaci gaba da soyayya mai zurfi.

Daga bisani dai aka kamoSagir, wani malami (Isa Ja)ya yi masa ru}iyya, har aljaniAbu Zullu ya fice dagajikinsa da ya sha }una, bayanya tona asirin Sa�idu. Sagirya sami lafiya. Shi ko aljani,sai ya koma gunmasoyiyarsa, ita ma ta gujeshi. Cikin fushi, ya je gun

aljani ya haukata su, bayanda suka sha artabu da kotunaa kan mamaye gidan Sagirda suka yi. {arshenmunafinci ya zo kenan.

A nan labarin ya }are.Idan aka auna Alaqa a kan

sikelin tsarin fim na Hausa,to za a ce ya ciri tuta. Yashiryu, kuma an yi matu}araiki da nuna }warewar da keakwai wajen yinsa. Da farko,tilas a yabi Shehu S. Bello,mai yin kwalliya, kan yaddaya shirya wannan aljanin.Shi kuma darakta ya yi aikiwajen fitowar aljanin,musamman yadda aka yiamfani da komfuta wajennuno yadda aljanin yaketafiya a karkara, siffarsa tanaha]ewa da filin da yaketafiya a cikinsa.

Babban darasin Alaqa shine an nuna yadda munafinciyake dodo, yakan ci mai shi.Ga shi Alh. Sa�idu ya zalunci]an�uwansa, kuma]an�uwan ya wahala, shiyana ganin ya more, asheabin }ai}ayi koma kanmashe}iya ne. Kamata ya yimutum ya tsaya a matsayin

farko shi ne gidanmahaukatan nan inda MalamDare yake kula da su. Annuno yadda mahaukata sukea gidan gargajiya. Sin nabiyu kuma shi ne inda Yautaida Mo]a da Zik suke dariyarnan. A wurin, su kansu suYautai, wa]anda suka ]aukikansu a matsayin masuhankali, kamar mahaukatansuke. Shin za}in rake ne dukya jawo wa Yautai haka? To,mashaya rake, a lura!

Inda fim ]in ya ragu yaha]a da Indiyancin da keciki, wato a wa}o}in �ShaBege, Hasken Raina� daAbin Da Na Yi Ki Yi Ha}uriNa Yi Nadama.� Ki]an darawar duk na Indiya ne; shiki]an ma daga Indiya ya zokai tsaye, aka ]ora muryoyinSadi Sharifai da RabiMustapha. Sanya wa}o}iirin wa]annan ci-baya ne a}o}arin da ake yi na ciyar daal�adun Hausa gaba, duk daburgewar da ake ganin an yi.Shin in an yi ki]an da kotsoda algaita ba zai kar~u ba ne?

Ita kanta wa}ar �ShaBege,� kamata ya yi a fara taa lokacin da Wasila ketunanin }uncin da ta shiga,ba sai an }are wa}ar a nunoWasilar ba. Wannan matsalace ta tacewa (editin). Hakakuma da aka rubuta �OfishinAl}ali Na Kotun Sashe Na[aya� da �Kotun [aukaka{ara� duk a kan fuskartalbijin, ba a nuna }warewaba. Me zai hana a yi rubutuna }ofar ofisoshin ko a kankatako (signboard) don suha]e da fim ]in? Kilamantawa aka yi!

Sulaiman da Zulai sun cewani abu; sun cancanci yabodomin sun taka muhimmiyarrawa. Rawar da suka taka tasoyayya ta nuna tsantsarsoyayyar mutum da mutum;da ma mun ga soyayyaraljani da aljana. To, AlhajiSani, ga wani labari: saura kayi fim a kan soyayyar mutumda aljana, tunda an ce hakanyana faruwa. In ba ka yi, bani wuri!

boka. Da gogan naka ya gaAbu Zullu, ya san ta ~aci.Haba, ai sai Zullu ya far masa,shi ma ya haukata shi. Hakasu ma su Sa�idu da matarsa,

da Allah ya aje shi, dominkwa]ayi mabu]in wahala ne.

Akwai wasu sinasinaimasu burgewa wa]anda yadace a yi la�akari da su. Na

Suleiman da Zulai suna soyayya a Alaqa

14

Page 16: Mujallar Bidiyo - Yuli/Agusta 2001

BIDIYO Yuli/Agusta 2001

AminanZamani 1Kamfani: bazanga Film ProductionBabban Fu rodusa: Ashiru Sani BazangaDarakta: Saminu Moh’d Mahmood’Yan wasa: Ashiru Sani Bazanga, A’isha

Musa, Yusuf Barau, WasilaIsma’il, Lubabatu Madaki, YakubuNuhu Danja, Hauwa Maina, MusaM. Abdullahi, Tabature Dandume

***

SHIN don me za ka kaibudurwarka gidanku don

a gan ta, amma daga jinasalinta sai gyatumarka tasome? Abin da ya jawo hakashi ne a cikin tsawon labarinwannan fim ]in.

Mujahid Bala (YakubuNuhu [anja) matashinsaurayi ne wanda ya rola maMaryam (Wasila Isma�il)bayan wata ha]uwa da sukayi a wani kanti. Bayan ya jegidansu har ya yi wa kakartaalheri, sai kuma ya kai tagidan iyayensa don uwarsata gan ta. Daga jin ko waneneuban Maryam, sai Hajiya(A�isha Musa) ta ~ingire. Data farfa]o sai ta ce a fitar daMaryam daga gidan, ba tason ganinta. Ga alama, jincewa �yar Alh. Zubairu da ke}auyen Tuddai ce ya tayarda hankalinta. Da akatambaye ta dalili ne sai tashiga juyayi, shi kumadarakta ya juya mu zuwa canbaya...

Ashe akwai wani matashiBashir (Ashiru SaniBazanga) wanda yakemutumin kirki mai sonzumunci da kowa. Yana da]an abin hannunsa, kuma daaboki Zubairu (Yusuf Barau).Iyayensu maza aminai ne.Bashir yana yi wa kowaalheri, har da uwar Zubairu(Tabature [andume). Ita kouwar, tana ba}in ciki daBashir, ba ta ganin dukalherin da yake yi wa ]an ta.Da Bashir ya sayi besfa, saiya ba Zubairu kekensa; daya sayi mota, ya ba shi besfar.To, matar Bashir dai ita ceA�isha Musa (wadda ta ru]e

tsantsan da Zubairu sabodahalin duniya. Shi ko sai yagarga]e ta da cewa kada tashiga tsakaninsu. Ciroki maya nemi ya yi zun]enZubairu, Bashir ya kwa~eshi. Bashir ya ci gaba dakyautata wa Zubairu, harkayan sawa yana ba shi.

To, shi kansa Zubairu daisai zugar ta ri}a shigarsa. a}arshe ma dai ya koma ya}yasa wa A�isha, matarBashir! Rannan da ya ragemata hanya a mota zai kai taasibiti (ba mu san indaBashir ya je ba!) sai yabayyana mata abin da keransa. Mamaki ya cika ta. Tagarga]e shi kan batun cinamanar da ya shirya, shi koya }i ji. Ta ce za ta yi fitsari,ya tsaya. Tana fita daga motarsai ya she}a cikin daji, shiko ya biyo ta a guje. A nankashi na 1 ya tsaya.

Shin yaya za ta kwashe

tunda maitar Zubairu ta fitofili? Za su ~ata da Bashirkenan? Ko kuwa ma zaikashe A�isha ne a dajin donkada ta tona masa asiri? Akashi na 2 za mu ga yadda zaa yi.

Fim ]in yana koyar dawani babban darasi: watoduk yadda ka yi dama}iyinka, ba zai so ka ba.Kuma amintaka ta zamanisa~anin amintaka ta dauri ce.Na uku, ka aikata alheri gakowa, sakayyarka tana wurinAllah. To amma kuma nahu]u, idan ba ka kula dahalin rayuwa sosai, to za a

zai yanke hukunci sosai.Duk da haka, fim ]in ya

burge wajen fito da wani~angare na zamantakewarHausawa ko �yan�adam duka.Matasa masu arziki da sukeda abokai sai su yi kaffa-kaffa. Ga sauti da hoto sunfito ra]au, kuma daraktan yagwada }warewa.

Sai dai akwai wurarendubawa. Na ]aya, Wasila tayi girma a matsayinbudurwar }auye, in dai ba soake a nuna cewa ta yikwantai ba ne. Kuma yaddata yi shiga a lokacin daMujahid ya je gidansu, ba ta

kai ka a baro.Mai wannan fim dai ba

ba}on hannu ba ne. ashiruSani sananne ne a fagendirama, musamman natalbijin, inda ya yi fice dawasan Sawun Keke a Kaduna.Wannan ne fim ]insa nafarko. A ciki, ya yi }o}ariwajen fito da rauwar }auyezalla, musamman wuringonar dawar nan!

Tabature [andume ta yiwasa abin yabawa amatsayinta na uwar Zubairu.Ta fito da yadda wasu iyayensuke tursasa �ya�yansu su sasu cikin da-na-sani. Dukhaushin da za ta ba mai kallosaboda iya kisisinarta, nasarace a fim ]in, tunda ta nunayadda ya kamata a nuna.

Kashi na 1 na wannan fim]in dai ya nuna cewaJumma�ar da za ta yi kyautun daga Laraba ake ganewa.Sai mutum ya ga kashi na 2

da ta ga Maryam). Tashawarce shi ya yi taka-

fito kamar �yar}auye ba,m u s a m m a ntunda gidansuba attajirai ba ne.

Haka kumashin Zubairutalasuru ne? Annuna malaminm a k a r a n t a rfiramare ne, tobai iya yi wakansa komai saidai ya yi ta yawoda riga ]aya,yana jiran maiakwai ya ba shi?Ai kamata ya yia ce ba ya da

aikin komai.Wa}ar Bashir da A�isha ta

�Masoyi Zo Mu Zauna MuTaka Rawa Ta {auna� ta yitsawo matu}a. Su �yan fimna Hausa har yanzu ba su iyata}aita abu ba; sai a dingaabu ]aya har sai ya ginshimai kallo. Wa}ar da da]i, toamma tana da ginsarwa.Haka ma wurin daCiroki daZubairu suke yin zun]enBashir; ko kawai don Cirokine? Laifin darakta ne.

Sannan wani laifin nadarakta shi ne yawanrugumniyar kayan aiki damutum ke ji, wanda ya farutun a wurin ]aukar fim ]in.Wato irin su wayoyi damakirfo da sauransu. Tun awurin bu]ewar farko hakanta faru. Sannan lokacin daMujahid ya aiki yarinya takira masa Maryam, dalokacin da Malam ya jegonar dawa. Sai a gyara gaba.

Ashiru Sani Bazanga (a hagu) lokacin daukar shirin Aminan Zamani

15

Page 17: Mujallar Bidiyo - Yuli/Agusta 2001

BIDIYO Yuli/Agusta 2001

M ACE Saliha fim newanda ke nuna yadda

ake tsantsar tawakkali dakar~ar }addara da kumawahalhalun rayuwa ta hanyarmaida al�amurra ga Allah darungumar addini. Labari nena wani attajiri mai suna Alh.Murtala wanda ya ha]u dawani Inyamuri har yazambace shi ku]in da yabayar domin su }ullakasuwanci.

Tun daga nan Alhajin yafara ganin bala�i iri daban-daban. Inda Allah Ya rufamasa asiri shi ne ya yi daceda mata mai ha}uri da kumajuriyar ]aukar }addara. Dukirin masifun da mai gidantaya shiga, ba ta ta~a tunanincanza masa fuska ba,ballantana tunanin rabuwa.

Na farko dai Inyamuri yakar~i ku]insa da nufin shigoda wasu injuna. Nairamiliyan ashirin ya nema. Dabai samu ba, sai shi Alhaji yaje ya samo miliyan hu]uwurin abokansa biyu. Bayanan ]auki lokaci mai tsawo saiabokan suka uzzura masa dadole sai ya biya su ku]insu.Wannan ne ya sa matarsaHalima ta ba shi shawarar yatafi Kaduna ya sayar da wanikamfani da yake da shi a can.

Bayan ya sayar dakamfanin, sai ya yi rashinsa�a ya ha]u da �yan fashi akan hanyarsa ta dawowaKano. Suka }wace masa ku]ida mota. Kafin hakan da masai da ya yi mafarkin hakanta faru gare shi.

Alhahi ya }ara ha]uwa dawata masifa bayan ya dawodaga asibiti. Kwatsam, yanakwance a gida da bandeji ajiki, sai aka kawo masasammaci, sanarwar gwanjongidansa daga babbar kotu.

Sanadiyyar haka, Halimata ba shi shawarar neman

aron ]aki domin su zauna agidan abokinsa MalamAbdullahi. Duk abin nanmatar ba ta karaya ba. [ansuAhmed ya kamu da rashinlafiya, an rasa ku]in magani.Alhaji ya ari babur ]inabokinsa don ya kai ]ansaasibiti amma barawo ya sacebabur ]in. A }rshe dai ]anmutuwa ya yi saboda rashinku]in magani.

Ya kuma }ara ha]uwa dajaraba lokacin da matarsa tasayar da kayan ]akinta ta bashi domin ya ja jarinkasuwanci. A nan kuma sai�yan fashi suka tare su a cikintasi suka yi masu }ar}af.

An yit a}o}arinz u g aHalimadon tarabu das h ia m m asaliharm a t a rnan tac eatabau.An jew u r i nboka baa yinasaraba. Ank a i} a r aw u r i na l } a l i(IbrahimMandawari), nan ma ba a yinasara ba.

A }arshe dai arzikinsaAlhaji ya dawo bayanshekara ]aya. Wani abokinsane ya dawo daga tafiyar daya yi wadda ta ]auki lokacimai tsawo. Bayan ya dawosai suka sha}u.

Ko shakka babu, an yi

nasarar isar da sa}on da akeson nunawa cikin fim ]in,musamman ganin cewa fimne wanda tsarinsa ya sha

bamban das a u r a nfinafinanHausa awurare dad a m a .Tsarin fim]in yan u n a} a d d a r a .Na farkodai a fim]in babui r i nsoyayyarnan da taz a m aruwan daret s a k a n i nsamari da�yan mata ac i k i nfinafinai.Wa}o}inal�ada ko

na zamani su ma an kaucemasu. Yayin da wasufinafinai ke magana kangyaran zaman aure kosoyayya ko illar zalunci,Mace Saliha ya ta�alla}ajigonsa ne kacokam kanmuhimmancin ri}on addini.

Duk da wannan, akwaiabubuwan dubawa da dama

a cikin fim ]in. Tashin farkoan kira fim ]in da suna MaceSaliha. Ma�ana, fim ]in nanufin jigon labarin ya ratayane a wuyan matar, watauHalima. Amma sai ga shi tundaga farkon warwarar jigonhar }arshe, labarin mijinta neake bayarwa ba nata ba. Abintambaya a nan shi ne, shinmatar ce ya kamata a kiramace saliha ko kuwa mijinne ya kamata a kira mijisalihi? Idan za a dubi fim ]inda idon basira, AlhajiMurtala ya fi Halima }arfi dajuriyar masifu. Ko ba komaidai, shi bala�in ke fa]a mawa,ita ko sai dai ta taya shi jaje.

Kuma masu fim ]in sun yiwani abu a farko da kuma}arshen fim ]in. Da farko sunnuna ]imbin dukiya a gidansu Alhaji Murtala da kumakyakkyawar tarbiyya a wurin]ansa Ahmed. A gidan babanMagaji kuwa, da yake cantalauci ya yi katutu,�ya�yansa ba shiryayyu bane, kuma shi baban Magajisaboda talauci ko fatiha baya iya karantawa.

Watau kenan wannan fimyana nuna wa masu kallocewa addini ya fi sau}i dakuma da]in yi idan akwaidukiya a gida? Ko da yake

MaceSalihaKamfani: Kazimiyya ProductionBabban Fu rodusa: Saminu Moh’d da Muktar IdrisDarakta: Al-Muktar

***

Malam Zakzaky: Ya yi jawabi mai ratsa zukata a wurinkaddamar da Mace Saliha

Ci gaba a shafi na 44

16

Page 18: Mujallar Bidiyo - Yuli/Agusta 2001

BIDIYO Yuli/Agusta 2001

SAKAMAKON }orafinda masu kallo suke yicewa �har yanzu

�Sarauniya Films� a daji sukeba su shigo birni ba,� ma�ana,yawancin finafinansu nakarkara ne, kwanan bayadaraktan kamfanin, AminuMohammed Sabo, da kumafurodusa Auwalu Moham-med Sabo, sun mayar damartani. Abin da suka yikuwa shi ne, tawagar �yanwasa suka kwasa bataliyaguda suka dira babban birnintarayya Abuja domin shiryawani fim mai suna Garwashi.

Kamar yadda daraktan dakuma shi furodusan sukashaida wa Bidiyo, sun shiryaGarwashi ne a cikin manya-manyan otal-otal har gudahu]u. Ba kuma a nan sukatsaya ba, domin sai da sukaje har Jihar Neja inda aka]auki shirin wata wa}a amagudanar ruwan da kekwararowa daga tsauninGurara (�Gurara Water Falls�).

Garwashi labari ne na irindambarwar da ke har}ewa ayawancin gidajen da ba azaman lafiya, musammantsakanin kishiyoyi. Yana]aya daga cikin finafinan dake nuna zahirin ba}in kishinmace, musamman uwargida.Ya kuma nuna yadda mafiyawan rayuwar wasu mata agidan miji ke tafiya wurinkitsa algungumanci, shiryabada}ala da kutungwila.

Fim ]in ya nuna yaddawata mata mai suna HajiyaSabuwa (Saratu Gida]o),kasancewar ba ta haihuwa(juya ce) take amfani da]imbin jahilcin addini daba}in kishi domin ginabangon hana wata matashigowa gidan da sunanaure. Bayan wannan, ha}artata ba ta cimma ruwa ba, saimaigidanta (IbrahimMandawari) ya auro Halima(Asiya Mohammed).

Don gudun kada ta haihua gidan, sai Hajiya Sabuwata shirya mata makircin daya yi sanadiyar barin gidan.Allah sarki! sai uwargidanta ri}a yin shigar maza tanagittawa ta bakin ]akinHalima. Da wannan sharrinne aka yi wa Halima tabonkawo kwarto a gida.

Bayan Halima ta bargidan, sai Mandawari ya

uwargidan ta ri}a shiryahalin maguzanci. Misali, ta

uwa ta biyo. A }arshe dai saceyaron take yi, ta jefar da shita bayan gida. Allah majiro}o, sai Ya }ara bai waMariya wani ]an.

Garwashi dai an nuna shia gidan sinima kuma ya kusafitowa. Ga rawar da fitattunmatan da ke kan shafinbangon mujallar Bidiyosuka taka:

LUBABATU MADAKIIta da ma ta saba fitowa da

yi amfanida ta~aryad ah a y a } i nb a r k o n owai don

halayen mata marasamutunci. A cikin Garwashima a hakan ta fito. {awa ceta }ut da }ut ga uwargidaHajiya Sabuwa. Da ita akeshirya tuggun ganin bayankishiyoyi. Da yake a birninwasan makirci ita Lubabatu�yar gari ce, sai ta yi ]inkinankon yinin suna ranar dakishiyar }awarsu ta haihu.Ka ji halin zagon }asa, waidon a ce babu wani abutsakaninta da Mariya.Auwalu Moh’d Sabo

17

Garwashi�Sarauniya Films� sun barba]a

a birnin

ababbinFinafinai

LABARAI DA

Abida Mohammed, Lubabatu Madaki, Saratu Gidado da Hauwa Ali Dodo a bakin gabar‘Gurara Water Falls’ cikin Jihar Neja lokacin daukar Garwashi

auro Mariya (HafsatuIliyasu). Ba ta da]e ba sai tasami ciki. Sai dai kafin hakaHajiya Sabuwa ta yi iyakar}o}arinta don ganin hakanbai yiwu ba. Domin ta shazuba mata rubutu a }ofar]aki.

Lokacin da ta haihu, sai

Page 19: Mujallar Bidiyo - Yuli/Agusta 2001

BIDIYO Yuli/Agusta 2001

HAUWA ALI DODO (BIBA)Ita ma Biba, }awar Sabuwa

ce ta }arshe. Da ita ake }ullamakirci don yaron cikin daMariya ta samu ya zube.Biba ce ke shigowa gidan damagani a zuba cikinso~orodo a }ofar ]akinkishiya.

ABIDA MOHAMMEDAbida da FATI MOHAMMED

duk �yan�uwan HajiyaSabuwa ne. Saboda ta samifilin mi}e }afa a gidan, sai takwaso su ta jibge,Mandawari yana ]aukarnauyinsu. Daga }auye ta]ebo su don su ri}a samunsamari suna ba su ku]i itakuma tana amshewa.

An shirya wa Abida ha]asoyayya da ]an maigidan,wato Sadik, don ta ri}asamun ku]i, wanda a }arshesai abin ya zama gaskiya.Fati kuwa da aka ce ta fitarda miji, sai ta ce Mandawarintake so. Tashin hakali kenan!

Wasu daga cikin ’yan wasan tare da furodusa a harabar otal din Sheraton a Abuja

A nan kashi na 1 na fim ]inke }arewa.

SARATU GIDADO:Hajiya Sabuwa kenan. Ita

ce uwargida kan gida kumauwar �yan tuggu.

Lallai Sarauniya sunshiryo tsiya a nan. Duk maimata fiye da ]aya, ko wata

mai kishiya, ko yake son yaga yadda ake }ulla sharri awasu gidajen auren, to yashirya yin kallo nan gabaka]an.

Hakika wannan fim yacancanci wannan suna daaka sa masa. Shiri ne da zaitattara hankalin mai kallonhar sai ya ga }wa}waf. Ya shabamban da akasarin yaddaaka sha tsara finafinanHausa, wato da mutum yafara kallo zai iya ayyanayanda fim ]in zai }are.Wannan fim ya zo da sabonsalo don ri}e mai kallo tareda kwa]aitar wa mai kalloganin yadda za a }arkesa~anin tunanin mai kallo.

Shirin ya }unshi mutuncida tsabagen rashin mutuncia caku]e da tsantsar cinamana, ga kuma ri}onamana. Ya tattara tsagwaronmunafurci da annamimanci.A wani ~angare kuwa fim]in na }unshe da }a}}arfarsoyayya da aka gina ta watasabuwar siga wadda za taburge kowa. Duk da yake

ke gabatar daFurodusa: Adam N. ZakiraiDarakta: A.G.M. Bashir’Yan Wasa: Hafsatu Sharada (Mai Aya), Suleiman

Sa’id, Kabiru Maikaba, Abdullahi Zakari,Dan’azumi Baba, Shu’aibu Lawan,Alasan Kwalle, Hajara Usman, A’ishaBashir

akwai abubuwan ban dariyamasu yawa, amma abubuwanban haushi da ban takaici maza su jefa mai kallo cikinyanayi na tausayi.

Shirin ya }unshishahararrun �yan wasa kamarsu Kabiru Maikaba, BaffaYaro (Yautai), Rabilu Musa(Ibro), Aina�u Ade, Rumasa�uAbdullahi, Isah A. Isah(Khalifa), Aminu Ali, JamilaHaruna, Hajara Usman(Hajjo) da wasunsu maza damata.

An narkar da ma}udanku]i don ganin shirin ya ginuyadda zai burge kowa.

Wa}o}in da ke ciki:* �Mamayelube Aiye

Mamayelube Waya-waya�* �Auren Soyayya Da]i�* �Al}awari�* �Yore Lale Yore Lale.�

Adamu Zakirai ... jaruminfim din Ishara

Isa A. Isa a cikin fim dinIshara

18

ISHARA zai fito nan ba da da]ewa ba!!

KANAWA PRODUCTIONS, KANO

Page 20: Mujallar Bidiyo - Yuli/Agusta 2001

BIDIYO Yuli/Agusta 2001

Shirin Maqabuli, fim ne dake yin hannunka-mai-

sanda kan masu yi wa iyayeri}on sakainar kashi. Koshakka babu, hakan nakasancewa musamman gawa]anda Allah Ya shafa wahannunsu shuni. Maimakonsu kuma su ]an ri}a goga waiyayensu, sai su shantakecikin ru]in duniya. Fim ]inyana kuma yin nuni da cewaiyaye abin a ri}e ne hannubibiyu. Babu kamarsu aduniya, kuma ba a sake su.Shi ya sa inda duk ka ji an ceai wannan ya yi uwar ]aki,to tabbas ko dai ya rasa uwamahaifiya, ko kuma shi daita sun yi wa juna nisa.

Fim ne wanda zai ]aukihankalin �yan kallo ganinyadda wani matashi (Zik)mahaifinsa zai mutu ya barmasa ku]i. Maimakon ya]auki mahaifiyar ya ri}ehannu bibiyu, sai yawofintar da ita. A }arshedai tuyar }osai takekomawa yi a bakin titi.Akwai abin mamaki daal�ajabi.

Abin ya yi }amari har ya}i ya kula da ita bayan ankai ta asibiti sanadiyyar}onewa da ta yi wurin tuyar}osan. Shi kuwa }anenmahaifiyar ke yi masanasiha ya tuna da irin]awainiyar da aka yi dashi tun yana cikin zanengoyo. �Ta yi mani bill inbiya ta ladar ]awainiyar da

ta yi da ni.� Ka ji abin damatashin ya fa]a wa }anenuwarsa.

A }arshe dai ga shi canya ]aga hannu zai mariuwar tasa. Shin zai mare tako fasawa zai yi? Ku jira

Furodusa: Zulkifili Muhammad (Zik)Darakta: ZikKamfani: Zik Entertainment’Yan Wasa: Zulkifili Muhammad, Husaina Ibrahim,

Ahmed S. Nuhu, Sani S.K., Habibu Yaro,Wasila Isma’il, Ali Nuhu, Aminu A. Shariff

a cikin fim ]in Alaqa ya fitoa mahaukaci tuburan. Dominda haukan ya yi zafi sai abirnin Katsina aka same shi.Kun tuna da fim ]in LaifiTudu Ne? A nan ma Zik dasabuwar kama ya fito. Bata~in hankali ya same shi ba,

don komai ba kuwa sai donmahaifiyarsa ce ya ke shukawa wani irin mugun abu.

Zil}ifilu Mohammedyana shirya finafinai na}ashin kansa. Shi ke da �ZikEntertainment,� kamfanin daya shirya finafinan da suka}unshi Su Ma �Ya�ya Ne na1 da na 2, Laifi Tudu, Adalci,Ba�asi, sai kuma yanzu gaMaqabuli nan tafe. Kada amanta, Zik yakan fito amatsayin ]an sanda. A kalliZakaran Gwajin Dafi na 2 dakuma Al�ajabi.

Da mujallar Bidiyo tatambaye shi ko matarsa tanadamuwa da irin rawar dayake takawa, musammaninda ya fito mahaukaci, saiya ce, �Sam, ni dai ba ta ta~anuna damuwa a gabana ba�.

An kuma tambaye shi koiyalan nasa kan yi gunagunimusamman idan sun ga yanataka �role� na soyayya da �yanmata a cikin fim.

Sai ya kada baki ya ce, �Tafa san shiri ne muke yi donfa]akarwa�.

Sai wakilinmu ya saketambayarsa cewa, �Gani nayi su matan �yan fim da kegida ba a yin irin wannansoyayyar da su.�

Duk da haka sai Zik ya ce,�Ai matar da ke gida ba waisonta ka]ai ake ba, har mada }auna da nuna tausayi nazaman tare�. Soyayyar shirinfim kuwa, inji Zulkifilu, �aishiri ne da ake yi don jawohankalin jama�a, ba soyayaba ce ta zahiri.�

A kan wuce gona da irinda ya yi a Maqabuli, shikansa abin ya jefa shi cikinjuyayi, yana tunanin anyakuwa ya kyauta? �Gaskiyana tsorata }warai da rawar dana taka ta wula}anta iyaye a

Zik a cikin Maqabuli

ku sha kallo idan Maqabuliya fito.

Jarumin Maqabuli,Zilkifilu Mohammed (Zik)ya saba fitowa cikin finafinaida kamannun da wasu kekallo bambara}wai. Misali,

a ]anc u w a -c u w a rman feturya fito. Ac i k i nA � i s h akuwa saiya fito dac i w o nshan innai n d a~angarenjikinsa yashanye.

A cikinfim ]inK i b i y a ,Zik yafito amatsayin] a nta�adda.Sai daid u kw a n n a nta�addancida ya yiba su kaii r i nwanda yayi a cikins a b o nfim ]inMaqabuliba. Ba

19

Ya kai wa uwarsa mari

Zik ya saba fitowa bambara}wai a fim. Ko ya wuce gona da iri a Maqabuli?

Page 21: Mujallar Bidiyo - Yuli/Agusta 2001

BIDIYO Yuli/Agusta 2001

cikin Maqabuli. Amma daga baya sai na dake don na yiimani da cewa ba wai iyayen nawa ne na wula}anta ba,� injishi. Ya }ara da cewa, �Shirin fim ne na shirya don yin wa�aziga masu irin wannan hali.�

To, Allah ya sa wa]anda aka yi dominsu su fahimci hakan.In an sami haka, to, burin Zik ya biya kenan, wato fim ]in yazama ma}abuli.

Tsigai (a matsayin mahaifiyar Zik) da konanniyar fuskaa asibiti cikin Maqabuli

WANNAN fim yana nunine kan illar aikata abu marakyau da kuma yin nadamadaga baya wanda ya aikataabin ya dawo ya yi ladaf.Yana kuma fa]akarwa gasamari, �yan mata, da kumamatan aure.

A cikinsa za a ga yaddaSani Mai Iska ke jarabta

Furodusa: Ibrahim Umar BuraimaDarakta: Abubakar I.G. DeleKamfani: Star Film Production’Yan Wasa: Sani Musa (Mai Iska), Yahanasu Sani,

Fati Mohammed, Sani Garba S.K., HajaraAbubakar (Dumbaru), Rabilu Musa (Ibro)

Ladaf

UWARGIDA TARI{E GIDA KAM!

kansa da auren mata. Babbanabin da ke haifar masawannan kuwa shi ne mugunhalin uwargidansa(Yahanasu A. Sani). Ita ce takame gida kuma ta hana dukwata mata ta shigo ta mi}e}afa da sunan zaman aure.

Asiya Mohammed ce Sani

ya fara yi wa Yahanasukishiya da ita. Abin bai yitsawo ba, domin uwargidanta shirya mata makircin daya yi sanadiyyar raba ta da

gidan. Bayan rabuwarsa daHasiya, sai Sani ya sake aurowata matar (Fati Mohammed)wadda ita ma tuni aka }ullamata sharrin da aka raba ta

Boka gulu: uwargida (Yahanasu) da Dumbaru a gaban boka

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI ’UN!Ni Ali Nuhu, a madadin iyayena da dukkan�yan�uwana da abokaina da masoyana, inami}a sa}on ta�aziyya ga iyalan shahararren

daraktan finafinan Hausa ]in nan

MALAM AMINU HASSAN YAKASAI

da �yar wasa MAIJIDDA MUSTAPHA

wa]anda Allah (SWT) ya yi wa cikawa a ranAsabar, 16 ga Yuni, 2001, sanadiyyarha]arin mota a kan hanyarsu ta zuwa

Katsina daga Kano

Aminu Hassan Yakasai

Malam Aminu mutumin kirki ne, mai son jama�a,kamili, kuma }wararre a fagen sana�ar shirya fim.Rasuwarsa babbar asara ce ga wannan sana�a tamu.Allah ya ji}ansu, ya sa Aljanna ce makomarsu, amin.

Sa hannun:ALI NUHU

20

Page 22: Mujallar Bidiyo - Yuli/Agusta 2001

BIDIYO Yuli/Agusta 2001

da gidan.Mai kallo ya tuna fa duk

wannan makirci da taimakonHajara Dum~aru ake }ulla

shi domin ita ce yarinyar dake aikace-aikace a gidan

Sani, kuma �yar gabangoshin uwargida ce.

A cikin �yan kwanakin nanba za ka rasa ganin wata fostainda Ibrahim Mandawari yafito buzu-buzu da }asumbakamar har}iya a gonar raggoba. Sunan fim ]in ajizi. Fim]in an shirya shi nemusamman domin ya koyarda darasi ga irin mutanen nanmasu makirci, mugunta darashin ri}on amana. Labarine game da wani hamsha}inattajiri wai shi Alhaji Ahmed(Umar yahaya Malumfashi)da yaron gidansa da ya ri}atun yana }an}ane, Salim(Ibrahim Mandawari). Yaronmai ladabi ne da ri}onamana. Saboda amincinsahar sai da Alhaji ya mayar dashi kamar ]an cikinsa, yasakar masa harkarkasuwancinsa yana gudanarmasa da ita. Kuma yana ganinhaske domin a kullum saiha~aka harkar take yi.

Ganin yadda abin ke cigaba, sai Alhaji Ahmed ya gaya kyautu ya sau}a}a waSalim yawan wahalhalun dayake fuskanta na gudanar dakasuwancin shi ka]ai. Ya kiraabokinsa (shi Alhaji kenan)wanda suka taso tare tun sunayara, Alhaji Ja�far (KabiruMaikaba), domin ya taimakawa Salim.

Amma shi Alhaji Ja�afaruda zuciya biyu ya zokamfanin, da niyyar sai yayi arziki ko ta wace hanya.Saboda haka ya nemi ha]inkan Salim domin a zambaciAlhaji Ahmed, amma Salimya }i. Kuma domin kada yaha]a su, bai fa]a wa AlhajiAhmed abin da Alhaji Ja�afarke nufi ba.

Saboda imaninsa daneman sau}a}a wa masu}aramin }arfi, Salim yabayar da shawara a rageku]in kayan masarufin dakamfaninsu ke samarwa dakashi goma domin talakawasu sami sau}i. Alhaji Ahmed

ya amince da hakan aka rage.Amma sai ragin ya zame

wa Salim bala�i. Domin ba tayi wa su Alhaji Aminu (SaniS.K.) da]i ba, domin irinkayan da kamfannsu ke yikenan. Ya samu Salim yanafa]a yana fa]in sai ya karyasu. Duk }o}arin da Salim yayi na nuna masa an yi ne badomin a karya su ba sai dontaimakon talakawa, ya citura.

Saboda haka Alhaji Aminuda sauran �yan kasuwamarasa imani irinsa, gami daha]in kan Alhaji Ja�afaru daya nemi a ha]a kai da Salima cuci Alhaji, suka shiga}ulla wa Salim sharri damakircin yadda za a halakashi. A }arshe dai aka sace shiaka ~oye shi a wani guri harna tsawon shekaru hu]u, baa san inda yake ba. Shi kuwaAlhaji Ja�afaru, sai duniya takomo sabuwa gare shi, yazama manajan Alhaji. Ya ci

gaba da cin duniyarsa datsinke.

Amma da yake Allah baazzalumin Sarki ba ne, yasanya ]aya daga cikin �yanta�addar da aka sa su saceSalim ya tausaya wa Salim]in, ya nemi ya tona asiri koya ku~utar da Salim. Ganinhaka aka harbe shi wannanyaron, da zaton ya mutu...

To, me zai biyo baya? Koazzaluman nan za su cinasara? Sai mai kallo ya jira

Salim ya gamu da fushinazzalumai a cikin Ajizi

Kamfanin ‘Home Alone’ zai fito da zakaran gwajin dafin finafinan Hausa

ya gani.Shirin Ajizi yana ]aya

daga cikin hamsha}anfinafinan da ake jira yanzu.

Kamfanin �Home AloneProduction� ne ya yi shi.Furodusan shirin, AlhajiHamza M. [anzaki, matashine wanda ke da }udurincanza yanayin finafinanHausa domin su yi gogayyada na ko�ina a }asar nan.

Idan fim ]in ya fito, za afahimci hakan.

Ibrahim Mandawari ne ajizi a cikin shirin Ajizi

Malam ko malama,yaya kuka gamujallar Bidiyo?Muna so ku rubutoku gaya mana inda kuke ganin tana bu}atar gyara.Haka kuma kuna iya rubuto ra�ayoyinku a kan kowane fimda kuka kalla, wato kyaunsa ko rashinsa, da inda yakebu}atar gyara.Sai a rubuto zuwa ga:

Edita, Bidiyo, P.O. Box 10784, Kano.ko ta hanyar Intanet, E-mail: [email protected]

21

Muna maraba da

Page 23: Mujallar Bidiyo - Yuli/Agusta 2001

BIDIYO Yuli/Agusta 2001

Fim ]in Shaida, shiri newanda ya }unshi dangantakata gaskiya da ri}on amana awani ~angaren da kumamakirci da matsananciyar}iyayya a tsakanin wa da}ane a ]aya ~angaren.

Kamfanin �Al-Nasid FilmProduction,� Kano, wanda yashirya shahararren fim ]innan Badali 1&2, shi ne yakeshirya wannan sabon fim naShaida.

A cikinsa, Aliyu (AhmedS. Nuhu), da Yakubu (NuraHusaini) wa da }ane ne.Aliyu ne wa, Yakubu kuma}ane. Aliyu yaro ne natsattse,kamili, mai kamun kai da]a�a. Amma Yakubu duk indaja�iri ya kai ya wuce nan.Hatsabibi ne na ji da}araswa, wanda ya addabiwan nasa. Komai yayansa yanuna yana so, shi ma sai shima sai ya tsaya kai da fatashi yake so. Ya katantanedole sai ya samu biyanbu}atarsa.

Aliyu ya ha]u da yarinyarda ta zama budurwarsa ajami�a mai suna Nafisa, tatsaya kai da fata sai shi. Tace in ba shi ba, to sai dairijiya.

Halayyar Aliyu datarbiyyarsa ta kirki, gami daala}arsa da yayanta Lawal(Ishaq Sidi Ishaq), wandayake abokin yayanta nematu}a, ta taimaka wajen}ara dan}on soyayyar Nafisada rabin ranta Aliyu.

Bayan da masoyan sunnutsa cikin kogin soyayya nedomin ya }ara karsashinguggu~in }aunar da ketsakaninsa da sahibarsaNafisa, ya shirya mata }war-}waryar walima dominmurnar zagayowar ranarhaihuwarta.

Saboda haka aka nemi dajimai ban sha�awa sabodadausayinsa da }oramarsa, gaciyayi na kore a zagaye da}oramar da ganyaye kala-kala masu sa idanu su samugamsuwa domin yin wannanwalima (picknick).

Aliyu ya gayyaci }awayen

Nafisa da abokansa da]an�uwansa Yakubu. AmmaYakubu ya }i amsar gorongayyatar, ya yi }ememe ya}i zuwa.

Me zai faru? Bayan sun jewajen walimar sun natsa, anyi shaye-shaye (ba na mayeba) da tan]e-tan]e da cinabinci na alfarma, sai Aliyuda Nafisa suka kewaya gefen

ne da la�asar sakaliya.Saboda haka da magariba tayi iyayen Aliyu ba su ga yadawo ba, sai suka tambayi]an�uwansa Yakubu. �InaAliyu ne?� Sai ya bayar daamsar cewa ya baro shi amakaranta za su tafi walimarmurnar zagayowar ranarhaihuwar Nafisa. Sai akasake tambayarsa wajen da

shiri da ita Nafisa da Aliyu,wanda ]an makarantarsu ne,ya zama babban wanda akezargi. Saboda haka za atuhume shi. Domin ya ta~afurta cewa sai ya ga bayanAliyu da Nafisa. Sabodahaka tawagar �yan sandamasu bincike ta dirar masa}ar}ashin jagorancin wanisufeto (Ali Nuhu). Ammabincike ya ci tura saboda�yan sanda ba su da}wa}}warar hujja baya gawancan furuci da aka ce yata~a yi.

Bayan an saki Bello, �yansanda sun ci gaba da bincike.Kafin a sake nemansa neBellon ya tafi asibitin da akakwantar da Nafisa dominduba }anwar babansa(gwaggonsa). Da Aliyu yagan shi sai ya ce, �Bayan kakashe Aliyu yanzu kuma kazo ka idasa Nafisa ne?�

Hayaniya ta yi }amaritsakaninsu har sufeto ya ji yafito domin ya zo yi wa Nafisatambayoyi. Sufeto yatambayi Bello dalilinzuwansa asibitin. Ya fa]amasa cewar gwaggonsa ya zodubawa.

Amma abin tambaya a nanshi ne, wanene ya tafkawannan aiki ga wa]annanmasoya biyu? Amsar wannantambayar furodusan fim ]in,Alhaji Rufa�i Nasidi, ya cekwa gani a }arshen fim ]in.

Fim ]in Shaida shiri ne daya }unshi zargi, cin amana,makirci, soyayya da }iyayyakuma wanda ya ]auki sabonsalo daga finafinan da akasani.

---------------------------------

SANARWAMuna dab da buga

mujallar nan muka samilabari daga kamfanin �Al-Nasid Film Production� cewaba Ahmed Nuhu ba ne zaifito a matsayin Aliyu a fim]in. An musanya shi da NuraHusaini, wanda a da akashirya zai fito a matsayinYakubu.

Wa ya dulmiyar da Aliyu, kuma ya sokashe masa budurwa a cikin S HAIDA?

wani fallen dutse domin subu]e ido, cikunansu su ragu.Wajen, }orama ce da ta}unshi kwazazzabon daruwa ke gudana da igiyarruwa mai }arfi.

Kwatsam, sai Naisa ta gawani abu ya make abin}aunarta Aliyu ya fa]a cikinruwa tsundum! Kafin ka cekwabo, ruwan ya yi gaba dashi. Kan ta farga, sai ta ji anfya]e ta ita ma ta je ta fa]awa wani falalen dutse wandasanadiyyar haka ta yi rauni akanta har }wa}walwarta tashafu, ta fita cikinhayyacinta. Watau ba ta ganekowa. Ta ta~u.

Wannan al�amari ya faru

haka aka nufi da Nafisaasibiti likita ya yi matamagani ta farfa]o, amma bata iya amsa komai. Rabinjikinta ya shanye. Likita yabai wa iyayenta shawarar susa malami ya taimaka matada addu�a yayin da shi mayake nasa }o}arin.

Amma me zai faru? Ganinyadda likita ke taimakawawajen samun lafiyarta dakuma }ila tunanin za a iyagano ��yan ta�adddar� da sukakashe Aliyu suka kuma bugeNafisa, sai shi ma likitan akabiyo dare aka kashe shi aofishinsa da ke asibitin.

Bayan an kashe likita saiwani yaro da ake zaton ba su

aka yiwalimar,ya fa]am a s us a b o d aAliyu yaf a ] am a s akafin sutafi.

Ammakash! daaka je saia k as a m uN a f i s akwancejina-jina.A l i y ukuma baw a n d aya sani n d ay a k e .Aka cinema baa ganeshi ba.

SabodaNura Hussaini

22

Page 24: Mujallar Bidiyo - Yuli/Agusta 2001

BIDIYO Yuli/Agusta 2001

Furodusa: Ahmad El-KanawyDarakta: Bala Anas BabinlataKamfani: Iyan- Tama Multimedia’Yan Wasa: Ruqayya Umar Santa, Musbahu M.

Ahmad, Balaraba Mohammed, HarunaAliyu, Galin Money.

Ma�anar dawayya, kamar yaddafurodusan fim ]in ya bayyana wamujallar Bidiyo, shi ne �dawowa�,amma fa a cikin Sakkwatanci. Wannanfim labari ne na wani saurayi ]anbautar }asa (NYSC) da yake soyayyada wata budurwa.

Sar}a}iyar fim ]in kuwa ita cewa]annan �yan mata �yan�uwan junane, watau ya da }anwa. Shi daisaurayi (Musbahu M. Ahmad) }anwaryake so, ita kuma yar ashe bai saniba tana son shi. Duk dai musabbabinabin shi ne zaman da ya yi a gidansulokacin da yake aikin bautar }asa agarin. Wannan fim an yi ]awainiyarshirya shi a garuruwa uku: Kano,Zariya da kuma Maigana.

Ya fito. Sai a duba a gani.

Dawayya

Yaro mai haskawa: Musbahu M. Ahmad (a kan gado), yana karbar umarni dagaBala Anas a lokacin daukar shirin

Duk wanda ya kalli Taqidi,ko shakka babu nan gaba

zai yi kokwanton ]aukarwani mutum daga cikin rana

ya maishe shi cikin inuwa.Fim ]in bai fito ba, to amma

ga ka]an daga cikinlabarinsa.

Taqidi dai labari ne nayadda Sadiq (Ahmed S.Nuhu) ya yi wa Abubakar(Aminu A. Shariff) dare shikuma ya yi masa rana. Tunsuna }anana abokan junane. A }auyen da suka tasomakarantarsu ]aya kumaajinsu ]aya. Saboda dan}onabokantaka da ketsakaninsu, tun sunamakaranta sai suka }ullaal}awarin taimakon juna.Ma�ana, wanda Allah ya]aga sama, to zai cicci~o]ayan su yi sama tare. ShiSadiq yana da ]an�uwa maiarziki da ke cikin birni(Shehu Kano). [an�uwanya ]auki Sadiq ya mayarda shi a hannunsa.

Sai Sadiq ya cikaal}awari ya ]aukoabokinsa tun na shan-banteAbubakar. Duk da cewamatar yayan Sadiq tana da}ane (Sani SK), mijin nata

TAQIDI: YA HARZU{A SOJOJI, YA FIRGITA FARAR HULA

Me ta yi masa zai bindige ta?: Jazuli Kazaza ya ritsa da Fati Mohammed a cikin Taqidi

[AN NYSC, ZA|INAKA!

23

Page 25: Mujallar Bidiyo - Yuli/Agusta 2001

BIDIYO Yuli/Agusta 2001

bai yi na�am da shi bakamar yadda ya amince daAbubakar abokin Sadiq. Dayake akan tura Sadiq}asashen waje harkarkasuwanci, sai Abubakar yayi amfani da wannan damaya yi masa kurciya donkawai ya hau kan dukiya.Abubakar dai ya yi nasarainda har ya aure budurwarSadiq, Saliha (Fati Moham-med) kan yarjejenjar cewaidan Sadiq ya dawo, zaisake ta ta aure shi. Tir}ashi!Ko yaya za su }are? Sai kagani!

Taqidi labari ne na bantausayi, ta�asa, cin amanamuraran. �Never trust a closefriend,� shi ne takensa, wato

’Yan ta’adda: Momo da Jazuli Kazaza a cikin Taqidi

Furodusa Aminu Shariff(Momo) ya bayyana cewa,�Ana yin asarar rayuka dayawa cikin Taqidi.� To, Al-lah ya ji}an mai }ararkwana.

Momo ya ce, �Diramar daaka nemi shiryawa kan titinfilin jirgin sama na MalamAminu Kano ta koma dagaske lokacin da sojoji dake gadin }ofar shiga filinjirgi suka ga mun fito dabindigogi kuma mun yishiga irin ta �yan fashi damakami.�

A daidai lokacin da sukafara bin Ahmed S. Nuhu aguje da bindigogi tsirara,su kuma sai sojoji sukabiyo su. Allah ya aunaarziki ba su bu]e wa junawuta ba. Abin tambaya anan shi ne, ina mai ]aukarhoton fim ]in? Ai da saiya ]auka kawai an samiribar }afa.

Su kuwa farar hula tunkafin fim ]in ya fito sukalla, tuni har ya firgita su.A kan titin Gya]i-Gya]izuwa Na�ibawa aka yiartabun fa]an }arshe. Isar�yan wasan ke da wuya, koda jama�a suka ga sun fiddobindigogi, sai kowa ya ce}afa me na ci ban ba ki ba!Tsammani suke bindigogingaske ne, kuma a hannun�yan fashi da makami. To,da ma ga yadda garin naDabo yake. Wa zai yarda a yiba shi?

a kul ka kuskura ka aminceda sha}i}in aboki.

Tun wurin ]aukar shirinfim ]in mutane suka faraganin tashin hankali.

... Ko dajama�a suka

ga sun fiddobindigogi, saikowa ya ce

}afa me na ciban ba ki ba!

Furodusa: Y akubu MuhammadDarakta: Sani Musa (Danja)Kamfani: Two Effects’Yan Wasa: Abida Mohammed,

Amina Hakuri,Alkhamees D. Bature,Balaraba Mohammed,Sani Musa Danja

Jaheed

Shi wannan fim, za a iyacewa wani ~angaren shari�arMusulunci ne yake }o}arinnunawa ga mutane. Fim ]inya yi }o}arin ya wayar wada mutane kai kan Shari�ayadda za a ga wasuabubuwa. Jaheed ya kumata�alla}a kan kawo gyara

t s a k a n i n�yan�uwa dagwamnati.

Fim newanda ya] a u k itsawon samada watabakwai ana Kisan baki sai gayya: Jami’ai da ’yan wasa sun taru suna shirya Jaheed

FIM [IN N700,000?

24

Page 26: Mujallar Bidiyo - Yuli/Agusta 2001

BIDIYO Yuli/Agusta 2001

shirya shi. �Mun kumakashe naira dubu ]aribakwai ya zuwa yanzu,�inji Sani Danja.

Wannan fim yana ]aukeda wa}ar �Taho Taho,�

wadda wa}a ce maisar}a}}iya (dubi filinwa}o}i cikin wannanmujallar). An nuna fasahayadda ake sa kalmar �ho� afarko da kuma }arshen

]ango. Wa}ar tana da da]ida kuma wuya dominjaruman �yan matan da sukakasa hardace wa}ar sun kaiuku (ba za mu fa]isunayensu ba). Ita ma cikon

ta hu]un sai da ta shafesama da wata ]aya kafin tayi harda. Kullum sai ta yitilawa. Da }yar da ji~ingoshi ta ci nasara. Saura a ganasarar shi fim ]in.

Furodusa: Mika’ilu Ibrahim (Gidigo)Darakta: Aliyu Shehu Yakasai (Baba Ali)Kamfani: Fasaha Films’Yan Wasa: Ali Nuhu, Salmat Baba Ali, Firdausi Tijjani

Ibrahim, Shehu Kano, Kabiru Nakwango

Sidiqu

Wannan labarin wanisaurayi ne da ya ri}eamanar dukiyar waniattajiri. Saboda gaskiyaryaron sai mai dukiyar nanya }udurta a ransa cewazai aura masa ]iyarsa dakuma ]ora shi jagorantar

al�amurran dukiyar. Wata rana sai aka tura wannan

yaro }auye domin ya gudanarda wasu ayyuka. Kwatsam, saiya yi kici~is da wata yarinya harmu�amalar soyayya ta shigatsakaninsu.

Bayan ya dawo gida sai

Salma Baba Ali

babban al�amari dangane da wannanfim shi ne: a karon farko fitaccendarakta Tijjani Ibrahim Bala ya sakababbar �yarsa a cikin shirin fim.Yarinyar, mai suna Fiddausi TijjaniIbrahim, kwanan nan ta kammalakaratun sakandare inda sakamakonjarabawarta ya yi mata kyau sosai.Shin me ta karanta? Kimiyya. Wanesakamako ta samu? Seven credits,two passes. Kun ji fa, �yan mata. Donhaka ne shi Tijjani, wanda yanaalfahari da }o}arin Fiddausi, yana sota wuce zuwa jami�a; wato ba shigansoja ta yi wa harkar fim ba.

Shi ma Baba Ali, �yarsa (�yar}anwarsa) Salma, ita ya sa a fim ]in,wanda shi ne fim ]insa na farko.Yaran biyu kuma sun nuna }warewa.Sababba da fararra: Abida ta rungume Fiddausi

ZA|E MAI WUYAR GASKE

sun fito. Wannan zai iya haifarda cushewar kasuwa yaddawani fim ]in tun bai gamashiga duniya ba zai ha]u da}arar kwanansa, musammanirin na �yan tagajan-tagajan ]innan. Baya ga wannan,yawaitar finafinan za tadakushe sa}onnin daingantattun finafinai za su isarga jama�a ta hanyar fa]akarwa.A }arshe kuma idan ba a yiaune ba, furodusoshi dadaraktoci suna ji suna gani karezai kashe ragon layya.

Finafinan dasuka fito acikin wannanwatan

Finafinan da suka fito ]in sunha]a da wa]annan:

1. Furuci2. Zainab3. �Yar Gudulle na 14. Biyu Babu5. {unchi6. Lalura7. Sartse na 28. Tallafi9. Badali na 210. Kantafi 211. Ni Ma Ina So na 212. Hamayya

WANI abin lura shi ne cikinwannan watan na Yuli an samiyawaitar fitowar finafinai.Domin tun watan na da kwanatakwas (8/7/2001) finafinai 13

13. Izaya na 214. Bonono15. Zumunci na 216. A Da]e Ana Yi17. Mu Wala18. Hauwa19. Sawun Giwa20. Ka Yi Rawa Kai Malam22. {angi23. Mu Sha}ata na 224. Tuna Baya25. Mishkila26. Mace Saliha27. Dawayya28. Ibro A Makka

m a i g i d a n s aya yi masaalbishir nazai aura masa]iyarsa. Shikuwa can a}auye ya yia l } a w a r i naure dabudurwarsa �ta }auye.Wacce zaiza~a? {a}a-tsara � kaka!Sai a jirafitowar fim]in.

W a n i

25

Page 27: Mujallar Bidiyo - Yuli/Agusta 2001

BIDIYO Yuli/Agusta 2001

Daraktan wannan fim baba}o ba ne, musamman gamasu karatun littattafanHausa. Duk wanda yaambaci sunan Bala AnasBabinlata, abin da zai farazuwa a }wa}walwarsa, shine marubucin littattafan dake }unshe da labaranal�ajabi da rikita tunaninmai karatu.

Da ya shigo cikinharkokin shirya finafinanHausa bai daina irinwa]ancan labarai ba. Saidai yanzu a finafinan ya fikarkata yake bayyana su.Bala ne daraktan fim ]innan mai suna Sirrinsu, kumashi ne ya yi Kallo Ya KomaSama da wasu finafinan dadama. To yanzu kuma yashirya wani mai ban tsoroda kuma al�ajabi mai sunaSalma Salma Duduf.

Wannan fim ]in labari nena wasu ma�aurata sabon

Abubakar da Hadiza Indiyar Daji a cikin shirin

Furodusa: Bala AnasDarakta: Bala AnasKamfani: Mazari Filmirage’Yan Wasa: Asiya Mohammed, Hadiza Ibrahim

(Indiyar Daji), Abubakar Sadiq

Salma Salma Duduf

aure. Kowane lokaci matartakan shaida wa mijintacewa tana ganin wata

fatalwa a cikin gidansu. Shikuwa mijin sai ya }aryatamatar tasa.

Wata rana sai tafiya bikinsuna ya kama matar daniyyar yin kwana biyu.Mijin ya raka ta. Kafin sufita sai da ya kulle gidansa,daga can kuma ya wuce yatafi ofis wurin aiki.

Ya fara ganin al�ajabi daabin ki]imewa lokacin daya dawo; kawai sai ya iskegidansa a bu]e. Da ya shige

ya yi kiran matarsa, saiwannan aljana ta amsaamma da muryar matarsa.

Kuma ta bayyana gare shida sifar matarsa. Abin damijin ke }aryatawa ya farugare shi. Yaya kenan, ya yakuma zai yi? Sai a jirafitowar fim ]in.

An gina wannan fim ne akan wata tatsuniya. Idan anlura, ya yi daidai da irinlabaran aljanu da fatawowiwa]anda aka san Bala dfa su,musamman bayan ya yiSirrinsu, wanda Batulu Wadata yi daga cikin littafin

Taurarin Kano sun sha}ataRanar 14 ga Mayu nawannan shekara, wasushahararun �yan wasa su13 suka hallara a otal ]in�Rock Castle� da ke Tiga,Jihar Kano, domin rera watawa}a }waya ]aya a cikin fim]in Mu Sha}ata na 3, shirinda �Mandawari Enterprises�ya shirya. �Yan wasan kuwasu ne wa]ansu shahararuntaurarin da ake ta}ama dasu a Kano. Sun ha]a daShehu Hassan Kano,Ibrahim Mandawari, HamisuLami]o Iyan-Tama, AliNuhu, Tahir Fagge da kumaFati Mohammed (Amarya).

Akwai kuma Bashir BalaCiroki, Rabilu Musa (Ibro),Hajara Usman, Shu�aibuLawan Kumurci, da SaimaMohammed, da kumaYarinya mai tasowa: Rukayya Umar Santa tana shakatawa a Mu Shakata na 2

BALA BAI RABU DA FATALWOWI BA!

marubuci Maje El-Hajeej.Mai so ya ga fatalwar da Balaya }ir}iro, ya tarba gaba.

26

Page 28: Mujallar Bidiyo - Yuli/Agusta 2001

BIDIYO Yuli/Agusta 2001

Ruqayya Umar.Irin wannan wa}a da

suka gabatar a bisa dukkanalamu ba a ta~a yin watawa~a mai sigar ta ba a shirinfim na Hausa. Amma za kaiya kwatanta ta da wa}ar nanta �We Are the World� waddafitacce mawa}an Amerikairin su Michael Jackson daStevie Wonder suka ta~a yi.

Wa}ar tana da amshi kamarhaka: �Ruwa, Ruwa Na Al-lah, Na Annabi Mai Suna DaDa]i� (Dubi ~angarenwa}o}i cikin wannanmujallar). Ta fito da waniabin al�ajabi da mamaki, dadon komai ba kuwa saiyadda wanda ya rera wa}ar(playback singer), SharuSadi Sharifai ya kwaikwayimuryar dukkan jarumai mazada suka yi wa}a a cikin fim]in.

Wani abin sha�awa kumashi ne, bayan an gama wa}arsai dukkan taurarin sukariki]e suka koma �yan jarida.Sai dai junansu ne suke yiwa tambayoyi suna ba daamsa. Fati Mohammed ce tafara tambayar Shu�aibuKumurci ra�ayinsa kan yaddamutane ke yi masa kallon]an daba. Ita kuwa SaimaMohammed, tsayawa ta yigaban Iyan-Tama sai ya fa]amata dalilin da ya sakamfaninsa ya daina sanyata cikin finafinansa. Shikuwa Hamisu ya dage kancewa ai babban kamfani nena �Mandawari Enterprises�ya ]auke ta ya maida ta ��yargida�.

Shi kuwa Tahir Fagge,tambayar Shehu Kano ya yidalilin da ya sa go]ai-go]aida shi ya yi rawa a cikin wanisabon fim mai suna Hauwa.

Tambayar da Mandawariya yi wa Ali Nuhu ita ce kanwa}ar nan da ya yi a cikinWasila 1 inda yake cewa,�Wai an ce Kanawa/Waikurkunu suke yi/Sun mancemagannsa...� Ali ya amsa dacewa ai wasa ne aka nunawanda kuma irinsa da]a]]ene tun fil�azal tsakaninKanawa da Zazzagawa.

An yi wani abin dariya adaidai lokacin da taurarinsuka zauna cikin wata rumfadomin yin bitar baitukan dasuka rera. Kowa daga cikinsuya }i ya kusanta da tsufa

balle mutuwa. Ma�ana, dukda cewa Ibro ya ro}i kowa

Ibro: Ya so suu fadishekarunsu, sun ki

Saima: Me ya sa Iyan-Tama suka ‘share’ ta?

Shehu: ‘Ka yi rawa kaiMalam...!’

don Allah ya fa]ishekarunsa na gaskiya, babu

wanda ya bi ro}on da ya yi.To, wa ke so a ce ya tsufa?

Gari ya waye tangaram, kowaya tashi lafiya babu alamartashin hankali. Kowa dakowa ya fuskanci al�amurranrayuwa, babu fargaba,tsuntsaye na rera kukansumai da]i iri iri.

Ga kuma iska na hurowatana ka]a ganyen bishiyoyida ciyayi. Wasu abokai cana waje ]aya suna ta guje-guje da dawakai, kowa na}o}arin nuna bajinta.

Can, sai }asa ta dare, sai

kuwwa kake ji ta ko�ina,Tashin hankali da fargabasun maye gurbin zamanlafiya da kwanciyar hankali.Ruguntsumi, kuka, jimami...

To, irin abubuwanal�ajabin da za a gani a shirinGirgizar {asa kashi na 1kenan; sun ha]a da ganinyadda }asa ta dare mutum yaauka ciki, da yadda wanikuma ya su~uto tsakiyardarewar aka ceto shi. Gakuwa yadda }asan }asar ke

aman wuta. Haka kuma akwaiwurare kamar inda wuta kelasar Sani Musa Danjamuraran, yana tsuwwa...Ka]an ma kenan.

Fim ]in na fitaccendarakta/furodusan nan ne,Sani Muhammed Sani,wanda ke da kamfanin�Samnet Media� a Jos. Yada]e ba a ji ]uriyarsa ba.Wata}ila da wannan fim ]inzai girgiza harkar shirya fim� ko ma }asar baki ]aya.

Za su girgiza }asar nan?

Masu girgiza kasa: A wwal Yusuf (Mugun Gaye), Sani Musa (Danja), Sani MuhammedSani (Namijin Duniya) da Salisu Mu’azu a lokacin daukar Girgizar Kasa

27

Page 29: Mujallar Bidiyo - Yuli/Agusta 2001

BIDIYO Yuli/Agusta 2001

Yawanci an ]auka cewatunda Maryam Haruna(Badawiyya) ta yi aurekwana 31 da gama yin fim]in Haya}i, ba yadda za a yia yi fim ]in Haya}i na 2. To,ashe �Zainab Production�suna da wata �yar dabara.Suna nan suna ta }o}arin fitoda Haya}i 2.

Fim ]in ya yi kasuwa awancan karon, kuma wa}arsata �Lililo Da Dariya Danya�ta }ara janyo masa farin jini.To, yadda kashi na 1 ]in yaburge �yan kallo, shi kuwana 2 mamaki zai ba su. Idanaka dubi labarin na kashi na2, za a ga ya faru ne tun aHaya}i na 1 inda gaba ce ke}ulluwa tsakanin ma}wabcida ma}wabci (Umar SaboKatakore da Muhammed B.Umar Hankaka). Sun sasantaa }arshen fim ]in, amma ba aga yadda zamansu yakasance ba.

Furodusa: Kabiru MohammedDarakta: Muh’d B. UmarKamfani: Zainab Production’Yan Wasa: Ali Rabi’u Ali, Fati Moh’d, Abida Moh’d,

da Nura Husaini

Hayaki 2

Sun sake kunno hayaki: Nura Husaini, Fati, Abida da Ali Rabi’u Ali (Daddy) lokacindaukar shirin Hayaki na 2

Ba a nan abin ya tsaya ba.An yi al}awarin ]aura waAminu da Badawiyya aure.Shin al}awarin na cika kokuwa? A cikin na 2 mun gaana shirin fim ]in tare da FatiMohammed. To ina ta shigociki?

Ko ma dai me kenan,babban abin da �yan kallo

zai fi ba su mamaki shi neyadda za su ga Badawiyyacikin Haya}i na 2 ]in, alhalikuwa an yi mata aure kusanshekara ]aya da ta shu]e.Wani labari ma ya ce har tasami }aruwa. Ku jira fitowarfim ]in, domin akwai abintausayi, da ]ebe kewa dakuma ban dariya a cikinsa.

KO MAULA ZAI KAWO {ARSHEN MAULA?

Hindatu Bashir shahararriyar �yar wasa ce. Ban da finafinanHausa, ta fito a cikin Nigerian films guda biyu, wato Show-down da kuma Eleventh Hour. Kwanan nan ta shiga sahunfurodusoshi inda ta shirya wannan fim mai suna Maula. Fim]in yana ]auke da wa�azi a kan illar almajiranci a arewacin}asar nan. Yana jawo hankali ne kan irin matan nan masuyawo da katin asibiti na }arya suna neman taimakon ku]i.

Ba a nan ka]ai Maula ya tsaya ba.Yana kuma tsokaci akan matan da za su ri}a yawo kwararo-kwararo suna baraalhali suna da �ya�ya mawadata masu taimaka masu. �Za kaga jama�a suna ganin laifin irin wa]annan �ya�yan alhali basu san cewa laifin uwar ba ce barar da take yi,� inji Hindatu.

Furodusa: Hindatu BashirDarakta: Sulaiman Sa’idKamfani: Saudat Production’Yan Wasa: Hafsatu Sharada (Mai Aya), Suleiman

Sa’id, Kabiru Maikaba, Abdullahi Zakari,Dan’azumi Baba, Shu’aibu Lawan,Alasan Kwalle, Hajara Usman, A’ishaBashir

Maula

Suleiman Sa’eedHafsatu Sharada

YARA KU ZO GA “LILILO” YA DAWO!

A fim ]in, Hafsatu Shara]a ce take ta}ar}arewa tana yinirin wannan nau�in barace-barace.

Kishin Arewa ne ya sa Hindaru ta shirya fim ]in. Shin kofim ]in zai iya kawo }arshen maula? To, zai dai wayar da

28

Page 30: Mujallar Bidiyo - Yuli/Agusta 2001

BIDIYO Yuli/Agusta 2001

kan mutane a kan wannanba}in halin, ya taimaka arage.

Jarumin shirin, SuleimanSa�id, wani mutumin Jos, shine ya ba da umarni a fim ]in.Ita kanta Hindatu ta takarawa a ciki, tare da }anwartaA�isha, da wasu mutum biyudaga Jos, da dai sauransu.

A�isha Bashir ta fito a

Furodusa: Ali NuhuDarakta: Tijjani IbrahimKamfani: FKD Productions’Yan Wasa: Fati Mohammed, Abida Mohammed,

Fatima S. Abubakar (Karishma), ZulkifiliMuhammad, Ahmed Nuhu, Ali Nuhu

Kuduri

Wannan shi ne sabon fim ]inAli Nuhu, bayan nasarar daya samu da fim ]insaMujadala 1&2. A wannankaron, Ali da darakta TijjaniIbrahim ba su tsaya gasoyayyar matasa �yan}walisa ba, duk da yake sunci riba a wancan karon.Yanzu sai suka shiga gidanaure na matasa, suka nunoyadda rikici ya lullu~eauren. Amma fa ba ci-gabanMujadala ba ne, wanda acikin kashi na 2 ]insa an yiwani baiti mai cewa, �A yau}arshen Mujadala ya zo/Babu batun tankiya,?/{warai!�

Shi {uduri, yana ]auke neda labari mai ban tausayi da

kuma jimami. �Yan mata neguda biyu �yan�uwan juna(Fati Mohammed da kumaAbida Mohammed). Jaruminfim ]in, Zulkifilu Moham-med, shi ke auren Fati harAllah ya ba su haihuwa.

Amma kash! me zai faru,sai ciwon ta~in hankali yakama Fati. Ganin cewa an kaita asibiti sai aka ba Zikshawara ya auri �yar�uwartaAbida, don ko ba komai daiai ta ri}e ]an Fati. Abin ikonAllah, bayan wani lokaci, saiAllah ya bai wa Fati sau}i,ta dawo ]akin mjiinta.

Al�amari ya fara canzawaa cikin gidan Zik tun lokacinda Fati ta dawo. Ganin tadawo sai gogan naka ya juya

matar Suleiman, wandauwarsa ce ke wannan bararduk da yake yana da hannuda shuni. Sannan akwaisabon ]an wasan nanZilkifilu, wanda ya fito amatsayin mataimakinjarumin fim ]in.

Wakilin mujallar Bidiyoya ji }orafe-}orafe a SabonTiti (Kallywood) a kan

]auko �ba}on darakta� daHindatu ta yi, wato ba ta sa]an Kano ba. Kuma ta ba shimatsayin jarumi. Don hakaya waiwayi fuodusar a kanwannan magana. Sai ta amsa.�To ai �yan wasa duka naKano ne, ba na Jos ba ne.Kuma na ga mukan yiwannan zumuncintsakaninmu. Kamar yadda

(furodusoshi) na Jos koKaduna sukan zo su kira(�yan fim) na Kano. Dalilikenan. Kuma ka san kowanelabari kakan duba wanda yadace ya fito maka a ciki. Toni sai na ga (Suleiman) yadace. Wannnan kurum nedalilin da ya sa na ]aukoshi.�

To, Allah ya sa sun ji.

SABODA ABIDA: FATI TA HAUKACE

dai Fati can ta ]auko wu}aza ta gagara wa jinjirin da tahaifa. Ba shi ka]ai ba, munkuma ga ta bi Abida a guje.Allah ya kiyaye!

Kada mu manta, ita Abidakafin ta auri Zik, tana damasoyi (Ali Nuhu). Sai daiAli mutuwa yake yi kafin suyi aure. Shi kuwa haukan daya sake dawowa kan Fatiyaya za a yi masa magani?Babu wanda ya sani saima�aikatan jinya, watauSaima Mohammed da kumaNura lmam.

Fati Mohammed za taburge mai kallo da yadda tanuna haukacewa, abin kamarda gaske! Da ma Fati ce,wadda ko rijiya aka ce ta fa]aa wasa, kila... Lallai za a shakallo a nan. Fim ]in ya kusafitowa.

Gamon jini: Fati ta nuna kwarewa wajen nuna haukacewa

Mai mace biyu, ya da kanwa: Zik tare da matansa

wa Abida baya. Ya dainakula ta, kuma bai mai da itamatarsa ba. Wannan al�amari

y adugunzumaF a t i ,g a n i nyadda Zikk ewula}anta�yar�uwarta.

To waces h a w a r aFati tay a n k e ?Sai ta} u d u r ia n i y a rt a i m a k awa Abidadomin tafita cikinw a n n a n}unci. Ga

29

Page 31: Mujallar Bidiyo - Yuli/Agusta 2001

BIDIYO Yuli/Agusta 2001

A farkon watan Yuni lokacinda ake ]aukar fim ]inHuznee a unguwar Kurnacikin {araman HukumarDala, Kano, an yi artubumuraran ba na dirama ba.Abin sai da ya kai ga zaromakamai.

Abin ya faru ne lokacin dawasu dakkakun samari sukanemi shiga cikin gidan daake ]aukar fim ]in wandadarakta Hafizu Bello yakeshiryawa bayan ribar da yaci daga fim ]in Jumur]a.Lokacin da aka kulle gidan,�yan dabar sun yi ta dukan}yauren gidan, yadda ta kai}ara ta sa an dakatar da aikin]aukar fim ]in.

Wata ruwaya ta ce HabibuAlma ne ya fara harzu}a, indaya fito yana fa]a, su kumabasawan unguwar suka faraantaya masa zagi. Ganinhaka sai wasu �yan wasan dasuke ganin daidai suke dasamarin suka fito domin a yita ta }are. Daga cikinsu kuwahar da Tijjani, mai fitowa amatsayin bos, da kumaAhmed S. Nuhu.

Bayan an shiga tsakani sai�yan dabar suka yi gangami,]auke da makamai, sukazagaye gidan da nufin cewasai sun sassari Tijjani Asase.Kowa dai ya san Asase ba yajiran ko-ta-kwana; da ma si�za ni� ce ta tad da �mu je mu.�Nan take ya ce sai ya fita.Sauran �yan fim ]in kuwasuka nace kada ya je.

{arshen labari dai an cehar baki Asase ya fasa wawani daga cikin �yan dabar.A cewar wani wanda ya gabada}alar da idonsa, �HafizuBello zai yi sakaci in dai baka saka wannan scene cikinHuzni ba.� Amma kila cikinraha ya yi wannan furucin.

Basawan Kurna sun kafsa da ’yan shirin Huznee

Gwanar rawa da gwanin rawa: Fatima S. Abubakar da Ali Nuhu suna cashewa

Hashimu Dikko, Hafizu Bello, da mai koyar da fada Masta Idi a wurin daukar shirin

LOKACIN da ake ]aukar fim ]in Cikas a asibitin El-Nouryda ke kan titin Gya]i-Gya]i, Kano, wani tsautsayi ya aukuga Aina�u Ade. Aina�u ta gamu da gamonta lokacin da takesarraf allura a matsayinta na ma�aikaciya. Ba ta ankara ba,sai allurar ta tsire ta. Nan take kuwa jini ya yi ta zuba.

Su kuwa masu aikin jinyar marasa lafiya a asibitinhankalinsu ya tashi matu}a, suka firgita. Bayan motar ta ciburki }ura ta tashi, sai Aminu Ali ({wai-A-Baka) ya fito a

matsayinsa na jami�in tsaro yana zazzare idanu tare daabokan aikinsa. Hankalin masu jinya ya }ara dugunzumada suka ga an fito da Kabiru Maikaba da raunuka a fuskakuma ]aure da sar}a.

Ya kamata furodusoshi su ri}a sanar da abin da za su yia wuraren ]aukar finafinai. Bai dace a ri}a yi wa wurikamar asibiti dirar ba-zata ba. Kada a auka wa wasu, subu]e wuta!

Aina�u Ade ta zubar da jini a wurin CIKAS

30

Page 32: Mujallar Bidiyo - Yuli/Agusta 2001

BIDIYO Yuli/Agusta 2001

dai mun ga yadda Alh.Murtala ya daure cikintalaucin da ya samu kansa aciki. Mai kallo zai iyatunawa da wani hoton gidada aka nuno mana a jikinbangon falon Alhaji tunkafin ya talauce. A jikinhoton an rubuta, �PeacefulHome,� watau gidan da akezaman lafiya. Wannan shinyana nufin gidan attajiri neka]ai ake zaman lafiya?

Sai kuma inda aka aikodaga kotu don a yi wa gidanAlhaji ku]i. Shin su wa sukakai }ara? Ya kamata a ce annuno shari�a a kotu dominba mamaki kotu ta tausayawa Alhaji idan ta gan shi acikin bandeji. Bayan an saida gidansa kuma, matarsa taba shi shawarar neman ]akia gidan abokinsa. Abinmamaki, a kwance yake fa

Mace Sal ihaCi gaba daga shafi na 16

Kamal. Kash! ba ta sani ba,ashe Ahmad (wanda ya fitoda sunan Ahmad) yana damata har da �ya�ya biyu. Tayi ~atan-~akatantan kenan?

Wanda zai fi ba mutumtausayi shi ne Kamal, wandaake neman a yi wa halin �yanmata bayan duk wahalar daya sha a baya (kun tuna dawa}ar �Ni Sai Ka Ba NiTantabarata�?). Duniyakenan, }wallon mangwaro.

Shin ko matan nan da kishike damu da kuma Ahmad zasu yi nasara kan }udurinsu?Sai fim ]in ya fito za a sani.

Furodusa Yakubu Lere yata~a furta cewa ba ya daniyyar yin shirin Adali na 2.A lokacin, kowa ya yarda,domin kusan a ce labarin ya}are. To kuma sai wasu sukamatsa wa Lere cewa ya yikashi na 2 mana, musammantunda na 1 ya ha]u an saminasara.

Don haka sai aka shirya na2 ]in, wanda ci-gaban na 1ne. Adali 2 dai zai fito awatan Oktoba. Kafin nan, zamu iya ~incina wa mai kalloka]an daga cikin labarin.

A fim ]in, za a ga matanIbrahim Mandawari(Maimuna da A�isha Ibrahim)sun haihu, amma sai �yarA�isha ta mutu, ita kumaMaimuna ta haifi ]a namiji,Mansir, wanda ya rayu.Wannan ya sa uwargidaA�isha kishi har tana zuwa

Furodusa: Y akubu LereDarakta: Ishaq Sidi IshaqKamfani: Lerawa Films’Yan Wasa: Ibrahim Mandawari, Shehu Hassan

Kano, Hauwa Ali Dodo, A’isha Ibrahim,Maimuna Moh’d, Tani Umar, Musbahu M.Ahmad, Ahmed Nuhu

Adali 2

KISHI KUMALLON MATA, IN YA MOTSA...

(Hauwa Ali Dodo) ta }iyarda. Sai ma ta samomaganin da za ta kasheuwargidan (Tani Umar); itako uwargidan tana ganinta.

Kun tuna da Bilki maitantabara (Fati Ibrahim)?Kun san fafutikar da Kamal(Musbahu M. Ahmad) ya shaa kashi na 1 wajen janra�ayinta don ta so shi, harya yi nasara ya ci }arfinzuciyarta? To a wannankaron sai ta ha]u da waniha]a]]en gaye (Ahmad S.Nuhu). Shi ne ya sace matazuciya har ta soma wula}anta

cikin raunuka amma kawaisai aka sake nuna shi a }ofargidan Malam Abdullahi yaje neman cin arzikin ]aki.Yaya }arshen Inyamuri yakasance?

Mai kallo kuma zai yimamaki ganin cewa watakusurwar ]akin Halimadan}am take da samiru dadibaida ta silba. Me ya sa bata yi tunanin saida samira ayi wa Ahmed magani ba? Saiga shi bayan ya mutu ta bada shawarar mijinta ya saidakayan ]akin don ya samijari! Ya kamata a ce abokansasun fi yabon dauriyarsa kanta matarsa.

A matsayin al}ali,Mandawari ya yi }o}ari daya }i goyon bayan iyayenHalima kan Alhaji Murtalaya sake ta. A nan darakta yayi }o}arin nuna yadda akeadalci a wurin shari�a. Sai daikuma bai dace a ce masinjanal}ali haka yake kace-kace

cikin tsumman kaya ba.Mace Saliha ya yi kyau,

sai dai kawai akwai matsalarfitar kyakkyawar murya. Sukansu �yan wasan sau dayawa ba a ambatar sunayenwasu a ciki. Halima dai tacika saliha. Amma dai AlhajiMurtala ya fi ta ]aukar}addara.

Wannan fim dai wasu�Yan�uwa Musulmai (Mus-lim Brothers) ne suka shiryashi. Wannan ya nunafahimtar da suka yi cewar fimhanya ce muhimmiya ta isarda sa}o. A wurin taron}addamar da fim ]in kwanannan a Kano, jagoranrundunar �Yan�uwa na }asabaki ]aya, Malam IbrahimEl-Zakzaky, ya bayyanamuhimmancin fim aMusulunci, ya ce idan an yiamfani da wannan hanya dakyau, to za a taimaka maaddini }warai. Mun ga hakatun a yadda �yan Kudu suke

amfani da fim don isar dasa}wannin coci.

Shin ko �Yan�uwaMusulmi za su iya sauyaakalar shirin fim na Hausa?E, to, wannan ya dangantakan yawan finafinan da za suiya shiryowa a lokaci-lokaci,da ingancinsu, da yayata suhar masu kallo su kalle su,da sanya �yan wasa fitattu,da kuma irin sa}wannin dake cikinsu.

Shirin Mace Salihafurofaganda ce wadda ba}iri-}iri ba, in ka ]ebewa�azin da aka bu]e wasanda shi da kuma wurare irinsa.Wannan zai taimaka wajenamsuwarsa, domin idan akazare nau�in nisha]antarwa,aka tsaya kan wa�azi abayyane ka]ai, sai abin yagunduri jama�a, kamar yaddawasannin �yan Kudu sukagunduri su kansu �yanKudun. A yanzu kam an]auko hanya saliha.

amayar. A}arshe daiI b r a h i myakan tare taa }ofarg i d a nDillaliya.

Shi koS h e h uH a s s a nK a n o(wanda yafito da sunaKalla) yanason ya yiadalci at s a k a n i nm a t a n s a ,amma saia m a r y a r ,wato Delu

wurin Dillaliya don a ba tamaganin da za ta kasheMansir. Kishi kumallonmata, in ya motsa sai sun

Darakta Ishaq da Lere suna kula da daukar shirin Adali 2

31

Page 33: Mujallar Bidiyo - Yuli/Agusta 2001

BIDIYO Yuli/Agusta 2001

TUN kimanin shekaru 200 da suka wuce(wato cikin shekarun 1800 miladiyya)mutane da dama a }asashen Turai da

Amerika suka fara }o}arin }ir}iro wata na�urawadda za ta iya sa a ga kamar hotuna suna motsi.Masanin kimiyya na farko da ya yi nasara awannan yun}urin wani ]an }asar Beljiyam newai shi Joseph Antoine Ferdinand Plateau. Acikin 1832, Plateau ya }ir}iro na�ura mai sunaphenakistoscope. Ita phenakistoscope an yi dawasu fayafaye kwatankwacin }aramin faifaiwa]anda aka ]ora a kan sandar }arfe, ]aya akan ]aya. Shi faifan da ke }asa an yi masa zanena hotuna masu girma daidai da juna. An yidabarar zana kowane hoto ya kasance ci gabane na motsin wanda ya gabace shi. Shi kumafaifan da ke sama, an yanka wasu �yan hudoji ajikinsa. A lokacin da kowane daga cikinfayafayen yake wurwurawa, mutum zai ga kamarhotunan nan suna motsawa ne idan ya kalle su

Yadda AkeShirya Fim

Ma}asudin wannan filinshi ne mu koyar da masuson shiga harkar fimdabarun yadda ake shiryafim. A ganinmu, filin zaiamfani su kansuwa]anda suka da]e aharkar, musamman dayake yawancin �yan fimna Hausa da ka kurumsuke yin abin, ba karanto

abin suka yi ba; kawai irinabin nan ne, �Tunda harwane ya yi, ni ma sai nayi!�

Filin zai sami agajimatu}a daga }wararrunmasana a gida da waje. Zamu yi amfani musammanda hanyar zamani taIntanet wajen samobayanai masu amfani don

nuna wa mutanenmucewa ga fa yadda ake yinwannan abu a inda abinya samo asali, kuma gayadda ya kamata mu yinamu.

Duk da haka, tunda muba malamai ba ne, in munyi kuskure, a tashe mu.

A yau za mu fara ne daba da tarihin shirya fim.

Tare da ALI KANO

Asalin shirin fimkyamarar (wato shut-ter) an jona shi da wanizare. Idan dokin ya zowucewa ta kusa da shi,sai ya tsinka kowanezaren, wanda hakan yasa kyamarar za ta]auki hotonsa a nantake.

A cikin }arshenshekarun na 1800,masana da dama sunyi }ir}ire-}ir}irewajen fito na hoto maimotsi (wato fim). Sunha]a da ThomasArmat, Thomas A.Edison, Charles F.Jenkins, da Woodville

Marey na Faransa. Har yau ]in nan ba a san kowanene ya soma shirya hoton talbijin mai motsihar ya nuna shi aka gan shi ba.

Daga cikin wa]annan masanan, shi Edisonya fara aikin }iR]irar na�urar da za ta sa a gahoto yana motsi. Shekaru biyu bayan ya soma,sai ya sami nasara a cikin 1889, bayan HannibalW. Goodwin, wanda wani malamin coci neBa�amurke, ya riga ya }ir}iri wani faifan fimirin na sinima (wato celluloid). Shi wannanfaifan, yana iya juyawa a guje a cikin kyamaraa lokacin da take ]aukar hotuna a jere. A da,guntattakin gilasai ne akan shafa wa wanisinadari mai aiki da haske. Ko ba a fa]a ba, shigilashi ya ]an faye girma kuma ba za a iyawurwura shi a guje ba a cikin kyamarar bidiyokamar shi faifan celluloid. George Eastman,wani masanin farko-farko a kan harkar ]aukarhoto, shi ne ya }ir}iro faifan celluloid mafi

Lantham wa]andaAmerikawa ne;sannan sai WilliamFriese Green da Rob-ert W. Paul �yan }asarBirtaniya; da kuma wada }ane ]in nan Louisda Auguste Lumiere,sai Etienne Jules

Eadward Muybridge

ta cikin hudojin nan da ke jikin faifan na sama.

Hoto na farko wanda yake motsi an yi shi nea cikin 1877 lokacin da Eadweard Muybridgeya }ir}iro wasu hotuna na doki da ke gudu.Yadda Muybridge ya yi shi ne ya kafakyamarorin ]aukar hoto (wa]anda ba na bidiyoba) su guda 24 a jere a gefen wani filin tserendawakai. Kowane abin ]aukar hoto da ke jikin

inganci.

Da aka sami wannan faifai mai da]in aiki, saiEdison ko mataimakinsa mai suna WilliamKennedy Laurie Dickson ya }ir}iro wata na�urarwai ita kinetoscope. Ba a san ainihin wanenedaga cikin wa]annan mutane biyu ya }ir}iro taba. Ita na�urar kinetoscope kamar wata }atuwardurowa ce mai ]auke da faifan fim mai tsawon

Hotunan farko masu motsi

32

Page 34: Mujallar Bidiyo - Yuli/Agusta 2001

BIDIYO Yuli/Agusta 2001

}afa 50 feet (ko mita 15) wanda ke wurwurawaa kan wasu zagayayyun turaku. Idan mutumyana le}en cikin durowar ta wani ]an rami daaka yi zai iya ganin hotunan suna motsawa.

A cikin1894, a Birnin New York, da London,da Paris, an kakkafa na�urorin kinetoscope awasu gidajen kallo wai su Kinetoscope Parlors.A nan mutum zai je ya jefa kwabo a cikin wanirami, sai na�urar ta soma nuna masa hotuna idanya le}a ta cikin wani rami. Kallo-kallo kenan.Duk da yake wa]annan na�urorin sun samigagarumar nasara, shi Edison bai yarda sosaiabin zai ha~aka ba, duk gani yake cewa waniyayi ne kurum aka shiga na kallo-kallo wandahar ma ya soma wucewa. To amma sauranmasana a Amerika da Turai ba su yi tunaninkasawa irin nasa ba, sai suka ci gaba da }ir}iro

kyamarorin sinimamafi inganci tare dana�urorin haska hotonfim ]in, wato projec-tors.

Fim na farko da akanuna wa jama�a ya farune a ran 28 gaDisamba, 1895 a wanigidan cin abinci da keParis, babban birnin}asar Faransa. Wa da}ane ]in nan Louis daAuguste Lumiere nesuka nuna shi, kumakamar dai saurantakwarorinsu masu

shirya fim, sun dai nuna �yan hotuna ne sunamotsi, ba wai wani dogon labari ba. Kawai}udurin fim ]in shi ne ya nuna an ]auki hotohar ga shi an nuna wa mutane a bango sun ganida idonsu. To, bayan wannan ne fa sai aka shigawani yayi na nuna finafinai a dukkan manyanal}aryun da ke nahiyar Turai.

Daga nan ne kuma sai Edison ya fahimcimuhimmancin finafinai da yadda za su iya samutum ya sami ku]i. Ba a da]e ba sai ya ri}ayin amfani da wata na�urar nuna majigi (projec-tor) wadda Armat ya }ir}iro, ya sa mata sunanprojecting kinetoscope. Edison ya nuna fim nafarko ga jama�a a wani gidan sha}atawa maisuna Koster and Bial�s Music Hall a Birnin NewYork na Amerika a ran 23 ga Afrilu, 1896.

Za mu ci gaba

Kwanan nan kamfanin �Arewa Film Awards Limited�ya ba da sanarwar shiga gasar finafinai ta Arewa,wadda ake bu}atar furodusoshi su shiga a kan N5,500kowane fim. A bara, ran 14 ga Mayu aka yi bikin, watoa bana an makara kenan. {ashin bayan shirya gasarshi ne Abdulkareem Mohammed, shugaban kamfanin�Moving Image� kuma tsohon manajan kamfaninFILABS wanda ya shirya gasar a bara. BarinsaFILABS ya sa ya fito da �Arewa Film Awards Lim-ited.�

Samun nasarar gasar bana ya dogara kan kauce wa}orafin da aka yi a bara, inda wasu suka ce an yi sonkai. Mu dubi Amerika, inda kwanan baya aka bayyanasakamakon gasar finafinai ta duniya (wato �Oscars�ko �Academy Awards�). Gasar finafinai ta Arewa itace kwatankwacin �Oscars� na Hausa. Don haka su wasuka ci �Oscars� na ainihi a Amerika? Kuma me zaihana a fa]a]a kyaututtukan da ake bayarwa a tamugasar? A bana, �yan fim na Hausa ba su ma san a wane~angaren za su shiga gasar ba, sai dai kawai mutum yacika fom! Zai kyautu masu shirya finafinan Hausa sunemi finafinai irin su Erin Brockovich, da Gladiator,da Crouching Tiger, Hidden Dragon, don su ga me yasa suka ci abin da suka ci? Ga sunayen gwarzayenfinafinan Turawa na �Oscar� na bana, kamar yaddamuka tsinto su a adireshin da ke dandalin duniya naIntanet, wato: http://movies.yahoo.com/movies/feature/oscar-winners-2001.html.

Gladiator

Best Animated ShortFilmFather and Daughter

Best Live ActionShort FilmQuiero Ser (I want to be)

Best Film Editing

Su wa suka ci gasar ‘Oscars’ a bana?

Best PictureFim ]in Gladiator

Best DirectorSteven Soderberg da fim]in Traffic

Best Original Screen-playCameron Crowe, a fim]in Almost Famous

Best AdaptedScreenplayStephen Gaghan, a fim]in Traffic

Best ActressJulia Roberts, a fim ]in

Erin Brockovich

Honorary AcademyAward: Ernest Lehman

Best ActorRussel Crowe a fim ]inGladiator

Best Original SongWa}ar �Things HaveChanged� ta Bob Dylan,cikin fim ]in WonderBoys

Best Foreign FilmCrouching Tiger, HiddenDragon (daga Taiwan)Irving Thalberg

AwardFurodusa Dino DeLaurentiis

Best Original ScoreTan Dun, a fim ]inCrouching Tiger, HiddenGragon

Best Visual EffectsNeil Corbould, a fim ]inGladiator

Best DocumentaryFeatureInto the Arms of Strang-ers

Best DocumentaryShortFim ]in Big Mama

Honorary AcademyAwardJack Cardiff, Cinematog-rapher

Best Make-upRick Baker da Gail Ryan,a fim ]in Dr. Sess� Howthe Gritch Stole Christ-mas

Best Sound EditingFim ]in U-571

Best SoundFim ]in Gladiator

Best Supporting Ac-torBenicio Del Toro, a fim]in Traffic

Best Costume DesignJanty Yates, a fim ]in

Su wa suka ci gasar‘Arewa’ a bara?

Best LegendaryAward : Adamu Halilu

Best DirectorU.S.A. Galadima

Best ScreenplayMu}addari

Best Legendary Ac-tress: Ladin Cima

Best Legendary Ac-tor: Mustapha [anhaki

Best ActressHalima Adamu Yahaya

Best Legendary FilmBaban Larai

Best ActorIbrahim Mandawari

Best Print MediaTauraruwa

Best Soundtrack�Soyayya {unar Zuci�

Best Film EditorUsman Abdu Nasara

Best Audio...Sai A Lahira

Best CameramanSuri Menti

Best Cable ConnectorABG Electronics

Best Cassette Re-tailer: Hassan Adamu

Best Exhibitor (Cin-ema Screener)Mujtaba [antata

Best Negative RoleIbrahim Mu�azzam

Best CultureWaiwaye Adon Tafiya

Best FilmMu}addari

Star of the Millennium{asimu Yero

Stephen Mirrione a fim]in Traffic

Best Supporting Ac-tressMarcia Gay Harden, a fim]in Pollock

Best Art/Set DirectionTim Yip, Crouching Ti-ger...

33

Page 35: Mujallar Bidiyo - Yuli/Agusta 2001

BIDIYO Yuli/Agusta 2001

Wa}o}in Finafinan Hausa

wahalarta. An sha wuya kafin asami yarinyar da za ta bi wa}ara cikin fim. Sani Danja ya nunamatu}ar }warewarsa a lokacinda ya }ir}iri wa}ar, kuma yagabatar da ita. Saura da me,saura masu kallo su ga yaddaza a aiwatar da ita a cikin fim)

Fim: JaheedKamfani: Two Effects, KanoFurodusa: Yakubu Muham-

madRerawa: Sani Musa (Danja)Shekara : 2001

He he he he ha hiya (sau 4)*

Gani nan ni na taso,Rayuwa, rayuwata na taso.

*Gani nan ni na taso,A ai ni gani nan na taso.

*Hayee yee ye iye,Taho taho, ke yarinyana taho,Na kuma bar ki ni ban da ho,Hotonki ki ba ni in daina ho,Ho horar zuciyarta ki ba ni

ho,Hotonki in je ni gida da ho,Hotonki in zo ina yin murna.

*Ka yi murna?

*Ahee! a ai ina yin murna.

*Jaheed nawa yarda da ni,Ba ya a yau ba tun tuni,Na ba ka kaina tun tuni,Kuma ba na bu}atar ko ani-Ni, na ba ka wu}a na ba ka

ni,Sai ka ]auki wu}ar ka yanki

rabonka.*

In yanka?*

E! daidai ka yanki rabonka,*

Hehehehe ha hiya (x 4)*

Hayee na ji �yanmata na ce-ku-ce,

Wai wace ce tai fice,Sai na ce masu ke ke he ce,Abincina ke he ce,Ruwa fa na sha na ke he ce,Ke ko hulata ta karkace,Ke za ki gyara ke he ce,Za ki gyara don kisa man da

kanki. *

In sa ma?*

Sa man daidai ki sa man dakanki.

*Ba ni komai sai in kana,Juyo idonka in ma fari,Ya mai kyan alfadari,Kuma ga ka da hali nagari,Duk a cikin samarin gari,Kai hi na za~a zahiri,Don ko zuriyata tana

}aunarka.*

Ta }aunace ni?*

E, ai tana }aunarka. *

Za ka wa}e?*

Ni zan wa}e ki ya Alhusna.To ra]a min,In na rasa ki wa zan koma?Ban gujewa.In ma kika gudu zan kamo

ki.*

To mu taka, Mu taka rawa muna yin juyi.

*Ni da kai?

*To ai ni da ke tamu ba ta

~aci,In ta ~aci?In ma fa ta ~aci za ma ta

mu shirya.*

Shirye-shirye? Shirye-shiryen ai na da

yawa.*

Hoho ho ho ho ha hiya (x4)

-------------------------------------

�GARI YAWAYE�

Fim : NagariKamfani : Sarauniya FilmsRerawa : Mudassir Kasim,

Zaliha Sani FaggeShekara : 2001

Gari ya waye dukkan duhu nayayewa (sau 2)

Bayani na taho in ba ki kansoyayyata,

Cikin natsuwa tsaf a waye bana yin wauta.

Mutanen kirki da gaskiya suka

�WATA DAISHARI�AR SAIALLAH�

Fim: ... Sai A LahiraFurodusa : Balaraba RamatRerawa : Alkhamees D.

Bature da Fati B. Muham-mad

Kida : Aleebaba Yakasai

AMSHI: Wata Dai Shari�ar SaiAllah,

Ba Dai Mutum Al}ali ba!

Jama�a ku ]an saurare ni,Wani ]an bayani zan nuni,Ba zan rage manufata ba.

*Ba}in ciki yake ci na,Shi zan fito yau in nunaDomin ko bai kyauta min ba.

*Wani ne abokina jama�a,Ya gwadan hali na rashin ]a�a,Bai kyautata wa kaina ba.

*Na ]au amana na ba shi,Don na amince mai sai shi,Ya ci bai kula amanar ba.

*Matan gidana na ba shi,Ya kula da su ban zargin shi,Sai ga shi bai mini daidai ba.

*Ya mai da matata tashi,Shege ashe ni �ya�yanshiNake ri}o ban gano ba.

*Na ]auki yaran �ya�yana,Har na kashe ragon suna,Ban ]auki �ya�yan shegu ba.

*{yale mutum ]an banza ne,Komai kai masa sai ya kanne,Ya nuna ba ]an goyo ba.

*Duk wanda bai adalci ba,Bai kyautata wa kainai ba,Shi ma ba za ya ga daidai ba.

*Wata dai shari�ar ba wai ba,Sai lahira a gaban Rabba,Nan ne a yi ba son rai ba.

*Ni na bari ba jayayya,Allah Yai min sakayya,Ran lahira ba }arya ba.

*Wata Dai Shari�ar Sai Allah, Ba

Dai Mutum Al}ali ba!

-------------------------------------

�SAMODARA�

Fim: SamodaraKamfani : Fatima ProductionRerawa: Musbahu M.AhmedShekara : 2000

Iya duba duba, samodara,Iya dubi idona, samodara. (x2)Fankeke da gazil, samodaraBaba ne ya saya min,Ya ce in yi yanga ,In yi rawata, duba duba

samodara.Ya ka zo ]an yaro,Ya ka mai fasa taro,Kai kake fasa taro,Ba gudu ba tsoro ,Na ri}e ka a raina,A zuci kai ne mai rufe }ofa,

samodara.*

Iya duba duba, samodara,Iya dubi idona, samodara.Duduwa ]an tako,Ni da ke ba sa}o.Za ni mi}o }o}oKar ki ce nai ro}o,Ki ]an zubo min in sha in yo

samodara.*

Ya kike gunguni,Ko ko ba kya ba ni,�Yar ka]an fa na ce ni,Daure ki zuban ni,In ko kin ce a�a,In tafi can,Ni in ha]a kaina da marmara!

--------------------------------------

�GA NI NAN NATASO�

Wannan wa}a an yi mata la}abida �wa}ar ~ad da bami� saboda

34

Page 36: Mujallar Bidiyo - Yuli/Agusta 2001

BIDIYO Yuli/Agusta 2001

shirya ta, Tunanina ai da ni da ke ba

sa~awa.*

Umhm, ka ji maigida a bar daitonawa!

*Ke ba kya son zama da kowa

na yarda,Ashe kishinki ya ~aci kawo ya

shaida,Amma ni lafiyar zama da ke

shi nah hanga, Shi yas sa duk tanke-tanke ba

na dubawa.*

Kama duba, in ka rabu da niwa za kai wa?

*A�a, don Allah ki daina zancen

�yan yara,Domin ni kin san game da so

shi na aura.Amma yanzu da ni da ke a yau

ni na lura,Kina ta wahalshe ni ni ko ban

iya ramawa.*

In ka rama, ni da kai fa wa taka kwa~ewa?

*Gidana duk ga abinci nan ba

yankewa,Ruwa an shaida duram-duram

nika tarawa.Tufafi dukkan wata guda nika

]inkawa,In kawo maki don gudun zugar

mai ~atawa.*

To wa ma zai zuga ni in zamkamawa?

*Dai ai fa ki ji ni na fa]a ba

]an hutu,Tsiren nan kin san in ba ki ci

ba zai lalace.Ku]i in na ba ki sai ki je fa ki

taskance,Abincin cina ko sai kin so kika

girkawa.*

Ni na }oshi kuma ku]in gidanika aikawa.

*Kalamaina yau gatse-gatse kika

amsa min.Yau na gane nufinki so kike fa

ki sa~a mim.To shikenan, duk abin da zan yi

ki ce amin,Yau zan mutu lallai ga Rabbi zan

zam komawa.

Kin tsaida ayyukana, dawayya,Kalli idanuwana, dawayya,Rama cikin jikina,Ya zan da rayuwata, dawayya.

* Wayyo masoyi ka tafi ka bari ni,Ya zan yi ni da raina, dawayya.

*Masoyiyata yaya zan bar ki,Kin ]auki rayuwata.

*Kullum a zuciya kai ne tsani,Farin wata da rana.

*Fa]i a hankali za}in baki,Ke dai ki nuna }auna.

*Albishirinka nawa, dawayya,Kai dai ka }yale kowa, dawayya,Ka san ni tun da]ewa, dawayya,Ni ba ni kula kowa, dawayyaKai ne farin wata mai dawayya!

*Masoyiya ki ]an saurare ni,In ba ki ]an batuna, dawayya.

*Fa]i fa]i ina saurarenka,

*Ka ma mutu man, in ka tafi miji

zan sakewa!* (Cashewa)

Don Allah taso fa, maigida faka san wasa,

Gama niyyata a ce naka sa-in-sa.Abin da ka yi man da safe ran

nan shi yas sa,Amma komai ya wuce abar ma

hangawa.*

Haba, na gwada ki ne kawai donramawa!

*Amma ka shammaci zuciyata ta

gamsu,To shikenan zo mu je mu zauna

mu yi hutu.*

To ba komai ai a yau fa lallai yakyautu,

In ]an ci abinci da ]an ruwadon walawa.

*Gari ya waye dukkan duhu na

yayewa (x2).

--------------------------------------

�DAWAYYA�

Fim : DawayyaKamfani : Iyan-Tama Multime-

diaFurodusa: Ahmed S. ElkanawyRerawa : Musbahu M.Ahmed,

Zuwaira Mohammed.Shekara : 2001

Ahayye dawo dawayya! (x2)*

Dawo masoyi dawo, dawayya.Dawo in ba ka dawo, dawayya.Hula zan ba ba ka dawo,

dawayya.Wando in ba ka dawo, dawayya,Dawo in ba ka riga, dawayya.

*Hula zan ba ka shirya, dawayya,Ga riguna ka sanya, dawayya,Ka zo mu ]auki hanya, dawayya,Mu yo rawa mu juya,Domin ka ]ebe kewa, dawayya.

*Dawo masoyiyata, dawayya,Dawo mu samu bauta, dawayya,Aurenmu na da tsafta, dawayya,Wa za ya fi ki gata, dawayya,Babu kamarki guna, dawayya.

*Kin ]auki hankalina, dawayya,

Farin cikina raina, dawayya.*

Kin san da ni da ke mun hautsani,

Na nuna so da }auna, dawayya.*

Fa]i fa]i ba shakka da }oramata }auna

Taho taho mu shirya dawayya,Aurenmu za mu shirya, dawayya,Wa za ya ja da baya, dawayya,Wallahi babu }arya,Babu kamarka zo mui dawayya.

*Toho taho mu shirya,Aurenmu zamu shirya,Wallahi babu }arya,Babu kamarki zo mui dawayya.

*Ahayye dawo, dawayya,Ahayye dawo, dawayya.

*Ahayye dawo, dawayya,Ahayya dawo, dawayya.

*Dawayya dawayya dawayya!

Fim : Mujadala 2Kamfani : FKD Production.Furodusa : Ali NuhuRerawa :Yakubu Muhammad

da Rabi MustaphaShekara : 2001

Lai lai lai la}anin }auna arerere,Bankwana makashin bege arerere

(x5)

To �yan mata zan yo maku caffa,Ku zo da ]ai ]ai kui min rumfa,Ka-ce-na-ce tsakaninku ku binne

ku shafa.*

Alo tsiya makamin fitina ne,Fushi na zuciyarku ku daddanne,Gani-gani gare ni fitsara ne,Kuna ta zantuka kui ta fushi da

sarfa.*

{yan}yasa na }wai fa halitta ne,[an duma a so ka lalura ne,Zantuka a kan ka jidali ne, Ka }ara yin gaba wata}il ka ga

saffa-saffa.*

Gasa da �ya mace yaka yi sosai,Tafin hannunmu kai kake ka ji

sosai,Duk tsiro na kirki zai rassai,

�LA{ANIN {AUNA�

Ka duba mu biyun ai mun zarcesaffa-saffa.

*Garga]in ka zan yi a kan bege,Ba ni yaudara a cikin bege,Ni hani da shi zan daddage,Har fa masu yi zan binne su in

shafa.*

Ban da kai, irinmu ake raino,Ba mu ba gida ya ya]on bono,Kai ka je gare mu ka tattono,Ji na masu ji da karan kansu yau

ka shafa.*

Na yi mafarki na afka a gidancinnaka,

Na rasa launi na gadara tamkarhankaka (x2)

*Lai lai lai la}anin }auna arerere,Bankwana makashin bege arerere

(x2)*

Gyangya]i nake fa ku tada ni,Sagegeduwa nake fa ku sanya

ni,Tarko ga zuci na yi asara ni,Ku taimaka fa raina ko ta yi saffa

saffa.*

Salo-salo na yaga ma zan yi,Gwadogwado garin da ake sanyi,

35

Page 37: Mujallar Bidiyo - Yuli/Agusta 2001

BIDIYO Yuli/Agusta 2001

Amalala.*

[an yaro ga mai magani.Ni dai ba na shan magani.Yaya ba ka shan magani?Ran nan mai maganin ya ce da ni

Amalala.*

Amalala mai fitsarin kwance,Saurara za ka sakankance,Shawara ko za kai dace,Ka je ka fito yanzu,In kai ka garin Amalala.

*Ni Zariya za ni in kankane,Tunda su a gun su ibada ne,Amalala a gun su abin so ne,In dai ]an gaye ne,Gurinsa a ce amalala.

*[a da uba da uwa kwance,Sun kwanta duk sun lalace,Kowane ya tsula kwance,Murna ta rufe kakarsu,Ta shirya bikin amalala.

*Ayyara iye nanaye,Ya ayye raye amalala (x2).

*Amalala Amalala Amalala.

*Musbahu ya shaida wa mujallarBidiyo cewa ya shirya wannanwa}a ta �Amalala� ne sabodatun can sunan fim ]in kenankuma akwai mai fitsarin (SaniMo]a) a cikinta. Batun sakasunan Zariya kuwa, Musbahuyace shi dai ya sanya sunan garinne don wa}ar ta yi da]i, ba donzambon ramuwar gayya gaZazzagawa ba.

--------------------------------------

�TAURARINKANO�

Fim : Mu Sha}ata na 3Rerawa : Sharu Sadi

SharifaiRubutawa : Ibrahim

MandawariRana: 28/03/01

Ruwa, ruwa na Allah,Na Annabi mai suna da

da]i.*

Ali Nuhu: Wannan ranamun yi sa�a,

Duk mun ce e babu a�a,Kowa sai kyawun ]abi�a,

Zufa idan ka zo dole fa ka yi,Idan na ce ka je ka gani ka zamo

karfa.*

Wanzan shi ya }yamaci jarfa,Na yi sallama kar ka ji wai fa,Ni da kai iyaka kai kulfa,Kar ka maida mu sai ka ce wasu

karfa.*

Kar ku yada ni a cikin tur~a,Na sako farar taguwa shar~a,In na tsunduma a cikin tur~a,Har a rayuwarta ta }are tabo ta

shafa.*

Na yi mafarki na afka a gidancinnaka,

Na rasa launi na gadara tamkarhankaka

*Lai lai lai la}anin }auna arerere,Bankwana makashin bege arerere

(x2).

--------------------------------------

�[AN�ADAM�

Fim : Zumunci 2Kamfani : Zainab Film Produc-

tionsRubutawa :Alkhamees D.

BatureRerawa : Sadi Sidi Sharifai

[an�adam mai sauyawa, butulumai bijerewa,

Ha]ama da gaggawa, halinsawahalarwa (x2)

*Ga halinsa na hawainiya,Kan ka }yafta ya sauya,{arshe yakan juya maka baya ba

}arya (2)*

[an adam shi ne butuluBincika cikin }aulu,In ya sami �yar daulu,Zai sauya ba wahala.

*[an adam mai mantawa,Bai so yana ramuwa,Ga halinsa na rainuwa,Shi ka]ai yake ginuwa (x2)

*[an�uwana ya yada niBai tunani ko }an}ani,Wahalar da nai ya sani,Guduwa yake don ni (x2)

*Ya manta nayi dawaniya,Yau yake juyan baya,

Halinsa �yan duniya shi yake tajuyawa.

*[an�uwana yau don ku]i,Ya guje ni gaba-ga]i,Duniyar ga mai ru]i,Ta hana mu yi ta]i.

*Su ku]i sukan haukata,Mai hankali ya ~ata,Halinsa mai nagartaYa zamo na lalata (x2).

*Rayuwata na sallama,Na yi bayani ba gardama,Darasi irin na zama,Na koya ba tantama.

*Wasu ma samun duniya,Na sa su bar hanyaMai kyau zubin shiriyaDomin samun duniya (x2).

--------------------------------------

�AMALALA MAIFITSARINKWANCE�

Fim : AmalalaKamfani: Usmaniya Film Pro-

ductionFurodusa: Musbahu M.

AhmadRerawa : Musbahu M. Ahmad,

Zuwaira Mohammed.

Ayyara iye nanaye,Ye ayya raye amalala.

*Amalala mai fitsarin kwance,Ya tsula, ya kuma tsulawaYa bar gwaggwansa da wankewaGwaggwansa da wankewa,Babanshi yana bulala.

*[an yaro yaka mu je wasa.A�a ni ba ni zuwa wasa.A kan me ba ka zuwa wasa?Ran nan na je wasa yara sun ce

Amalala.*

[an yaro yaka mu sai tsire.A�a ni ba na cin tsire.A kan me ba ka cin tsire?Ran nan ma mai tsiren ya ce da ni

Amalala.*

[an yaro ya ka mu je zance.A�a ni ba ni zuwa zance.A kan me ba ka zuwa zance?Ran nan na je zance ta ce da ni

Sai kirki da zama na da]i.*

Tahir Fagge: Ba sauran sharrida suka,

Ko kuwa harbin nan na iska,Babu harara babu duka,Ba ]aga murya babu kau]i.

*Ruqayya Umar: Mu yau duk

mun ]aura niyya,Za mu ha]e kai ba }iyayya,Ba baMbanci ba hamayya,Sai dai mui ta zama na da]i.

*Ibro: Da ma can mu �yan�

uwa ne,Duk asalinmu gari guda ne,Addininmu iri guda ne,Allah sa mu haye sira]i.

*Ruwa, ruwa na Allah,Na Annabi mai suna da da]i.

*Bashir Bala Ciroki: Ai mun

]au babbar sana�a,Wasan Hausa cikin jama�a,Fatana Allah ba mu sa�a,Mui aiki a cikin nisha]i.

*Shu�aibu Kumurci: Ni dai

yau na share hanya,Sannan na ]auro aniyya,Gun manyana sai biyayya,Don ba na so nai zumu]i.

*Iyan-Tama: Mu manyan mun

sami suna,Don haka mun jawo }anana,Sai ladabi da mutunta juna,Domin duniyar nan da fa]i.

*Fati Mohammed: Mu mata ba

ma ]agawa,Nan ga maza yau babu tsiwa,Ba kwakwazo babu kuwwa,Sai dai mui ta zama na da]i.

*Ruwa, ruwa na Allah, na

Annabi da da]i.*

Saima Moh�d: Harha]a kaishi ne sawaba,

Kun ga tafarki ne na riba,Ci gaba alheri da haiba,Shi zai sa mu cikin nisha]i.

*Shehu Kano: Duk sabon da

mukai a baya,Wato giba ko hamayya,Ko wani }yashi ko }iyayya,Allah yafe duk zunubi.

*Hajara Usman: Alhairi naka

36

Page 38: Mujallar Bidiyo - Yuli/Agusta 2001

BIDIYO Yuli/Agusta 2001

so gare mu,Kowa fatana ya samu,Ba na son sharri a gun mu,Wannan shi ne ya fi da]i.

*Mandawari: Allah ba mu ruwa

ya wankeDuk zunubin da mukai ya

narke,Kowa sai haske da haske,Kowa aljihu da kur]i.--------------------------------------

�RUWA RUWASHALELE�

Fim : HauwaKamfani: N.B. EntertainmentRerawa : Yakubu Muhammad.

Amshi: Ruwa Ruwa ShaleleRuwa Maraba da Lale RuwaGarai Son Raina x2 shalele

Mace: Mu wataya don begeA girgiza ba }wangeDoki na so don begeShi ne muradin raina.

*Namiji: Farin cikin begenki, Sahiba ke kanki,Kin san ina ko]a ki,Ki sanyaya min raina.

*Mace: Wallahi kai naka ]oki

M U S B A H U N A M U K OM I S B A H U W A N C A N ?

SHAHARARREN mawa}i wanda sunansa ya fito fili tundaga wa}ar �Sangaya� wadda ya rubuta kuma ya rera,Musbahu M. Ahmad, ya so ya yi abin mamaki. Kwanan nanmawa}in na Amalala ya yi yun}urin kammala rubuta sunansada adireshinsa da haruffan farko daga wasu sunayen wa}o}ida ya za}ulo daga cikin wasu finafinai wa]anda shi ne yarubuta su. In ka ha]a su, za ka sami MISBAHU M AHMADUSMANIYYA FILM KANO. To, gyara dai a nan shi ne, baMISBAHU mawa}in ke rubutawa ba, MUSBAHU muka sani.Sai dai ko in wani Musbahun ne. Sannan ba FILM ake rubutawaba, FILMS ake rubutawa. A }arshe, wasu wa}o}in da ya lissafabai fa]i a wa]anne finafinan suka fito ko za su fito ba. GaskiyaMusbahu sai a sake komawa kan kujera a yo wani tsarin, ko agyara wannan. Za mu jira ka!

�Mun {osa� ta fim ]in Adali�Ilu Kai Ne Nawa� (Samodara)�Sangaya� (Sangaya)�Ban Da Komai� (Sangaya)�Amalala� (Amalala)�Hassana Da Usaina� (Hassana Da Usaina)

�Umbolo Bolo�

�Mu Daina Gaba� (Sa}o)

�Alalo Alalo Ta~akaka (Amalala)�Hawaye��Mun Yi Murna� (Biyu Babu)�Ahayye Sama Ruwa� (Sha Daka)�Dawayya� (Dawayya)

�Uwo Uwo��Samodara� (Samodara)�Mun Gode Allah��Alo Lilo� (Laila)�Namalle� (Samodara)�Iye Iye Ciro Gwaiba� (Zumunci)��Yar Fulani� (Idaniyar Ruwa)�Ya Masoyi� (Bushara)�Ai Zancen {auna� (Zato)

�Filaya��Iya Zubar Ruwa� (A}iba)�Lililo Da Dariya� (Haya}i)�Maigida Ka Taso Mu Yi Wasa�

Agajinka da sau}i Nake bi]a mai mulki A zuciyata raina.

*Namiji: {aunarki don na gada Batunki randa-randa Nake da shi ba gaba Na so cikar ruhina.

*Namiji: Taho ki zo gaggauta So nake yi ki furta A so ki ]an siffanta Ki jinjina don }auna.

*Yarinya: Allahu zai saka min Tunda ka }wace min Rezata ka kar~e min Rashinta na damuna.

*Namiji: Meye kuke tababa Kar ta kai ku ga gaba Ku zo na ]an dudduba Fa]anku na damuna.

*Yaro: Wai don fa ni na kar~a Rezar hannunta na kar~a Don kar ta yanke baba Shi ne take zagina.

*Yarinya: Ni dai ka ban rezata Kawai ka ba ni abata An ba ni ita ne kyauta Ka ba ni ya yayana.

*Namiji: Tsaya tsaya ya �yata Lafiyarki ya �yata Rezar ya kakkar~e ta

Rauninki bai so kana.*

Yarinya: Yau Baba ni na lura Ba a sona gara In ma tafi nai }ara An goyi bayan yaya.

*Yaro: Haba haba }anwata Baba bai bambanta Abin da shi ya kwatanta

Shi ne fa har rayina.*

Mace: A kul ki bar zancen nan Na gaya miki ran nan Da shi da ke �ya�yan nan Ai duk ]aya kuke guna.

*Namiji: Ruwa ruwa shalele Mu iyaye lalle Muna maraba da lale Shirinku ya �ya�yana.

*Yaro: Ruwa ruwa shalele Mu fa �ya�yan lele Muna maraba da lale Zuwanka ya abbana.

*Yaro: Ki ce ki ce shalele

Ruwa ruwa shalele Mu fa �ya�yan lele Muna maraba da lale Zuwanka ya abbana.

*Namiji: Babarku fa Babarku fa!

*Yaro: Au! Ruwa ruwa shalele

Mu fa �ya�yan lale Muna maraba da lale Zuwanki ya ummina.

*Yaro/Yarinya: Ruwa ruwa

shalele Mu fa �ya�yan lele Muna maraba da lale Zuwanki ya ummina/

abbana.*

Namiji: Ruwa ruwa shalele Mu iyayen lele-lele Muna maraba da lale Shirinku ya �ya�yana

*Yaro: ShaleleYarinya: ShaleleYaro: AbbanaYarinya: Ummina.--------------------------------------

�KI TAHO �YARHALAK�

Fim : Wasila 3Kamfani: Lerawa FilmsRerawa : Sharu Sadi Sharifai da

Zuwaira Muhammad

Jamilu: Ki taho �yar halak ki barguranta min;

Ki taho �yar halak ki bar muzantani.

Ki bar kau da kai ki ]an sassauta

�Kin Burge Ni Birthday [inaKin Zo (Sakamo)

Ayye Yara Dandalili (A}iba)Nab bab (Kada Mage)Oni Lando, Lando Na Bani �

(A}iba)

Musbahu M. Ahmad37

Page 39: Mujallar Bidiyo - Yuli/Agusta 2001

BIDIYO Yuli/Agusta 2001

min,Ko ki bar yin fushi ki ]an

rangwanta minRo}ona da ke ki ce �Allah amin�In na aure ki babu mai guranta

minZuman nan ta ragaya ]an ]ebo

minIn sha don in kere dukkan mai

�yam min.*

Saliha: Kai jaye ka ban wuri niba na sonka

Ni da }awata mun ka je ofis]inka

Wai har ni ka ce wa in saurare kaYanzu ko ka ga na ha]e na zu}e

kaShi ne ka lalla~o ka zo, don in so

kaNi ma ]an jira ni zan kirawo ka.

*

Jamilu: To ai ni Jamilu komaiban cewa,

Tunda a kan }aunarki na zamtowawa,

Nai laifi amman ki zamtoyafewa,

Mui komai aurenmu mui tamaidawa,

Komai ya wuce sai daijajantawa,

In dai kin fushi ki zamtohucewa.

*Saliha: Kai ni Saliha fa ka ban

mamaki,Duk an san ni kan yawan halin

kirki,Amma don kawai ka ]ora min

hakki,To yanzu wai da ma kake da]in

bakiAi ni ba ni son yawan ciwon

bakiDa dai za ka bar ni zai fi min

sau}i.*

(CASHEWA)

Jamilu: Alkhairin kare fa ba akai wa kura,

Mai ilimin abin ake kai wagyara.

Ni yau ai gurinki ne na yo}aura,

Sai kin ce da ni taho don muihira.

Ya ke Saliha da ke za mui gyara.Mai kirki ake kusanta don hira.

*Saliha: Na ce kai na ce da kai ba

na zance,Ai sai ya zamo maza na tantance,Hujjata ko ba ni jin da]in zance,Akwai lokacin da zan hankali

kwance,Don laifin da kai yi min sai na

huce,Kuma duk kalmominka sai na

tantance.*

Jamilu: To Saliha wai me kike soin ba ki?

Domin na ga kin koma kin sokan ki.

To Saliha wai me kike so in baki,

Domin dai in sami tsantsaryardarki?

Ni dai zahiri ina tsantsar son ki.*

Sai nai shawara sannan zan kar~eka,

Kuma sai na ji dukkaninhujjojinka,

Ban �yan kwanaki zan ]ansaurare ka!

[aya daga cikin taurarin fim mafi shahara...

ta yi aure a ran 15 ga Yuli, 2001

* AUREN TARIHI NEWANDA �YA�YAN ZAMANIBA SU TA|A GANINIRINSA A KANO BA...

Mujallarku mai farin jini

tana cikin ’yan bikin. Don samun cikakken labarin bikin, nemiFIM ta watan Agusta ... a farkon watan, don samun sahihin labarin.Rabu da kame-kame da ji-ta-ji-ta, nemi mujallar FIM!

Fati da angonta Sani Musa a ranar bikin aurensu

* KOWA YA AMINCE DA CEWA BA A TA|A NUNA WA WANI[AN WASAN FIM NA HAUSA SOYAYYA IRIN WANNAN BA!

HO

TO

: Bal

a M

oham

med

Bac

hira

wa

Jagorar Mujallun Hausa

38

Page 40: Mujallar Bidiyo - Yuli/Agusta 2001

BIDIYO Yuli/Agusta 2001

�NA ZO SALLAMADA �YAN�UWANA�(wa}ar bankwanan Maijidda)

Fim: Mu Sha}ata na 2Furodusa : Ibrahim

Mandawari

AMSHI: �Na zo sallama da�yan�uwana ,

Zan kama hanyar gidan mijina.�

Ga Jallah khali}u nai tasbihi,Gurin Muhammadu naitaslimi,

Zan so na yo batu kan aurena.*

Ya �yan�uwana ku yi saurara,Don ga batu nan da za ni tsara,Fata ku tattaro ku ji zancena.

*Wasan kwaikwayo da na ]an

soma,Wato ina nufin wasan dirama,Yau ga shi na bari nai

bankwana.*

Domin bikina ai ya zo ne,Sauran ]an ka]an a sa ni a

lalle,In tafi gidan miji in yi bikina.

*Maijidda ni dai na kama dahir,Ango Abubakar kai ne zahir,Ni ce uwargida kai ko mijina.

*Domin ko Abba ya umarce ni,Na tsaida sunna na yi addini,Na kama hanyar gidan mijina.

*Finafinan duk da na ]an ]ana,Don masu kallonmu su amfana,Ba don ku]i nake yin zarafina.

*(CASHEWA)

To ga shi al�amari yau ya }are,Don }arshen wata ni za ni tare,Wato ina nufin za ai bikina.

*Idan hali ma ]an gana,In babu hali sai wata rana,Ko nan a duniya ko Aljanna.

*Na yi ba}in ciki da za ni bar

ku,Ba ku ganina ba ni ganinku,Sai dai cikin kaset ko hotona.

*Sarauniya ina yin begenku,Iyan-Tama ina gaggaishe ku,Mandawarin Kano sai wata

rana.*

Hafizu har ma da Nura Ilu,Ahmad har ma da Ali Nuhu,Ina ta sallamar yin bankwana.

*(CASHEWA)

Fati ki marmatso ki kai ni ]aki,

Ibrahim Mandawari, dilasarkin wayo! A lokacin da yatsinkayi auren fitattun �yanwasan nan biyu MaijiddaAbdul}adir da Fati Moham-med ya }arato, sai ya yi wuf,ya yi wani tsari. Sai ya rubutaabin da ya kira �wa}arbankwana.� Ta Maijidda

daban kuma ta Fati daban.Aka saka su a shirin�Mandawari Enterprises�, MuSha}ata na 2 da na3. Fati cetake rera tata a kashi na 2wanda ya fito kwanan nan,kuma Maijida za a gani tanarera tata a kashi na 3 wandabai fito ba. Kamata ya yi a ce

finafinan na Mu Sha}ata sunfito a daidai lokacinaurarrakin, amma matsalolisuka hana. Ko da yake dai suFati sun tafi, furodusan zaici gaba da cin moriyarsu tawannan sabuwar hanya. To,amma ba a nan ka]ai ba,�Baban Soyayya� ya fa

Wakokin bankwanan Maijidda da Fatikarrama �yan wasan ne. Ya citudu biyu kenan, gakarramawa ga wazgar riba akasuwa. Babu mamaki idan]an wasan kuma darakta yashirya wa}ar bankwananAbida ko Saima a nan gaba.Allah ya kai mu! Yanzu daiga wa}o}in bankwanan:

Maijidda Abdulkadir Fati Mohammed

Ke Abida ki zo taya ni kirki,Wato ina nufin girkin bikina!

*Wasan kwaikwayo da masu yin

shi,Duk ku ha]e kai ku daina yin

shi,Ro}o nake muku ku ji zancena.

(CASHEWA)*

Maijidda ni dai yau na bar ku,Laifin da kun yi min na yafe

ku,Ni ma ku yafe min laifina.

*Ni dai sallama cikin salama,

Zaman da nai da ku ba ninadama,

Kowa ya zo ]aurin aurena.

------------------------------

�SUNNARKA NAKETA SO IN TARAYAWA�

(Wa}ar bankwanan FatiMohammed)

Fim: Mu Sha}ata na 3Furodusa : Ibrahim

Mandawari

Amshi: Ya Muhammadu,Sunnarka nake ta so in tarayawa.

Hamdu Lillah,Tun da ni na gode Allah,Nai salati gurin Rasulu, Al�aminu batunka ba nidainawa.

*�Yan�uwana,

39

Page 41: Mujallar Bidiyo - Yuli/Agusta 2001

BIDIYO Yuli/Agusta 2001

Sai mu ]au ha}uri da juna,Tun da yau za ai bikina,

In wuce kuma ni da kubabu ganawa.

*In yi aure,

Nan ga Sunnata na kare,Ka ga wasa ya fa }are,

Na dirama tun da yau za nidainawa.

*Ni fa Fati,

Kun ga yau na ]au garanti,Na bar yawo a titi,

Tun da aurena a yau za a]aurawa.

*Ya mijina,

Ka zamo ~arin jikina,Sani kai ne rayuwana,

Ko a aljanna da kai za muzaunawa.

*Ya ka Sani,

Wani kyakkayawa amini, Mai biyayya mai addini,

Da ganina sai ya ce za yaaurewa.

*Ku]i na zance,

Ya fa kawo an amince,Wanga yaro ya yi dace, Don iyayena kakaf sun

amincewa.*

Masu so na,Daga ku har ma}iyana, Ku yi min afuwar halina, Tunda ni a gare ku ai ba

ni rainawa.*

�Yan dirama,Wasu mata masu homa,Masu son su zubar da }ima, A�a ha lallai ku tuba ku

dainawa.*

Sun tsane ni,Da can sun tsangwame ni,�Yar }auye �yar Fulani,

Ga shi yau Allah gwaniya yi sakawa.

(CASHEWA)*

Ya Muhammadu,Sunnarka nake ta so in tarayawa.

*Tauraruwa ni,

Na zamo haske a birni, Kowa na so ya gan ni,

In na keto ko�ina sai

tafawa.*

Ga ziyara,Ta gidanmu manya da yara, Ga wasi}u na kwarara,

Har a kullum masu sonasuna zowa.

*Kyautuka ma,

Na ku]i da su sutturu ma, Kun ga albarkar dirama, Kowa Fati ake so ya

dan}awa.*

Na gode Allah,Na zamo hasken fitilla, Kuma har na tsaida salla, Kuma alhairi a kullum

yana zowa.*

Masu kallo,Na yaba muku nai adabo, Tun da ni yau na ci }wallo, Wato nasara gare ni take

zowa.*

(CASHEWA)

Ya Muhammadu,Sunnarka nake ta so in tarayawa.

AssalamuAlaikum �yan�uwanmu, Mata da mazan cikinmu, Na yi bankwana da ku sai

ku amsawa.*

Yau bikina,Na gayyaci �yan�uwana, Manya har }an}anana, Kowa na gayyato babu

fasawa.*

Manyan }awaye,Ga su Biba manyan iyaye, Da su Saima ayye arauye, Ga su Rabi �yar Mustapha

ma suna zowa.*

Addu�a ce,Za ku min domin na dace, Domin auren ya zarce, Ya yi dan}o ba saki babu

fitowa.*

Na fa bar ku,Sai a ranar da na haihu, Sannan zan gayyace ku, Fatana dukkaninku ku

amsawa.*

Ya Muhammadu,

Sunnarka nake ta so in tarayawa.

*Ya Muhammadu,

Sunnarka nake taso in ta

Fati: Daga rera wa}a tazarce da kukaFATI Mohammed, wadda wa�adin kwanakintaa harkar fim ya }are a ranar 15 ga Yuli, ta ba damamaki a wajen rera wa}ar bankwana dashirin fim da kuma su kansu masu shirya fim]in. Wannan ya biyo bayan aurenta da SaniMusa (Mai Iska), auren da bikinsa ya kusajanyo tarzoma a Kano.

Wa}ar da aka ]auka a faifai za ta fito ne acikin Mu Sha}ata na 3. Ana ]aukar hotonwa}ar a cikin ]aki, Fati tana zaune tanarerawa. Kamar wasa, sai da ta yi baitika hu]utana murmushi, can mai kyamara bai ankara basai ya ga ta fara so~are baki. Ba ta gama baitina biyar ba sai ta ~arke da kuka.

A ta}aice dai, haka ta }arasa sauranbaitukan tana kuka. Duk wa]anda ke wurinsuna kallo sai tausayi ya kama su matu}a.Daidai lokacin da ta gama wa}ar, maimakonFati ta tashi ta bar wurin, sai kawai ta yi zaunekan kujera tana rusa kuka har da hawaye shar-shar. Allah Sarki, }aryar kwaram-kwaram ya}are wai mai kalangu ya fa]a ruwa.

Ina masoyan Fati? Tunda ba irin ruwan daza ku shiga ku ceto ta ba ne, ku ma sai ku yi tarusa kuka.

Duk a wurin wa}ar dai, fitacciyar yarinyamai tashi Abida Mohammed ta gabatar da Fatiga masu kallo. Gabatarwar an yi ta ne tamkaririn shirin nan na gidan talbijin da �yan jariduke gayyato ba}o.

Abida, wadda ta fito a matsayin �yar jarida,a shirin, ta yi wa Fati tambayoyi kamar haka:

Abida: Ko za mu iya jin sunan Fim ]in dakika fara kallo?

Fati. Fim ]in da na fara kallo shi ne Ki YardaDa Ni.

Abida: To baiwar Allah wanne fim kika farayi da kika shigo harkar fim?

Fati: Fim ]in da na fara yi shi ne Da Babu,wanda kamfanin �Ibrahimawa Production�suka shirya.

Abida: Daga cikin finafinan da kika yi,wanne ne ya fi kwanta maki a rai?

Fati: Gaskiya suna da yawa, amma dai donAllah sauran furodusoshi su yafe min kuma suyi ha}uri. Fim ]in da na fi ji da shi bai fito batukuna, shi ne...

Fati dai ta fa]i sunan fim ]in, amma a donkada mu ha]a ta fa]a da furodusoshi mun }ibayyanawa don ta sami damar shan amarcilafiya. Mai so ya sani ya bari fim ]in ya fito. Alokacin ta yi masa nisa.

rayawa.*

Ya Muhammadu,Sunnarka nake taso in ta

rayawa!

40

Page 42: Mujallar Bidiyo - Yuli/Agusta 2001

BIDIYO Yuli/Agusta 2001

�Ni ne wanda yake ba da umurni,watau wanda ya yi tunanin yadda yakamata a tsara hotunan yadda masukallo za su gan su,� inji shi.

A kan yadda ya yi daraktan shirin,sai ya ce, �Ni na yi tunani na kuma tsara.Ma�ana mai ba da umurni yana tunanisosai wanda kamar littafin Maganar JariCe wadda labaran an yi su ba a yanzuba, wanda ba ci gaba ba. Ana rayuwa ceta da. A yin fim ]in mun ri}a nuna dace, lokacin da yake ba wayar lantarki,babu wani abu wanda zai nuna yanzu.Haka ma su kansu wa]anda za su fitosai muka sanya su su fito ba alama kowani kamanni na yanzu ko ]inki � dukdai yadda mai kallo zai kalla ya ga dace yake gani, shi ne muka tsara, wandani na ba da umurnin.�

Alhaji Ibrahim ya ba da tarihinsa harzuwa yin fim na Magana Jari Ce dacewa: �Na fara aiki a gidan talabijin na

Daga DANJUMA KATSINA

LITTAFIN Magana Jari Ce shi nelittafi mafi kar~uwa da kumatasiri a adabin Hausa. Littafi ne

wanda aka yi amfani da hikima dabasira wajen rubuta shi, aka kuma isarda sa}o mai amfani ga mai karatunsa.Ba littafin ba, hatta fim na wannanlittafin sai da ya ratsa zukata, kuma yayi tasirin gaske.

Dokta Ibrahim Malunfashi, ]anjarida, marubuci, kuma malamin jami�a,ya ta~a bayyana (a wani sharhinsa)marubucin littafin, marigayi DoktaAbubakar Imam, a matsayin wanda baa yi ba kuma babu kamarsa. Saninmuhimmancin marigayi Dokta Imam yasa lokacin da NTA Kaduna ta fara ]aukarwani shiri mai kama da kishiyarMaganar Jari Ce ya sa Malumfashi ya]au al}alami don kariya ga wannanhikima da Allah Ya aje ga adabin Hausa.

Wata rana ina a zaune a ofis ]inDaraktan Watsa Labarai na gwamnatinJihar Katsina, Alhaji Ibrahim Boyi, saiga Umaru [anjuma Katsina (kada kadamu da sunan, ba ]ana ba ne!) da wanishaharren ]an wasa sun shigo. Su Alh.Umaru (wato Kasagi) su ne suka yi fimna Magana Jari Ce. Sai kawai na ji sun]auko tarihi na yadda suka yi fim ]inda kuma wasu finafinan na Hausa.Tattaunawar ta yi matu}ar burge ni, harnan take na ji cewa bari in zaro rikodatain yi mujallar Fim aiki.

Alhaji Ibrahim Boyi shi ne wanda yajagoranci shirin fim na Magana Jari Ce,wancan na farko wanda aka ri}a nunawa duk �yan Nijeriya, ba wannan wandaNTA Kaduna suke so su yi ba. Ya ri}emu}amai da yawa a gidajen talbijin,ciki har da shugaban gidan Rediyo daTalbijin na Jihar Katsina. Yanzu kumashi ne mai ba Gwamna Umaru Musa�Yar�aduwa shawara a kan harkokinwatsa labarai.

Kaduna tun lokacin ana Rediyo-Talabijin (RTK) a matsayin mai ]aukarhoto. Tun ina yaro ni mai tsananinsha�awar fim ne; tun ina firamare nakeyanka hotuna in samu batur a sa �yarfitila. In na yanka hotunan sai in ri}akanga su a jikin fitila sai inuwarsu tari}a fitowa a jikin bango. Wanda nakanyi shi a wani ]aki wanda yara masushiga su kalla suna biyana ina amsarkwabo da ]ari ne. Masu yara bisa turmisuke biya na kwabo, masu yaran }asasuke biyana ]ari ]ari.

�Kuma a lokacin duk rana in zan yiwannan kallo sai in ri}a yawo unguwaunguwa, ina fa]i ma yara ga abin da zamu nuna da dare. Duk ku]in da na samuda dare, to da safe da su zan yi amfaniin sayi batura in kuma sayi wasulittattafai (exercise books) da zan yiamfani da su in sake wani zanen wandazan nuna a dare na gaba. Ina da wannan

Yadda muka shirya wasan

Alh. Ibrahim Boyi yana amsa tambayoyin marubuci Danjuma Katsina

– Boyi

41

Page 43: Mujallar Bidiyo - Yuli/Agusta 2001

BIDIYO Yuli/Agusta 2001

haza}ar ta nuna fim, in gacewa na yi irin wannan nuni.

�Ina a haka na kama aiki agidan talbijin. A lokacinBCNN ne na Kaduna. Na yikwasa-kwasai iri-iri, cikinsuhar da gidan talbijin na BBCinda na wo kwas a kan shirye-shirye na talbijin.�

Kafin yin fim na MaganaJari Ce Ibrahim Boyi ya yishirye-shirye da dama. Dagacikinsu akwai wasan nan naGidan Kashe Ahu wanda acewarsa shi ne ma ya }agoshi, suka fara yinsa. Akwaiwasu shirye-shiryen, irin suKarambana wanda shi ne ya}ago shi don ba da dariya.�A lokacin, gidan talbijin na}asa suna wasu shirye-shiryewanda mu ba su yi mana waniamfani. Sai manyanmu natalbijin irin su AbdurrahmanMincika suka ga ya cewa yakamata a cikin �Network�,watau talbijin da ake nunashiri duk }asa, mu sami wanilabari wanda yake an san shian yi wasanshi tunda alokacin su ma wancan~angaren suna irin wannan.�

To, sai aka tsaya a kan a]au Magana Jari Ce. Abu nagaba da aka yi shi ne sai suIbrahim Boyi suka faratambayar wa]anda suke daha}}in rubuta littafin, watauiyalan marigayi AbubakarImam, suka fa]a masuniyyarsu. Aka yi sa�a, iyalansuka ba da izinin yi.

Bayan wannan kuma saiaka tara wasu masana a kanadabin Hausa don saboda zaa ]auki labari ne daga cikinMagana Jari Ce a mayar dashi da Turanci yadda zaikasance ba a lalata shiwannan labari na MaganaJari Ce ba.

Don haka a duk lokacin daza a ]auki shirin, sai an samuwa]anda suke ba da shawararnan an nuna masu tsarin sunga shi ya yi daidai sannan ayi.

Alh. Ibrahim Boyi ya }arada cewa, �Mun kuma tuntu~iSarkin Zazzau da na Katsinaa lokacin don gudunmuwadon sabili da kayayyakin dawa]annan mutane za su sana sarakuna ne da maya}ansarakun gargajiya, dasauransu. Kuma wa]annansarakuna sun ba mu goyonbaya sosai.�

Bayan wannan ne aka faratunanin wa]anne �yan wasaya kamata a sa a cikin shirin?Wannan ya sa dole a samumutane wa]anda suna dasanin Turanci, kumaTurancin ba wai na �yankoyo ba, a�a wa]andaTurancin nasu mai ingancine, wanda ko Sarauniya ta jiza ta san me aka ce. Aikiwurjanjan. Aka kewaya dukgidajen talbijin a Arewa anaza}ulo su, wasu dagaMaiduguri, Sakkwato, dasauransu. Duk aka taru aKaduna, inda nan ne aka ri}ayin shirin

�Mun yi shiri da yawa akan litaffin tun dagafarkonsa har }arshe,� injidaraktan fim ]in. �Hattashirin aljannu duk munkwatanta mun yi. Mun yiiyakar }o}ari da sanin yaddaya kamata a yi mun yi.�

Alh. Ibrahim ya ce dukwannan aiki da suka yi, sunyine saboda kishi da suke dashi da kuma son su nunarayuwa irin ta Bahaushe tada, wato kamar yadda akeya}i, su nuna wa duniyaal�adunmu! �Ka san mailitafin ya ]auko ne dagarubutun Larabawa (da naTurawa), ya gyara daidai danamu,� inji shi.

To nawa aikin ya ci?�A lokacin ba mu kashe

ku]i masu yawan gaske bakamar yadda masu yin fimna yanzu ke kashewa,� injishi. Ya }ara da cewa, �Alokacin kowane shiri na awa]aya ana kashe kamarN100,000; dubu ]arin nanhar da ku]in da za mu ba sumasu yin wasan da man daake zubawa a motoci donzuwa wajen wasan, da ku]inabinci da komai da komai. Alokacin, ita gidan talbijin na}asa sun sami wa]anda suka]au nauyin a yi wasan.Wa]anda aka ri}a tallarsu acikin wasan. Wannan ya saabin ya zo da sau}i; lokacinkamfanonin sabulai na farinciki su suka ]au nauyinshirin.�

Alh. Ibrahim ya tuno dawani abu da ya faru a lokacin.�Saboda tsantseni da mukea yayin shirin, akwai lokacinda ana iya yin awa hu]u ba a]au minti uku ba. Don kuwasai an yi an yi, ana kuma

Sarki Abdurrahman dan Alhaji

Su Musa ’ya’yan Sarki

42

Page 44: Mujallar Bidiyo - Yuli/Agusta 2001

BIDIYO Yuli/Agusta 2001

tabbatar da cewa wa]annanabubuwa da za a nuna yadace da yadda ake so. Donhaka kowane shiri sai angwada sosai kafin a fara. Dukda cewa masu rubuta labarindaga Hausa zuwa Turancisun kammala sun aje kumamasu wasan ga su a shiryekoyaushe, ga kuma kayanaiki a tsaye. Duk da hakayana ]aukar mu kwanabakwai ne a shirya wasangida ]aya da za a nuna a satimai zuwa. Kuma tun da akafara na fara rasa wani lokacinawa na kaina; wani lokaciban dawowa gidana sai ukuna dare. Wasu na tsara labaringaba, wasu na shirya inda zaa yi shiri na gaba, wasu nashirya hotuna. Anakamallawa sai a ]auka sai ahau jirgi sai Legas. A Legascan ma akwai mai jira sai ya}arba. Sai sanyawa. Hakamuka yi ta yi har mukakammala.�

A lokacin da suke shiryafinafinan na Magana Jari Ce,su Ibrahim Boyi sun fuskancimatsaloli iri-iri, musammanna lalacewar kayan aiki. Inana tsakar aiki da yawalalla~ar �yan wasan ake yi,musamman kan batunha}}insu. In an yi jinkirin basu sai ka ga wata matsala takunno kai. �Wasu kuma �yanwasan mukan rabo su dagawurin aikinsu ne don su zo a

yi wasan,� inji shi. �Wasu saisun yi aikin nasu sun gamasannan za su zo ga namu.�

A �yan wasan da aka ri}a]auka akwai na din din din,akwai kuma na lokaci lokaci.

Babbar matsalar da sukasamu ita ce,a k w a ilokacin dashi Waziriya yihatsari damota har yakarye. Akakai shiasibiti aKano. To gashi za a yiwasa, kumaga babuyadda za ayi wani yacanje shi. Don haka ya akayi? Boyi ya ce, �Yadda mukari}a yi shi ne duk sati sai mukwaso kayan aiki zuwaKano, da duk wa]andaWaziri zai fito tare da su, (mukafa su) a cikin ]akinasibitin. Muka ri}a sanyazana muna yin shirin donWaziri ya fito.�

A labarin na Magana JariCe, babu inda Waziri yakarye, to amma a nan saisuka sa}a shi, kamar garinkilisa ne doki ya fa]o da shi.A cikin asibitin suka ri}a yinwasan. A lokacin Waziriyana kwance yana jinya.

Fadawa da su Musa a gaban Sarki Abdurrahman dan Alhaji

�Kuma muka ri}a tsara shikamar yadda da take, dayadda duk wata hikima tacewa yanzu ne wannanlokacin, har ya gama, shirinbai tsaya ba. Duk shiri saiWaziri ya fito. Don haka duk

sati sai munzo asibitin anyi shiri daWaziri.�

Tun farkolittafin har}arshensa balabarin da suBoyi ba su yiba sai wandaa lokacin baiy i w u w a ,wanda dayanzu ne zaiyiwu. Ya bada misali da

�Labarin Sarkin Busa�wanda ~eraye suka ri}a bi.�Akawai lokacin da ta kaihatta ginin ganuwa da fadarSarki Abdurrahaman duk saida muka yi don dai ya daceda fim ]in, wato ya dace dayadda labarin yake.�

Shin yaya aka yi har masukallo suka ga aku yanamagana a shirin? Menenesirrin abin? Daraktan ya yimana bayani. Ya ce, �Alokacin, bayan da mukasamo aku sai kuma muka yimasa tarbiyya sosai yaddaduk lokacin da aka nuno shizai ri}a kamar yana magana

ne. Mun ri}a samun waniruwa mai za}i kamar na lemoko ruwan rake muna ]igamasa a baki. Wanda daidailokacin da muke ]iga masashi kuma yana mui mui dabaki, sai mu sa kyamara tana]auka.�

To riba fa, tunda kila badon a burge kawai aka yishirin ba? A cewar daraktanshirin, a ku]in da aka kashean ci riba sosai daga abin daNTA ta samu. Amma yabayyana cewa, �Duk a ribarnan ba wani abin da aka basu iyalan marubucin littafindon ba su nuna suna so ba.Kuma da sun tambaya da anba su wani abu daga cikinribar da muka samu.�

Mun yi magana da Alh.Ibrahim Boyi a kan yiwuwarfito da fim ]in a kaset donkowa ya saya, musamman awannan zamanin na yayinfim. Sai ya kada baki ya ce,�Fim ]in yana da sceneshamsin da hu]u kuma ha}}ine na NTA ta }asa wadda itake da ikon kawo shi kasuwakowa ya saya don kallo.Wanda kuma tuni wasu sukafara yin magana a kan haka.Wata}ila nan gaba su fito dashi kasuwa.�

Wata}ila abin da daraktanbai sani ba shi ne a yanmzuhaka akwai ~arayin zaune(pirates) da suke sayar da fim]in na Magana Jari Ce agaruruwan Arewa.

Alh. Ibrahim ya kuma yitsokaci a kan sabon fim ]inMagana Jari Ce wanda NTAKaduna ke shirin fito da shida sunan The Adventures ofWaziri, wanda an sha ba dalabarinsa a wannan mujallar.Ga abin da daraktan ya ce,�A kan wani sabon fim kuwamai suna Yawon DuniyarWaziri, tun muna a NTA,bayan da aka kammalaMagana Jari Ce aka ga yaddaya kar~u da kuma tasirin daya yi, wasu suka fara ba dashawara a yi wani fim wandazai zama makwafin MaganaJari Ce, wasu suka kawowasu littattafai, wasu kumasuka kawo shawarar a ginawani labari mai ci gaba. Ansamu }in yarda sosai don kara baddalla ainihin labarin naMagana Jari Ce. Sai kwanannan na fara jin cewa har an}ir}iro kuma an fara.�

A labarin naMagana Jari Ce,

babu inda Waziri yakarye, to amma anan sai suka sa}ashi, kamar garinkilisa ne doki ya

fa]o da shi.

43

Page 45: Mujallar Bidiyo - Yuli/Agusta 2001

BIDIYO Yuli/Agusta 2001

SATAR AMSA:

* Abida* Abu Likoro* Ainau* Aisha* Cima* [ayyiba* Dumba* Fati Mohd* Hafsatu* Hajjo* Halima* Halisa* Hasiya* Hauwa Ali Dodo* Hindatu

A M A M A N W A S I Y Y A U

S U G I N D I Y A M I L A H

A I B R A S H I D A A I G X

B C I M A I A Y C Q S X H O

M U D A U L J Z Z H I V A R

U W A S I L A I A I M B J O

D F A T I M O H D N A R J K

J H A U W A A L I D O D O I

M U H A L I S A A T Z A L U

I T S I G A I P I U B N X B

A G D A Y Y I B A U L A D I

U T A S F A H T A M B A Y A

L U A M I S U A N I A Y P A

A M A S H A H A M A A K R L

�Yan Wasa Mata 30

* Jamila* Kanya* Ladi* Luba* Maijidda* Maina* MamanWasiyya* Mashahama* Rabi* Rashida* Saima* Sima* Tambaya* Tsigai* Wasila

Dubi tsarin da ke damarka a sabonshirinmu na Wasa {wa}walwa. Acikinsa akwai sunayen wasu �yanwasan fim mata (na da da na yanzu)su 30.Sunayen sun fito a gicciye, ko atsaye, ko a mi}e, ko baya-baya, ko}asa-}asa, ko gefe-gefe (dama dahagu). Muna so ku zagaye sunayen,ku ga ko za ku za}ulo su.

Wasa {wa}walwa

Za mu kawo amsoshin a fitowa ta gaba

dai mun ga yadda Alh. Murtala ya daurecikin talaucin da ya samu kansa a ciki.Mai kallo zai iya tunawa da wani hotongida da aka nuno mana a jikin bangonfalon Alhaji tun kafin ya talauce. A jikinhoton an rubuta, �Peaceful Home,�watau gidan da ake zaman lafiya.Wannan shin yana nufin gidan attajirine ka]ai ake zaman lafiya?

Sai kuma inda aka aiko daga kotudon a yi wa gidan Alhaji ku]i. Shin suwa suka kai }ara? Ya kamata a ce annuno shari�a a kotu domin ba mamakikotu ta tausaya wa Alhaji idan ta ganshi a cikin bandeji. Bayan an sai dagidansa kuma, matarsa ta ba shishawarar neman ]aki a gidan abokinsa.Abin mamaki, a kwance yake fa cikinraunuka amma kawai sai aka sake nunashi a }ofar gidan Malam Abdullahi yaje neman cin arzikin ]aki. Yaya }arshenInyamuri ya kasance?

Mai kallo kuma zai yi mamaki ganincewa wata kusurwar ]akin Halimadan}am take da samiru da dibaida ta

silba. Me ya sa ba ta yi tunanin saidasamira a yi wa Ahmed magani ba? Saiga shi bayan ya mutu ta ba da shawararmijinta ya saida kayan ]akin don yasami jari! Ya kamata a ceabokansa sun fi yabondauriyarsa kan ta matarsa.

A matsayin al}ali,Mandawari ya yi }o}arida ya }i goyon bayaniyayen Halima kan AlhajiMurtala ya sake ta. A nandarakta ya yi }o}arinnuna yadda ake adalci awurin shari�a. Sai daikuma bai dace a cemasinjan al}ali haka yake kace-kacecikin tsumman kaya ba.

Mace Saliha ya yi kyau, sai dai kawaiakwai matsalar fitar kyakkyawar murya.Su kansu �yan wasan sau da yawa ba aambatar sunayen wasu a ciki. Halimadai ta cika saliha. Amma dai AlhajiMurtala ya fi ta ]aukar }addara.

Wannan fim dai wasu �Yan�uwaMusulmai (Muslim Brothers) ne sukashirya shi. Wannan ya nuna fahimtarda suka yi cewar fim hanya cemuhimmiya ta isar da sa}o. A wurintaron }addamar da fim ]in kwanan nan

Mace SalihaCi gaba daga shafi na 16

a Kano, jagoran rundunar �Yan�uwa na}asa baki ]aya, Malam Ibrahim El-Zakzaky, ya bayyana muhimmancinfim a Musulunci, ya ce idan an yi

amfani da wannan hanya dakyau, to za a taimaka maaddini }warai. Mun ga hakatun a yadda �yan Kudu sukeamfani da fim don isar dasa}wannin coci.

Shin ko �Yan�uwa Musulmiza su iya sauya akalar shirinfim na Hausa? E, to, wannanya danganta kan yawanfinafinan da za su iyashiryowa a lokaci-lokaci, da

ingancinsu, da yayata su har masu kallosu kalle su, da sanya �yan wasa fitattu,da kuma irin sa}wannin da ke cikinsu.

Shirin Mace Saliha furofaganda cewadda ba }iri-}iri ba, in ka ]ebewa�azin da aka bu]e wasan da shi dakuma wurare irinsa. Wannan zai taimakawajen amsuwarsa, domin idan aka zarenau�in nisha]antarwa, aka tsaya kanwa�azi a bayyane ka]ai, sai abin yagunduri jama�a, kamar yadda wasannin�yan Kudu suka gunduri su kansu �yanKudun. A yanzu kam an ]auko hanyasaliha.

Mace Salihafurofaganda cewadda ba }iri-}iri ba, in ka

]ebe wa�azin daaka bu]e wasan

da shi

44