hausar masu {wallon {afa a cikin garin sakkwatodegeljournal.org/papers/degel-2016-12-13.pdf ·...

19
DEGEL JOURNAL OF FACULTY OF ARTS AND ISLAMIC STUDIES, VOl. 12, (June 2016) ISSN: 0794-9316 130 http://www.degeljournal.org UDU SOKOTO Hausar Masu {wallon {afa a Cikin Garin Sakkwato Muhammad M. Umar & Musa Shehu Tsakure Wannan bincike ya shafi karin harshen rukunin masu }wallon }afa a cikin garin Sakkwato. Wato binciken za a gudanar da shi ne don }o}arin gano ainihin yanayin samuwar sauyi a sanadiyar zamantakewa, wanda ya haifar da Hausar masu sha’awar tamola. Domin tabbatar da samuwar wannan Hausar da ta sha bamban da ta wasu rukunan jama’a, za a yi amfani da kalmomi da sassan jimla, wa]anda suka fi armashi da kar~uwa a idon magoya bayan ‘yan wasa ko kulob- kulob. Hanyoyin cim ma wannan }uduri sun ha]a da: Ziyarar kai tsaye a filayen buga }wallon }afa da kuma gidajen kallon }wallo daban-daban da ke a cikin garin Sakkwato, domin ji kai tsaye daga bakin masu amfani da wannan Hausar, da kuma samun damar tattaunawa da su, domin tattara bayanai. Haka kuma, binciken ya gano cewa masu harkar }wallon }afa sun }ware sosai wajen amfani da salon }ir}ira sababbin kalmomi, ta hanyar fa]a]a ma’anar kalmomin Hausa, da kuma Hausantar da kalmomin Ingilishi tare da sarrafa su ta yadda za su dace da tsarin Hausa mai mayar da ]an wani nata. 1.0 Gabatarwa Karin harshen rukuni ya samu ne sanadiyar bambancin aji ko matsayi ko jinsi ko mu}ami ko kuma sana’a da ake samun a cikin zamantakewar al’umma. Kuma }ar}ashin wannan kashi na karin harshe ake samun nau’o’i da dama, musamman abin da ya shafi Hausar rukunin jama’a masu }wallon }afa, mai matsayin wasa wadda }ungiyoyi biyu masu ‘yan wasa goma sha ]aya (11) kowannensu, ke }o}arin buga wani abu da aka yi da tsumma ko roba ko fata domin samun nasarar cin }wallo ko jefa ta a cikin gola. Ana gudanar da wasar tamola ko tawayya a filin buga }wallon }afa, tare da kulawar al}alan wasa bisa wasu sharu]]a da ke yi wa ‘yan }wallon jagoranci. Kowace }ungiya tana da masu horar da ‘yan wasa da kuma magoya bayansu. Da gangan na }i kawo tarihin }wallon }afa. 1 Farfajiyar binciken za ta tsaya ne a kan hanyoyi biyu da aka fi amfani da wannan karin harshe, wato duba yanayin samuwar Hausar masu buga }wallon }afa, yayin da suke wasar motsa jiki a filayen buga wasanni daban-daban, da kuma masu kallon }wallon }afa, yayin da suke kallon wasannin }wallo na cikin gida da na }asashen waje, musamman a gidajen kallon wasanni na ku]i, da kuma dandalin tattaunawarsu inda suke tabka muhawarori. Akwai kuma, dandalin zaman ma’abota wasanni da za a ri}a ziyara, domin jin hirar da suke yi, musamman bayan an dawo daga buga wasa, ko kuma bayan kammala kallon wata wasar kulob-kulob na }asashen }etare. Akasari a wa]annan lokuta ake samun zafafar gardandami, da sharhi ko a dawa a kan yadda wasanni suka 1 Don ta}aitaccen labarin abubuwan da suka wuce a kan }wallon }afa dubi Fage, Usman Usaini. Ire-iren Karin Harshen Hausa na Rukuni. Kano: Benchmark Publishers Limited, 2002, shafi na 134-135.

Upload: others

Post on 16-May-2020

6 views

Category:

Documents


0 download

TRANSCRIPT

Page 1: Hausar Masu {wallon {afa a Cikin Garin Sakkwatodegeljournal.org/Papers/DEGEL-2016-12-13.pdf · sha’awar }wallon }afa a cikin al’umma, haka ake samun ]imbin masu tsananin }iyayya

DEGEL JOURNAL OF FACULTY OF ARTS AND ISLAMIC STUDIES, VOl. 12, (June 2016) ISSN: 0794-9316

130 http://www.degeljournal.org UDU SOKOTO

Hausar Masu {wallon {afa a Cikin Garin Sakkwato

Muhammad M. Umar & Musa Shehu

Tsakure

Wannan bincike ya shafi karin harshen rukunin masu }wallon }afa a cikin garin

Sakkwato. Wato binciken za a gudanar da shi ne don }o}arin gano ainihin

yanayin samuwar sauyi a sanadiyar zamantakewa, wanda ya haifar da Hausar

masu sha’awar tamola. Domin tabbatar da samuwar wannan Hausar da ta sha

bamban da ta wasu rukunan jama’a, za a yi amfani da kalmomi da sassan jimla,

wa]anda suka fi armashi da kar~uwa a idon magoya bayan ‘yan wasa ko kulob-

kulob. Hanyoyin cim ma wannan }uduri sun ha]a da: Ziyarar kai tsaye a filayen

buga }wallon }afa da kuma gidajen kallon }wallo daban-daban da ke a cikin

garin Sakkwato, domin ji kai tsaye daga bakin masu amfani da wannan Hausar,

da kuma samun damar tattaunawa da su, domin tattara bayanai. Haka kuma,

binciken ya gano cewa masu harkar }wallon }afa sun }ware sosai wajen amfani

da salon }ir}ira sababbin kalmomi, ta hanyar fa]a]a ma’anar kalmomin Hausa,

da kuma Hausantar da kalmomin Ingilishi tare da sarrafa su ta yadda za su dace

da tsarin Hausa mai mayar da ]an wani nata.

1.0 Gabatarwa

Karin harshen rukuni ya samu ne sanadiyar bambancin aji ko matsayi ko jinsi ko mu}ami ko kuma

sana’a da ake samun a cikin zamantakewar al’umma. Kuma }ar}ashin wannan kashi na karin

harshe ake samun nau’o’i da dama, musamman abin da ya shafi Hausar rukunin jama’a masu

}wallon }afa, mai matsayin wasa wadda }ungiyoyi biyu masu ‘yan wasa goma sha ]aya (11)

kowannensu, ke }o}arin buga wani abu da aka yi da tsumma ko roba ko fata domin samun nasarar

cin }wallo ko jefa ta a cikin gola. Ana gudanar da wasar tamola ko tawayya a filin buga }wallon

}afa, tare da kulawar al}alan wasa bisa wasu sharu]]a da ke yi wa ‘yan }wallon jagoranci.

Kowace }ungiya tana da masu horar da ‘yan wasa da kuma magoya bayansu. Da gangan na }i

kawo tarihin }wallon }afa.1

Farfajiyar binciken za ta tsaya ne a kan hanyoyi biyu da aka fi amfani da wannan karin harshe,

wato duba yanayin samuwar Hausar masu buga }wallon }afa, yayin da suke wasar motsa jiki a

filayen buga wasanni daban-daban, da kuma masu kallon }wallon }afa, yayin da suke kallon

wasannin }wallo na cikin gida da na }asashen waje, musamman a gidajen kallon wasanni na ku]i,

da kuma dandalin tattaunawarsu inda suke tabka muhawarori. Akwai kuma, dandalin zaman

ma’abota wasanni da za a ri}a ziyara, domin jin hirar da suke yi, musamman bayan an dawo daga

buga wasa, ko kuma bayan kammala kallon wata wasar kulob-kulob na }asashen }etare. Akasari

a wa]annan lokuta ake samun zafafar gardandami, da sharhi ko a dawa a kan yadda wasanni suka

1Don ta}aitaccen labarin abubuwan da suka wuce a kan }wallon }afa dubi Fage, Usman Usaini. Ire-iren Karin Harshen

Hausa na Rukuni. Kano: Benchmark Publishers Limited, 2002, shafi na 134-135.

Page 2: Hausar Masu {wallon {afa a Cikin Garin Sakkwatodegeljournal.org/Papers/DEGEL-2016-12-13.pdf · sha’awar }wallon }afa a cikin al’umma, haka ake samun ]imbin masu tsananin }iyayya

DEGEL JOURNAL OF FACULTY OF ARTS AND ISLAMIC STUDIES, VOl. 12, (June 2016) ISSN: 0794-9316

131 http://www.degeljournal.org UDU SOKOTO

kaya, wanda ta haka ne ake samun samuwar kalmomi da dama da ake dangantakawa da masu

}wallon }afa.

2.0 Matsayin {wallon {afa ga Al’ummar Hausawa

{wallon }afa na ]aya daga cikin manyan wasanni da suka samu kar~uwa a duniya. Wannan dalili

ne ya sa ake samun yara da manya na mayar da hankali wajen bugawa domin motsa jini ko kallonta

ta talabijin domin nisha]i. Tsananin tasirin }wallon }afa ga masu sha’awarta ya haifar musu

matu}ar shagala sosai, da kuma samun wasu Hausawa na amsa sunayen wasu ‘yan }wallo na cikin

gida da ma na }asashen waje a matsayin la}abinsu. Saboda haka, a wannan sashe za mu duba irin

yadda Hausawan garin Sakkwato ke kallon }wallon }afa, ko mu duba irin matsayin da suka bata

a wannan lokaci da muke ciki. Sai dai ya kamata mu san cewa; kamar yadda ake samun masu

sha’awar }wallon }afa a cikin al’umma, haka ake samun ]imbin masu tsananin }iyayya da ita.

{wallon }afa wata babbar hanya ce da mutane ke amfani da ita wajen motsa jikinsu, domin samun

ingantacciyar lafiya da jin garau. A yau al’ummar garin Sakkwato sun ]auki yin }wallon }afa ko

buga ta a matsayin nau’in atisaye. Saboda haka, wannan ne ya sa ake samun nau’o’in mutane masu

buga }wallon }afa domin motsa jini kawai. Misali ana samun rukunin mutane masu }iba, ko

babban ciki na rungumar wasar }wallo don kawai rage jikinsu. Ta wannan wasar sukan

saminasarar zubar da kitsen da ke tattare a jikinsu. Haka kuma, wasu daga cikinsu suna yin wasar

ne domin samun }arfin jiki da kuzari. Domin likitoci sun ba da fatawar cewa; gudanar da wasar

}wallon }afa ko zagayen filin }wallo ko kuma yawaita atisaye ko gudu, sukan taimaki jiki samun

isassar lafiya da taimaka wa jiki }arin inganci.

{wallon }afa a yau ta zama wata hanya da ake neman abincin kai wa ga bakin salati. Saboda

mutane da dama sun ri}i }wallon }afa a matsayin sana’ar zamani, wadda ake iya dogaro da ita

domin biya wa kai bu}atu na yau da kullum. Kamar kowace sana’a ita ma }wallon }afa sai an

saka jari da kuma }wazo da himma wajen koyon dabaru wasar, tun daga mataki na }asa. Wannan

ya sa ake samun ‘yan wasa da dama da ke ]aukar horo na musamman, a makarantun koyon

}wallon }afa da ake samu a wasu }asashe na duniya. A ta}aice, babban abin da ya sa mutane ke

tururuwa cikin harkar wasannin }wallon }afa, shi ne ana samun ku]a]e masu ]imbin yawa ta

wannan hanya. A yau ‘yan }wallon }afa na ]aya daga cikin masu ku]in duniya, kamar dai yadda

hasashe ya nuna.

A yau siyasar duniya ta taimaka ainun wajen bun}asa sana’ar buga }wallo, domin akwai babbar

}ungiyar }wallon }afa ta duniya da aka kafa domin ha]a kan al’ummomin duniya. Aikin wannan

}ungiya shi ne alhakin kula da harkokin wasannin duniya. Wannan ya samar da tsarin gasar

wasannin }wallon }afa, wanda ke farawa tun daga matakin cikin gida, da matakin nahiya har zuwa

ga matakin duniya. Misali kowace }asa tana da ‘yan wasa masu wakiltarta, kuma gwamnatin }asar

ita ke kula da albashin kowane ]an wasa, tare da lafiyarsa. Akwai kuma kulob-kulob da ke sayen

‘yan wasa domin samun nasarar lashe gasar da suke fafatawa. Sayen ‘yan wasa yana da matsayi

tun daga matakin }asa zuwa nahiyoyi daban daban. Kuma kowane kulob shi ke biyan ]an wasa

albashi da alawus-alawus da sauransu.

Page 3: Hausar Masu {wallon {afa a Cikin Garin Sakkwatodegeljournal.org/Papers/DEGEL-2016-12-13.pdf · sha’awar }wallon }afa a cikin al’umma, haka ake samun ]imbin masu tsananin }iyayya

DEGEL JOURNAL OF FACULTY OF ARTS AND ISLAMIC STUDIES, VOl. 12, (June 2016) ISSN: 0794-9316

132 http://www.degeljournal.org UDU SOKOTO

Wasar }wallon }afa na ]aya daga cikin manyan wasanni masu kawo sada zumunci tsakanin

al’umma. Ana amfani da wasar ne wajen ha]a kan }abilu daban-daban na duniya, musamman

saboda bambancin wurin zama, ko harshe, ko addini ko al’ada ko sauran hanyoyin zamantakewar

rayuwa. Misali, a da }asashe suna zaune cikin ya}e-ya}e da rashin zaman lafiya da matsananciyar

gaba. Amma a yau wasar }wallo ta kasance hanyar sulhu da sasantawa tsakanin }abilun duniya.

Saboda haka, muna iya cewa wasar }wallon }afa ta taimaka wajen rage }abilanci ko nuna wariyar

launin fata, musamman saboda shirya wasannin sada zumunci, da kuma gasar cin kofin duniya da

ta nahiyoyi daban-daban. Ga shi kuma hukumomin }wallon }afa sun tanadi hukunci daban-daban

ga duk wanda aka sama da laifin aikata irin wa]annan laifuka.

Idan kuma muka juya a ~angaren filayen buga wasanni za mu ga ‘yan wasar sukan fito daga

}abilu, da addinai, da al’adu daban-daban, kuma abin ban sha’awa wasar kan ~atar da bambance-

bambancen da ke tsakaninsu har ana cewa suna zama abu ]aya. Misali, a kulob-kolob na }asashen

waje da suka ha]a }abilu daga }asashe mabambanta, za ga ka ‘yan wasa na rungumar juna,

musamman bayan zura }wallo a raga, ba tare da nuna }yama ko wariyar launin fata. Su ma gidajen

kallon }wallo maha]a ce ta }abilu masu bambancin addinai daban-daban, amma saboda tarayyar

goyon bayan wani kulob sai ka nemi bambance-bambancen da ke tsakanin ‘yan kallo ka rasa. Ko

babu komi wasar }wallon }afa ta taimaka ainun ta wannan haujin.

Akwai Hausawan da suka ]auki }wallon }afa a matsayin abokiyar hira, domin takan taya al’umma

hira ta hanyar rage lokaci ga masu bugawa ko masu kallon yadda take kayawa a cikin akwatunan

talabijin. Haka kuma, muna iya cewa aba ce da ke ]ebe wa ma’abota wasanni kewa. Sa’annan

}wallon }afa ta zama sahun gaba wajen samar da sha}atawa, musamman lokacin da rayuwa ke

son hutu, bayan share dogon lokaci ana ayyuka barkatai. Wani abin armashi ga wasar }wallo shi

ne ana samunta cikin kasakasan CD, da kuma cikin sigar wasannin gem da ake samu a kwamfuta

da wasu wayoyin salula. A ta}aice, tagulla a wani }auli, ta taimaka wajen taya al’umma hira,

musamman lokutan ka]aici, ko lokutan da babu ayyuka da yawa, kai ko lokutan da ake hutu da

sauransu.

3.0 Matsayin Gidajen Kallon {wallo a Garin Sakkwato

Gidajen kallon }wallo wurare ne da aka ke~e a cikin wani gida, ko shago ko kuma wani katafaren

fili, domin gudanar da sana’ar watsa wasanni da ake biya kafin a kalla. Akasarin }wallayen da ake

kallo a talabijin, }wallaye ne na }asashen waje, musamman }ungiyoyin wasanni da ke Turai, da

sauran }asashen duniya. Masu wannan sana’ar kan tanadi wuri, da wutar lantarki ko janareta, da

manyan akwatunan talabijin, da tauraron ]an’adam ko dish, tare da sayen kati mai kawo dukkanin

wasannin da ake bu}ata.

Babban matsayin wa]annan gidaje na kallon }wallo shi ne sana’ar zamani, wadda musamman

‘yan shekaru baya ake samun ma}udan ku]a]e a cikinta. Dalilin kiran ta sana’ar zamani bai wuce

ganin daga baya ta kunno kai ba, kuma duk abubuwan da ta }umsa na zamani ne. Haka kuma,

wannan sana’ar gidan kallon }wallo ta taimaka wajen bun}asa tattalin arzikin garin Sakkwato,

domin an sami yawaitar mutane cikin wannan sana’ar, sannan ana samun masu }anana sana’a’o’i

suna ca~awa a duk lokacin da ake kallon }wallo. Misali, akwai masu sayar da ruwan sanyi, da

rake, gasasshen nama, da ‘yan tireda, kai duk shagon da ke kusa da irin wa]annan gidaje yakan

sami ciniki, saboda yawan masu kallo. Kuma ana iya cewa wannan sana’ar ta rage zaman kashe

Page 4: Hausar Masu {wallon {afa a Cikin Garin Sakkwatodegeljournal.org/Papers/DEGEL-2016-12-13.pdf · sha’awar }wallon }afa a cikin al’umma, haka ake samun ]imbin masu tsananin }iyayya

DEGEL JOURNAL OF FACULTY OF ARTS AND ISLAMIC STUDIES, VOl. 12, (June 2016) ISSN: 0794-9316

133 http://www.degeljournal.org UDU SOKOTO

wando, tare da samar da aikin dogaro da kai, musamman ga masu tsaro ko kar~ar ku]i a gidajen

kallon wasanni.

Akwai ~angaren jama’ar Sakkwato masu kallon }wallo saboda tana samar da nisha]i da

annashuwa. Wato, akwai farin ciki tattare da ita, musamman idan wani abu ya faru na ban dariya,

ko na burgewa, ko na al’ajabi ko kuma idan }ungiyar da mutum ke goyon baya ta ci }wallo, ko ta

yi nasara. Misali idan ana kallon }wallo a cikin unguwa, da zarar an ci wasa za ka ji kuwace-

kuwace, da sowa da dare-dare masu nuna murna da jin da]i. A ta}aice, ma’abota kallon }wallo

na ha]uwa da raha da kwanciyar hankali, ko samun wadatar zucci a wasu lokuta.

4.0 Abubuwan da ke Haifar da Hausar Masu {wallon {afa

Ha]uwar al’umma wuri ]aya, na cikin muhimman abubuwan da suka haifar da Hausar masu

}wallon }afa, musamman saboda bambancin }abila ko addini. Wannan ya sa dole uwar na }i, ake

samun karin harshen buroka a tsakanin masu buga }wallo ko masu kallonta a akwatunan talabijin.

Saboda haka, ba abin mamaki ba ne a sami }ir}irar sabbin kalmomi, wa]anda sai wanda ke cikin

rukunin ma’abota wasar }wallon }afa, ke iya fahimtar abin da ake nufi.

Adawa na nufin kushewa ko jin zafin wani da wani samu. Adawa na faruwa a wasar }wallon }afa

yayin da aka ce }ungiyoyi biyu sun ha]u, saboda wasar sada zumunci, a yayin wata takara ko

gasar lashe wani kofi ko kyauta. A irin wannan yanayi kowane sashe yana tsananin adawa da

]an’uwansu, domin kowa ya fi da son ya sami galaba. Su ma masu kallo ko goyon bayan

}ungiyoyin suna tsananin adawa da junansu, domin kowa ya fi son }ungiyar da yake so ta yi

nasara. A fagen masu }wallon }afa adawa na iya ]aukar zuwa kallon }wallon abokanin hamayya,

da fatar ganin yadda za a lalla sa su. A ta}aice, wani lokaci akan dace a ci abokanin adawa, a yayin

wata rana akan sami akasin haka, kuma wannan adawa ta taimaka wajen samar da Hausar masu

}wallon }afa.

A ~angaren masu kallon wasanni, an fi samun adawa tsakanin magoya bayan babban kulob,

musamman mai ri}e da kambu, ko kuma a tsakanin manyan }wararrun kulob-kulob, wa]anda

kowane daga cikinsu zakara ne, kuma yakan yi adawar ganin abokin hamayyar sa ya yi nasara

komi zamanta }arama. A ko’ina ana samun wannan adawa, sai dai tafi }arfi a wasannin Turai,

inda ake samun ma’abota goyon bayansu a garin Sakkwato. Tsananin adawa yayin kallo }wallo

na haifar da sabbin kalmomi da ake dangantawa da masu }wallon }afa. Misali a }asar Ispaniya

ana samun adawa tsakanin Real Madrid da Barcelona, a Ingila akwai adawa tsakani Manchester United da Arsenal, ko tsakanin Manchester United da Manchester City, sai a }asar Italiya inda ake

samu adawa tsakanin A.C Milan da Inter Milan da sauran.

Tsokana na nufin jawo magana, ko yin wani abu da zai jawo hankalin wani, da zimmar ~ata masa

rai ko don tsokanarsa wasa. Sai dai, tsokana a nan tafi shafuwar yinta don nuna adawa. Masu kallon

}wallon na amfani da wasu kalmomi don ci wa ‘yan adawa rai, ko don kawai a ~ata musu rai,

musamman idan ba su ke ci ba. Saboda haka, ta wannan hanya ce ake samun }ir}ira kalmomi,

wa]anda suke samuwa sanadiyar wannan tsokana da ake yi tsakanin masu kallon }wallon }afa.

Yadda tsokana ke kasancewa a gidajen kallon }wallo kan faru ne, lokacin da ake lallasa wani

kulob, ko kuma kulob yana wasa amma cin }wallo bai samu ba. A irin wannan lokaci ne tsokana

Page 5: Hausar Masu {wallon {afa a Cikin Garin Sakkwatodegeljournal.org/Papers/DEGEL-2016-12-13.pdf · sha’awar }wallon }afa a cikin al’umma, haka ake samun ]imbin masu tsananin }iyayya

DEGEL JOURNAL OF FACULTY OF ARTS AND ISLAMIC STUDIES, VOl. 12, (June 2016) ISSN: 0794-9316

134 http://www.degeljournal.org UDU SOKOTO

ke kutsowa. Misali idan ana cikin wasa, sai aka ga wani daga cikin gwarzayen ‘yan wasa ya rage

motsi ko taka leda, sai ka ji abokan adawa na cewa ruwa na malala, ko su yi ta fa]in a shigo da

wane, ko da yana cikin wasar. Idan kuma ana son a ba da tsoro ko tsokana ga abokan adawa, to

duk lokacin kyamara da nuno layin ‘yan wasan da ba a saba, wato masu jiran canji ko ta kwana,

sai ka ji ana cewa; benci na haya}i, ko kuma idan wani ]an wasa ya ji rauni, ko wanda ya yi likya-

likya har ya nemi a yi canjinsa. A irin wannan lokaci za ka ji abokan adawa na cewa “sai ya ishe

ta”. A ta}aice, haka wa]annan kalmomi ko jimloli ke samuwa har su sami gindin zama a tsakanin

rukunin jama’a ma’abota wasannin }wallon }afa.

Idan muka lura da kyau za mu ga dalilan adawa da tsokana suna cikin muhimman abubuwan da

suka samar da Hausar masu }wallon }afa. Sai dai, sun bar baya da }ura, musamman a shekarun

baya da aka fi samun fa]ace-fa]ace da tashin hankali, wa]anda ke haifar da samun raunuka da

jikkitar wasu, kai wani lokaci har hasarar rayuka ake samu. Saboda kawai an ci }ungiyar da wasu

ke goyon baya, musamman idan an nuna musu adawa ko tsananiin tsokana, ko ri}a yi musu sowa

ko dariya a kan rashin nasarar da suka yi. Wannan dalili ya sa a farko-farkon buga }wallon }afa

da kallonta ake gayyatar jami’an tsaro, domin rage fa]a tsakanin masu }wallon }afa, amma da

tafiya ta yi tafiya an sami wayewar kai da fahimtar juna, inda a yau an rage samun tashin-tashina

a gidaje kallon }wallo da filayen da ake buga wasanni.

Nisha]i wani abu da ke faruwa cikin zukatan al’umma, ta hanyar nisha]i mutum ke iya bayyanar

da abin da ke cikin zuciyarsa, musamman na farinciki, tare da yin fara’a. Saboda haka, dangantakar

nisha]i da wasar }wallon }afa wata ala}a ce da ke bayyana ~aro-~aro lokacin aka sami abubuwan

burgewa ko na taka leda kamar haka; yin yanka gwanin ban sha’awa, tare da yin wani sitayil, ko

zura }wallo ta amfani da salon da zai }ayatar, ko yin fasin ko ri}a raba }wallo yadda ya kamata.

Duk wa]annan suna sa a sami nisha]i da jin da]i, musamman masu kallo kan tashi tsaye suna

kuwa, suna murna, kai wani lokaci har da zage-zage don nuna jaruntaka da dai sauransu. Su ma

‘yan kallo kan ba junansu dariya saboda faruwar wani abu cikin wasar da ake kallo. A ta}aice,

}wallon }afa tana samar da nishatantarwa a cikin al’umma a garin Sakkwato, musamman a

tsakanin masu sha’awar wasanni.

6.0 Matsayin Hausar Masu {wallon {afa ga Daidaitacciyar Hausa

Hausar masu }wallon }afa karin harshen Hausa na rukuni ne, kuma karin harshen Hausa na rukuni

mataki ne na biyu cikin rabe-raben karin harshen Hausa. Dalilin mu a nan shi ne, Hausar masu

}wallon }afa yanayi ne na samar da sababbin kalmomi da sarrafa harshe wanda ya bambanta da

yadda wasu rukunoni na al’umma ke amfani da harshen Hausa, sai dai kamar kullum ana samun

fahimta tsakaninsu.

Matsayin Hausar masu }wallon }afa a cikin harshen Hausa, shi ne karin harshe ne da wasu

ke~a~~un rukunin jama’a ke amfani da shi a cikin al’ummar Hausawa. Wannan karin harshe ne

da ya samu sanadiyar zamani, kuma tuni ya sami gindin zama a cikin harshen Hausa, saboda

kasancewar wasu rukunin jama’a na ri}a jefa ire-iren kalmomi ko jimlolin }wallon }afa,

musamman yayin da ake magana ko zantawa. Har ila yau, wannan karin harshe ya ba da

gudummuwa wajen bun}asa harshen Hausa, wato dai Hausar masu }wallon }afa ta taimaka wajen

ha~aka Hausa, musamman saboda sauye-sauyen da ta haddasa a cikin Hausa. A ta}aice, muna iya

Page 6: Hausar Masu {wallon {afa a Cikin Garin Sakkwatodegeljournal.org/Papers/DEGEL-2016-12-13.pdf · sha’awar }wallon }afa a cikin al’umma, haka ake samun ]imbin masu tsananin }iyayya

DEGEL JOURNAL OF FACULTY OF ARTS AND ISLAMIC STUDIES, VOl. 12, (June 2016) ISSN: 0794-9316

135 http://www.degeljournal.org UDU SOKOTO

cewa harshen Hausa ya amfana ta Hausar masu }wallon }afa, ta fuskar }ari da aka samu na nau’in

Hausar rukuni, da ha~akar kalmomi da jimlolin Hausa da dama

Kamar yadda harshe ke ya]uwa, haka shi ma wannan karin harshe na Hausar masu }wallon }afa

ke ya]uwa. Saboda haka, Hausar kan fara ne daga mutum ]aya zuwa biyu ko fiye, a musamman

filayen da ake buga }wallo ko gidajen kallon }wallo da ke birjik a cikin garin Sakkwato. Ya]uwa

a nan kan kasance ta daga mutum zuwa mutum ko daga rukunin jama’a zuwa wani rukuni. A mafi

yawan lokuta, an fi ]aukar Hausar tare da ya]a ta a wuraren buga }wallo, ko wuraren da ake

hidimar kallonta har zuwa maha]ar matasa ko majalisarsu.

Kamar yadda aka al’adanta, matasa kan zauna a majalisu inda suke hirar }wallon }afa, musamman

a lokutan kakannin wasannin duniya. Ta haka irin wa]annan kalmomi da jimloli ke game ko’ina

gwargwadon hali, musamman a muhallan bincikenmu. Tamkar karin harshen Sakkwatanci Hausar

masu }wallon }afa ta game sa}o da lungu cikin garin Sakkwato.

7.0 Hausar Masu {wallon {afa a Cikin Garin Sakkwato

Hausar masu }wallon }afa Hausa ce da ake samu a tsakanin matasa a filayen buga }wallon }afa,

wato wuri ne da ake kira filin wasa, inda ake buga }wallo a matsayin motsa jiki. Yayin gudanar

da wannan wasa ake samun yawan amfani da salon magana, wanda ya ji~inci yanayin wasar

}wallon }afa. Misali ri}a ambatar sunayen da suka shafi }wallo, da fili, da ‘yan wasa da sauran

yanaye-yanayen yadda ake gudanar da wasar. A ~angaren gidajen kallon }wallo kuwa, ana iya

cewa wuri ne da aka shirya domin kallon }wallo, wadda ake bugawa kai tsaye, ko wadda aka riga

aka kammala. A nan ma, lokacin kallon }wallo ake samu ma’abota kallo na jefa kalmomi ko

jimloli, wa]anda ke dacewa da yanayin yadda ‘yan wasa ke taka leda a cikin talabijin, ko sharhi

irin na ]an kallo ko bayan fage.

Wannan Hausar masu }wallon }afa da ake amfani da ita a cikin garin Sakkwato ana iya cewa ta

ha]a da: Hausar masu }wallon }afa wadda ake yi tare da fahimtarta a cikin gari na yankin

Sakkwato. Wato duk wanda ya fito daga wani yanki ba zai fahimci akasarin wainar da ake toyawa

ba. Akwai kuma, Hausar gama-gari wadda ake samu a ko’ina a cikin Hausawa. Saboda mafi yawan

wa]annan kalmomin }wallon }afa na gama-gari an kar~e su ne daga harshen Ingilishi, don a yi

amfani da su kai tsaye a cikin harshen Hausa. Sannan ana samun }ago ko gano hanyar sarrafa

harshe ko samar da Hausar da za ta dace da rukunin masu sha’awar }wallon }afa. Sai dai ana

samun tarayya ta fuskar wannan }ir}ira, inda ake samun amfani da wannan Hausar tsakanin masu

}wallon }afa da ke zaune a wurare mabambanta a cikin }asar Hausa.

7.1 Hausar Masu Buga {wallon {afa

Hausar masu buga }wallon }afa Hausa ce wadda masu buga }wallon }afa kan yi amfani da

wannan karin harshe, yayin da suke hidimar buga }wallo a filayen wasanni daban-daban. Ko kafin

fara wasa, lokacin da ake shirye-shiryen farawa za ka iske matasan na hasashen yadda za su motsa

jikinsu, ko bayan an kammala ta, inda ake samun sharhi na yadda wasar ta gudana, da kuma shirya

wa wasa ta gaba lokutan tirenin. Wani lokaci ma idan ana zaune a majalisa akan ri}a hirar yadda

Page 7: Hausar Masu {wallon {afa a Cikin Garin Sakkwatodegeljournal.org/Papers/DEGEL-2016-12-13.pdf · sha’awar }wallon }afa a cikin al’umma, haka ake samun ]imbin masu tsananin }iyayya

DEGEL JOURNAL OF FACULTY OF ARTS AND ISLAMIC STUDIES, VOl. 12, (June 2016) ISSN: 0794-9316

136 http://www.degeljournal.org UDU SOKOTO

wasar yau ko ta wani lokaci ta kaya, tare da fashin ba}in matsaloli da nasarorin da aka samu, da

}o}arin fito da hanyoyin gyara ko na ci gaba da farar anniyya.

Abin ban sha’awa da wannan Hausar masu buga }wallon }afa shi ne, suna amfani da ita a cikin

harkokinsu na al’amurran rayuwa, sai dai ba kowa zai fahimci ma’anar ire-iren wa]annan

kalmomi ba, sai wanda ke cikin rukunin masu abu. Sai dai ya kamata a san cewa, ana samun

jama’a masu sha’awar zuwa kallon masu buga }wallon }afa a filayen wasa, domin ]ebe wa ido

}eya.

7.2 Hausar Masu Kallon {wallon {afa

Wannan sashe ya }umshi tsokaci ne kan Hausar masu kallon }wallon }afa, yadda take samuwa da

yadda ake sarrafa ta a gidajen kallon }afa, ko majalisun samari daban-daban da ke cikin garin

Sakkwato. Wannan karin harshe yana samuwa ne kafin a fara kallon wasa, inda kowane mai goyon

baya zai tofa albarkacin bakinsa a kan yadda wasar za ta kasance. Sai dai, idan an fara kallon

wasar, lokaci ne da ake samun tsananin adawa, nuna goyon baya, da ri}a jefa kalaman tsokana ko

na wasa kai, musamman idan ana kan nasara. Sai babban lokacin gardandami bayan an gama

kallon wasar, wanda ke haifar da hirar }wallo a duk inda aka ga gungun matasa. Irin wannan lokaci

ne magoya bayan }ungiyoyin da suka fafata ke bayyana ra’ayoyinsu a kan rashin adalcin da aka

yi wa wani ~angare, ko nuna jin da]i ko rashin jin da]in yadda }wallon ta kaya.

Ita ma wannan Hausar masu kallon }wallon }afa kamar takwararta da ake yi a filin buga }wallo,

ana samun ma’abota kallon wasar }wallon }afa na tsarma ta a cikin maganganunsu na yau da

kullum, musamman idan sun ha]u da junansu. Sai dai shi ko duk wanda bai tu’ammuli da harkar

kallon }wallon }afa ba zai fahimci wainar da ake toyawa ba, balantana ma har ya kama tasha. A

ta}aice, ga muhimman kalaman Hausar masu kallon }wallon }afa, kamar yadda aka kalato a

bakunan ma’abota kallon wasanni, da wa]anda aka ci karo da su a gidajen kallon }wallo a cikin

garin Sakkwato.

Jadawali Mai Nuna Hausar Masu {wallon {afa a Cikin Garin Sakkwato

Lamba Hausar Masu {wallon

{afa

Ma’anarta

1 Wacce ku ci mu Ramuwar zura }wallo ta nan take, bayan an fara zura

wa gefen da ya rama }wallo

2 {yare ko wasi}a ko sa}o Ingantaccen kurosin, ko bugun sama da zai kai ga

wanda ake so ya kar~a

3 Katanga Jeruwar ‘yan wasa, a matsayin kariya ga gola ko mai

tsaron gida, idan za a buga firikik

Page 8: Hausar Masu {wallon {afa a Cikin Garin Sakkwatodegeljournal.org/Papers/DEGEL-2016-12-13.pdf · sha’awar }wallon }afa a cikin al’umma, haka ake samun ]imbin masu tsananin }iyayya

DEGEL JOURNAL OF FACULTY OF ARTS AND ISLAMIC STUDIES, VOl. 12, (June 2016) ISSN: 0794-9316

137 http://www.degeljournal.org UDU SOKOTO

4 Mai kan jaki/ tururuwa Ruud van Nistelrooy lokacin da yana buga wa

}ungiyar Manchester United

5 Ya sa kai ]an wasa ya ja }wallo da gudu

6 Akwai }ura Nuni ne a kan fafatawar manyan }ungiyoyin }wallo

7 Osi Zura wa ]an wasa }wallo ta }ar}ashin }afafunsa

8 Suka Buga }wallo da cikin faruttan }afa

9 Kora Kai wa abokan karawa hari na ba zata

10 Kwante Ragowar }wallo da aka jinkirta bugawa

11 Yau akwai zama Akwai kallon }wallo ke nan

12 Záárìyáá2 Sunan da ake yi wa Gerrad Pique ]an wasar Barcelona

13 Kullu yaumin hasara Sunan da aka ri}a yi wa Real Madrid tlokacin da suka

rage kuzari

14 Ga ci ga yanka {ungiyar }wallon }afa ta Barcelona da ke }asar

Ispaniya

15 Kanikawa {ungiyar wasar }wallon }afa ta Chelsea da ke }asar

Ingila

16 Cehwane Sayen sabbin ‘yan wasa

17 Agogo [an wasa ya zagaya da }wallo

18 Ya yi mai taggo da

wando

Obahed, ko jallabiyya ko a yanke mutum ta sama, ta

hanyar buga }wallo ta tsallake kansa

19 [an na farce Messi ]an wasan Barcelona

20 Jahili ne [an wasan da bai iya ba

21 Kare shi, ko tashi da shi Mai tsaron gida ya hana wucewa

22 Ya buga mai su Wasa da }afafu, ko yin wala-wala da su, bayan ]an

wasa na ri}e da }wallo a tsakiyar }afafunsa, don

2Siriri ko sar}a}}en yanki dogo da ake zurawa a kubakar wando don ]aurawa a gindi. Masu }wallon }afa sun fa]a]a

ma’anarta saboda ganin yadda ake wuce Gerrad Pique da }wallo tamkar yadda ake zura zariya a kubakar wando.

Page 9: Hausar Masu {wallon {afa a Cikin Garin Sakkwatodegeljournal.org/Papers/DEGEL-2016-12-13.pdf · sha’awar }wallon }afa a cikin al’umma, haka ake samun ]imbin masu tsananin }iyayya

DEGEL JOURNAL OF FACULTY OF ARTS AND ISLAMIC STUDIES, VOl. 12, (June 2016) ISSN: 0794-9316

138 http://www.degeljournal.org UDU SOKOTO

kawai ya samu yanke wani, ko wucewa da }wallo ba

tare da wata tangar]a ba

23 Ja shara [an wasa ya ja }wallo daga tsakiya yana yankan

abokan takara

24 Sun ba da }waya Sun ba ri an cinye su, ta hanyar kar~ar maki uku daga

gare su.

25 Ku bi]i }wa]]o ‘Yan wasa su nemi cin gwal

26 Ku bi]i tsaro A yi difendin gem, a buga }wallo tare da tsare gida,

kuma ba a damu a je a zura }wallo ba

27 Ruhe Lokacin da wani [an wasa ya yi shot, ko ya buga

}wallo da }arfi don neman gwal

28 Ana tare Masu kallon }wallo su yi tarayyar kulob wajen goyon

baya, ko a sami ha]in guiwar goyon baya tsakanin

}ungiyoyi biyu mabambanta. Misali, Barcelona da ke

Ispaniya suna abota da Manchester United da ke

Ingila. Su kuma Real Madrid na Ispaniya suna abota

da ‘yan Arsenal da ke Ingila

29 Dodon raga Ronaldo na Brazil

30 Gyado Ronaldo ko Ronaldinho ‘yan wasar }asar Brazil, ana

yi musu wannan suna ne saboda fitowar ha}oransu na

sama

31 A ci gaba da gashi3 A ci gaba da matsa lamba, ko lallasa abokan fafatawa

32 Kahirrai masu kurus {ungiyar Barcelona, wanda bajensu ked a ratsin

kurus

33 Ba a tare Idan [an wasa ya zura }wallo a raga, sai ya yi alamar

kurus don nuna jin da]insa, a nan masu goyon

bayansu kan ce ba a tare.

34 [an sarauniyar Ingila Wayne Rooney ko [an wasan }ungiyar Manchester United

35 Golan duniya Iker Casillas golan }ungiyarReal Madrid.

3Nama sai ran sallah na matsayin cikin zancen a fa]ar Hausawa.

Page 10: Hausar Masu {wallon {afa a Cikin Garin Sakkwatodegeljournal.org/Papers/DEGEL-2016-12-13.pdf · sha’awar }wallon }afa a cikin al’umma, haka ake samun ]imbin masu tsananin }iyayya

DEGEL JOURNAL OF FACULTY OF ARTS AND ISLAMIC STUDIES, VOl. 12, (June 2016) ISSN: 0794-9316

139 http://www.degeljournal.org UDU SOKOTO

36 A ruhe }ohwa Idan an ci wani kulob, kuma magoyon bayansa suna

fita kafin a gama, ko a bushe.

37 Sai ya ishe ta [an wasa ya nemi a sauya shi, saboda gajiya ko

samun rauni.

38 Za a coke baya Za a ]inke ~ara ko gi~in da kulob ke fuskanta a wani

~angare yayin da ake buga wasa.

39 Ya tunhwaye ta, ya ishe

ta

Cin }wallo bayan gola ya yi amai.

40 Ta ]anyace Ramuwar cin }wallo da za ta sauya galaban wani

~angare zuwa matakin daidai kafin a tashi daga wasa.

41 Ya yi odiye ko ya ci gida

‘Yeskwaba

[an wasa ya zura }wallo ragarsu bias kuskure

42 Kawo Tsakiyar filin wasa, inda ake ]ora }wallo idan za a

fara wasa ko idan an ci }wallo

43 Yaji Sunan da ake yi wa Pepe ]an wasar Real Madrid

44 |arawon gola A bar ]an wasa shi ka]ai cikin gidan da ba nasu ba,

sannan a bashi }wallo

45 Ku ja layi A tsare gida a hana kowa wucewa zura }wallo

46 Ya ri}e shi Wani ]an wasa ya hana abokin karawarsu sha}at ko

samun walwala a cikin wasa

47 Ga Mesin nan bayanku,

ko ga Ronaldo nan

bayanku.

Ma’abota kallon }wallo kan tsokani junansu,

musamman kafin buga }wallon adawa tsakanin Real Madrid da Barcelona

48 Gidauniya Cin gwal mai yawan adadin ga~o~in sunan wani

kulob

Jadawali Mai Nuna Hausar Masu {wallon {afa ta Gama-Gari

Lamba Hausar Masu {wallon

{afa

Ma’anarta

1. Turoyin Jifar }wallo da hannu

Page 11: Hausar Masu {wallon {afa a Cikin Garin Sakkwatodegeljournal.org/Papers/DEGEL-2016-12-13.pdf · sha’awar }wallon }afa a cikin al’umma, haka ake samun ]imbin masu tsananin }iyayya

DEGEL JOURNAL OF FACULTY OF ARTS AND ISLAMIC STUDIES, VOl. 12, (June 2016) ISSN: 0794-9316

140 http://www.degeljournal.org UDU SOKOTO

2. Kwánàà4 Bugun gefe

3. Fyanariti Bugun daga kai sai mai tsaron gida ko gola.

4. Gola Mai tsaron gida, ko raga, ko inda ake cin }wallo

5. Kohi Kofi ko kyautar da ake ba }ungiyar da ta yi nasarar

lashe wata gasa

6. Gwal Zura }wallo cikin raga

7. Fawul Laifi ko sa~a }a’idar a wasar }wallon }afa

8. Ofsayid Shiga gidan abokan karawa ba bisa tsari ba. Wato

]an wasa ya kasance ba tare da kowa ba, ko ya wuce

wanda suke tare sannan a bashi }wallo, satar fage

9. Firikik Bugun kyauta da ake ba wa]anda aka yi wa sharri

ko }eta

10. Yalokad Katin jan kunne ko na kashedi da ake ba wanda ya

yi laifi a cikin wasa

11. Difendin gem Buga }wallo tare da tsare gida, kuma ba a damu a je

a zura }wallo ba

12. Akuro Cirawa sama a buga }wallo ta baya, wanda zai sa

mutum ya fa]i rairan

13. Hedin ko sa kai Nusar }wallon sama da gaban goshi, ko bugu-da-kai

14. Obahed Jallabiyya ko a yanke mutum ta sama, ta hanyar

buga }wallo ta tsallake kansa

15. Kurosin Buga }wallo sama a gidan abokan karawa, da

zimmar ta kai ga ]an wasan gefenku

16. Lasiman/lasman Mataimakin al}alin wasa, mai ]aga tuta idan wani

abu ya faru a cikin fili

17. Ya yi firi [an wasa ri}e da }wallo daga shi sai gola ko mai

tsaron gida

18. Ya kashe gwal Ya kasa zura }wallo cikin raga

4Lan}wasa ko karkacewa da ke gefen gola a filin buga }wallon }afa.

Page 12: Hausar Masu {wallon {afa a Cikin Garin Sakkwatodegeljournal.org/Papers/DEGEL-2016-12-13.pdf · sha’awar }wallon }afa a cikin al’umma, haka ake samun ]imbin masu tsananin }iyayya

DEGEL JOURNAL OF FACULTY OF ARTS AND ISLAMIC STUDIES, VOl. 12, (June 2016) ISSN: 0794-9316

141 http://www.degeljournal.org UDU SOKOTO

19. Tirenin Horar da ‘yan wasa, ko koyon }wallo, ta hanyar

motsa jiki

20. Kwata-fainal Wasar kusa da wadda ke kusa da }arshe

21. Sami-fainal Wasar kusa da }arshe

22. Fainal Wasar }arshe

23. Koc Mai horar da ‘yan wasa

24. Kaftin Shugaban ‘yan wasa

25. Difenda [an wasan baya

26. Sitiraika Mai kai hari

27. Tim {ungiyar ‘yan wasa

28. Jassi/Jesi Rigar ‘yan wasa

29. Fasin Le

30. Fasin-fasin Yin yawo da hankalin ]an wasa ta hanyar hana shi

kar~ar }wallo

31. Rezin Ri}a buga }wallo sama da saman }afa ko }afa biyu

bayan ana tsaye wuri ]aya. Ko hikimar sarrafa

}wallo

32. Ongwal [an wasa ya zura }wallo gidansu da kuskure

33. Duro Kunnen doki ko canjarar, wato ba wanda ya cinye

wani, ko a ce kowa ya samu maki ]aya maimakon

maki uku da ake ba kulob guda da ya yi galaba a kan

]an’uwansa

34. Tiri Point Maki uku

35. Basa {ungiyarBarcelona da ke Ispaniya.

36. Riyal {ungiyarReal Madrid da ke Ispaniya.

37. Manyu {ungiyarManchester United da ke Ingila.

Page 13: Hausar Masu {wallon {afa a Cikin Garin Sakkwatodegeljournal.org/Papers/DEGEL-2016-12-13.pdf · sha’awar }wallon }afa a cikin al’umma, haka ake samun ]imbin masu tsananin }iyayya

DEGEL JOURNAL OF FACULTY OF ARTS AND ISLAMIC STUDIES, VOl. 12, (June 2016) ISSN: 0794-9316

142 http://www.degeljournal.org UDU SOKOTO

38. Fagi Mai horar da }ungiyarManchester United da ke

}asar Ingila.

39. Tebur Jerin sunayen }ungiyoyin }wallo da sakamakon

gasa mai nuna kulob ]in da ke kan gaba da maki.

40. Lokal camfiyon {ungiyar da ba ta ]aukar kofi.

41. Wolbes [an }wallon duniya mai ri}e da lamban girma ta

shekara

42. Laliga Gasar cin kofi tsakanin manyan }ungiyoyin }asar

Ispaniya

43. Firimiya Gasar cin kofi tsakanin manyan }ungiyoyin }asar

Ingila

44. Siri’a Gasar cin kofi tsakanin manyan }ungiyoyin }asar

Italiya

45. Ralageshon, sun

tsunduma

Rage darajar kulob daga babban mataki na gasa

zuwa }aramin mataki, don ya kasa samun wani kaso

na maki da ake bu}ata

46. Camfiyon lig Gasar cin kofin zakarun Turai

47. ‘Yan ralageshon, ko

sabbin yara

[aukaka darajar kulob daga }aramin mataki na gasa

zuwa babban mataki, bayan kulob ya samun wani

kaso na maki da ake bu}ata

48. Fifa Ta}aitaccen sunan }ungiyar }wallon }afa ta duniya

49. General Gatuso Sunan da ake yi wa tsohon ]an wasar A.C Milan Gennaro Ivan Gattuso

50. Timba ko ya sha timba5 Buga }wallo ta daki gimshi}an da ke ri}e da ragar

gola, ba tare da ta shiga raga ba.

51. Hawa tebur, mun hau

tebur

{ungiyar da ta wuce kowa da yawan maki, ko hawa

matsayi na farko da yawan maki

5 Ana yi wa shan timba kirari da cewa; mai tayar da hankalin gola.

Page 14: Hausar Masu {wallon {afa a Cikin Garin Sakkwatodegeljournal.org/Papers/DEGEL-2016-12-13.pdf · sha’awar }wallon }afa a cikin al’umma, haka ake samun ]imbin masu tsananin }iyayya

DEGEL JOURNAL OF FACULTY OF ARTS AND ISLAMIC STUDIES, VOl. 12, (June 2016) ISSN: 0794-9316

143 http://www.degeljournal.org UDU SOKOTO

52. Kowa na nan, babu injuri Dukkanin ‘yan wasa suna cikinn }oshin lafiya, babu

wanda ya ji rauni.

53. Ya hange gola Cin }wallo ta sama

54. An kai shi injuri [an wasa ya yi raunin da zai hana shi buga }wallo

na wani lokaci

Jadawali Mai Nuna Hausar Masu {wallon {afa ta Ha[in Gambiza (ta cikin garin sakkwato da

ta gama-gari)

Lamba Hausar Masu {wallon

{afa

Ma’anarta

1 Homa Ragar gola ko cin gwal

2 ‘Yan madara, ko

madara, ko ‘yan

babban gida

{ungiyar wasar Real Madrid da ke }asar

Ispaniya

3 Samba Iya raba }wallo daki-daki, tare da yanka

4 {ungiyar tsofaffi/

sanet

{ungiyar wasar }wallon }afa ta A.C Milan da

ke }asar Italiya

5 Kohi haram {ungiyar wasar }wallon }afa ta Arsenal da ke

}asar Ingila

6 Sun ba da gari Lokacin da wata }ungiyar wasa suka kasa

kamo abokan adawarsu bayan sun ba su ratar

maki

7 An wanke mai kashi,

ko an yi mai tsalki

Yi wa ]an wasa osi, ko zura wa ]an wasa

}wallo ta }ar}ashin }afafunsa

8 Ya je sayen kayan

miya

An yanke shi

9 Ya kashe mu, ko ya

kashe gwal

Ya kasa cin }wallo, bayan ya sami damar zura

ta a raga

Page 15: Hausar Masu {wallon {afa a Cikin Garin Sakkwatodegeljournal.org/Papers/DEGEL-2016-12-13.pdf · sha’awar }wallon }afa a cikin al’umma, haka ake samun ]imbin masu tsananin }iyayya

DEGEL JOURNAL OF FACULTY OF ARTS AND ISLAMIC STUDIES, VOl. 12, (June 2016) ISSN: 0794-9316

144 http://www.degeljournal.org UDU SOKOTO

10 An yi muna PDP An yi rashin adalci ko an nuna son kai

11 Sun ji matsi Gana wa wata }ungiyar }wallo azaba, ta

hanyar yanka, da kai matsanantan hari, da shan

timba

12 Ya hauta [an wasa ya taki }wallo ya juya da ita

13 Kare shi, ko tashi da

shi

Mai tsaron gida ya hana wucewa

14 Ya auna shi, ko ya

gwada shi

[an wasa ya kwarari gola ya fito, sai ya nemi

cin }wallo daga nesa

15 Gida, ko gida muke Filin wasar }ungiyar da ake goyon baya ake

buga wasar

16 Waje muke, ko

gidansu

{ungiyar da ake goyon baya ta ziyarci filin

abokan karawarta

17 Gida da daji, ko gida

da waje, ko mun yi

musu gida da daji

An cinye abokan karawa gidansu, da gidan

}ungiyar da ta lallasa su

18 Bai da kai [an wasan da ba ya sa kai ya doki }wallon

sama

19 Ku zo mu tafi [an wasa ya ja }wallo ya zura da gudu a bi shi

20 Ya }are [an wasa ya gaji, ko kuzarinsa ya rage.

21 A sawo Messi, ko

Ronaldo

Tsokanar abokan takara lokacin wani [an

wasa yana ciki, amma bai aikin da ya saba yi

ba

22 Igwai, ko sarki Henry lokacin da yana bugawa }ungiyar

Arsenal

23 Zuzu ko sarki Zidane lokacin da yana bugawa }ungiyar Real

Madrid

24 {wallo ba ta sonmu A cinye }ungiyar da ]an kallo ke goyon baya.

25 ‘Yan wasanmu ba su

nan

Wasu sun sami raunin da zai hana su buga

}wallo.

Page 16: Hausar Masu {wallon {afa a Cikin Garin Sakkwatodegeljournal.org/Papers/DEGEL-2016-12-13.pdf · sha’awar }wallon }afa a cikin al’umma, haka ake samun ]imbin masu tsananin }iyayya

DEGEL JOURNAL OF FACULTY OF ARTS AND ISLAMIC STUDIES, VOl. 12, (June 2016) ISSN: 0794-9316

145 http://www.degeljournal.org UDU SOKOTO

26 Ya yi caca Buga }wallo daga nesa, don gwada sa’a, ko

kutsawa cikin abokan fafatawa masu yawa,

don }o}arin wucewa da }wallo.

27 Ya sa shi talla A yi wa ]an wasa yankan wala}anci har ‘yan

jarida su ri}a nuna shi yayin share fage ko filin

tallace-tallace

28 Ya aika shi/bodi Ru]in ]an wasa, musamman idan ana ri}e da

}wallo za a yi kamar a yi dama da ya tafi, sai a

yi gefen hagu.

29 Zan neme ka Alwashin samun nasara daga magoya bayan

kulob-kulob a wata wasa da za a fafata.

30 Bushi Amfani da al}alin wasa ke yi da mabusa wajen

ba da umurni a cikin wasa

31 An bushe An tashi ko an kammala wasa

32 Hari Abokan karawa su ja }wallo da gudu rufe da

ido, suna neman gwal

33 Le [an wasa ya ba ]an gidansu }wallo, ba tare

da abokin karawa ya kar~e ba

34 Sa ido Zuwa kallon }wallon abokanin adawa domin

ganin yadda wasarsu za ta kaya

35 Ya hange6 [an wasa ya yi ritaya daga buga }wallo }afa.

36 Yanka Hikima ko dabarar wuce ]an wasa da }wallo

ba tare da ya kar~e ba

37 Ga ci ga yanka An cinye abokanin karawa, sannan an taka

musu leda

38 Mamaya A mamayi abokan karawa, tun ba su shirya ba

a buga firikik ko }wallo

39 Na saye [an wasa ya shirya kar~ar }wallon sama,

musamma wadda za a tare da gaba

6 An sarrafa kalmar aro ta ‘hang up’

Page 17: Hausar Masu {wallon {afa a Cikin Garin Sakkwatodegeljournal.org/Papers/DEGEL-2016-12-13.pdf · sha’awar }wallon }afa a cikin al’umma, haka ake samun ]imbin masu tsananin }iyayya

DEGEL JOURNAL OF FACULTY OF ARTS AND ISLAMIC STUDIES, VOl. 12, (June 2016) ISSN: 0794-9316

146 http://www.degeljournal.org UDU SOKOTO

40 Ya yi kwáánáá7 [an wasa ya rage kuzarin wasa kamar da.

41 Ya yi amai Gola ya kama }wallo ya saki, saboda ba ta

kamuwa, sabili da zafin shot ko bugu

Wa]annan jadawalai uku suna ]auke da wasu daga cikin kalmomi ko yankin jimla ko jimloli da

ke ha]uwa su samar da Hausar masu }wallon }afa a cikin garin Sakkwato. Ita wannan Hausar ta

}umshi Hausar gama-gari wadda ake iya samu a mafi yawan garuruwan }asar Hausa, da kuma

Hausa Basakkwaciya wadda ake amfani da ita a cikin garin Sakkwato kawai. Sai ha]in gambizar

Hausar masu }wallon }afa wadda ake hasashen ana amfani da ita a garin Sakkwato da wasu

garuruwan }asar Hausa. Sai dai idan muka lura da kyau, za mu fahimci cewa wannan Hausar ta

samu ne ta hanyar aron kalmomin harshen Ingilishi, ta hanyar yi musu kwaskwarima domin

dacewa da tsarin harshen Hausa. Kuma wa]annan kalmommin aro na }wallon }afa suna aiki cikin

bambance-bambancen karin harshe tamkar yadda kalmomin asali ke fuskantar rabe-rabe, saboda

kawai bambancin wurin zaman majiya harshe. Sannan kuma akan yi amfani da salon }ir}ira ta

hanyar }ir}ira daga kalmomin asali ko hikimar fa]a]a ma’anar kalmomin aro domin fassara

abubuwa sababbi wa]anda suka shafi }wallon }afa. Haka kuma, akasarin Hausar ta masu buga

}wallon }afa, ita ce mataki na farko kafin samuwar Hausar masu kallon }wallon }afa. A ta}aice,

an sami tasirin Hausar masu buga }wallon }afa a kan ta masu kallonta, saboda mafi yawan masu

buga }wallon suna kallon }wallayen da ake nunawa, na musamman }asashen waje.

8.0 Kammalawa

Binciken da aka gudanar gudummuwa ce a kan karin harshen Hausar masu }wallon }afa a cikin

garin Sakkwato. Bayanan da suka gabata sun nuna cewa akasarin masu buga }wallon }afa a garin

Sakkwato, suna kallon }wallo a gidajen kallon }wallo, sannan ana samun wa]anda ba su buga

}wallo a filayen wasanni, kuma ba su zuwa kallon }wallo a filayen buga ta, amma sai ga su suna

zuwa gidayen kallon }wallo. Saboda haka, muna iya cewa ana samun masu zuwa kallon }wallo

saboda yayi, wai an ce lokacin abu a yi shi. Wayewar kai ya taimaka wajen rage fa]ace-fa]ace a

tsakanin masu sha’awar bugawa ko kallon }wallon }afa, musamman kasancewar wa]anda suka fi

kowane mataki na cikin al’umma runguwar wannan yayin }wallon }afa matasa ne, kuma samari

maza. Daga }arshe, muna fatar wannan ma}ala ta bu]e sabon babin gudanar da zuzzurfan bincike

game da asalin Hausar masu }wallon }afa da abin da ya shafi dangantakarta da Hausar wasu

wasanni na daban, tare da duba bambancin karin harshe sosai a cikin Hausar masu }wallon }afa.

7An fa]a]a ma’anar dare da wuni ko barci zuwa ragewar samba tamkar a ce mai ko kitse ya yi kwana.

Page 18: Hausar Masu {wallon {afa a Cikin Garin Sakkwatodegeljournal.org/Papers/DEGEL-2016-12-13.pdf · sha’awar }wallon }afa a cikin al’umma, haka ake samun ]imbin masu tsananin }iyayya

DEGEL JOURNAL OF FACULTY OF ARTS AND ISLAMIC STUDIES, VOl. 12, (June 2016) ISSN: 0794-9316

147 http://www.degeljournal.org UDU SOKOTO

Manazarta

Bature, A. 1995. “Nazari kan {ir}irar Sababbin Kalmomi a Hausa”, BabbanTaron {arawa Juna

Sani na Biyar (5) kan Harshe da Adabida Al’adun Hausawa. Kano: Jami’ar Bayero.

[antumbishi, M.A. 2003. A Study of Hausa Slang in Kano Metropolis: A Sociolinguistic

Approach. Unpublished PhD Thesis, Sakkwato: Usmanu [anfodiyo

University.

[antumbishi, M.A. 2004. “Harshe, Al’umma da Kuma Zamananci”: Takardar {ara wa Juna

Ilimi da Aka Gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya. Sakkwato: Jami’ar Usmanu

[anfodiyo.

Fage, U.U. 2002. Ire-iren Karin Harshen Hausa na Rukuni. Kano: Benchmark Publishers

Limited.

Garba, S.A. 2010. Hausa a Gidan Rediyon BBC. Kundin Digiri na Biyu, Sakkwato: Jamai’ar

Usmanu [anfodiyo.

{araye, M. 2003. Sabbin Kalmomi: Ingilishi Zuwa Hausa (Littafi na [aya), Cibiyar Nazarin

Harsunan Nijeriya, Kano: Jami’ar Bayero.

Sa’id, B. (Ed.). 2006. {amusunHausa. Kano:Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar

Bayero.

Sani, M.A.Z. 2003.Alfiyyar Mu’azu Sani 3: Karorin Harshen Hausa a Wa}e. Kano:

Benchmark Publishers Limited.

Sirajo, I.2001. Hausar Kasuwanci: Yanayin {ir}irar Sababbin Kalmomia Kasuwar Garin

Sakkwato. Kundin Digiri na Farko. Sakkwato:Jami’ar Usman [anfodiyo.

Skinner, N. 1965.{amus Na Turanci Da Hausa-English, Hausa Illustrated Dictionary (Babban Jagora Ga Turanci). Zaria: Northern Nigerian Publishing Company

Ltd.

Umar, M.M. 2005. Kasuwanci da Muhimmancinsa ga Al’ummar Hausawa. Kundin Digiri na

[aya, Sakkwato: Jami’ar Usmanu [anfodiyo.

Umar, M.M. 2012. Nazarin Sa}on G.S.M a Wayar Salular Hausawa. Kundin Digiri na Biyu,

Sakkwato: Jamai’ar Usmanu [anfodiyo.

Yakasai, S.A 2005. “Aro da {ir}ira: Nazarin Samuwar Sababbin Kalmomin Hausa a Jami’a

da Kuma Garin Sakkwato”: Ma}alar da Aka Gabatar a Sashen Nazarin Harsunan

Nijeriya. Sakkwato: Jami’ar Usmanu [anfodiyo.

Page 19: Hausar Masu {wallon {afa a Cikin Garin Sakkwatodegeljournal.org/Papers/DEGEL-2016-12-13.pdf · sha’awar }wallon }afa a cikin al’umma, haka ake samun ]imbin masu tsananin }iyayya

DEGEL JOURNAL OF FACULTY OF ARTS AND ISLAMIC STUDIES, VOl. 12, (June 2016) ISSN: 0794-9316

148 http://www.degeljournal.org UDU SOKOTO

Yakasai, S.A 2007. “Dangantakar Harshe Da Al’umma: Nazarin Halaye Da [abi’un

Magana a Al’ummar Hausawa”: Ma}alar Da Aka Gabatar a Sashen

Harsunan Asiya da na Afrika. Beijing: Jami’ar Koyon Harsunan Waje.

Yakasai, S.A 2010. “Dangantakar Harshe Da Muhallin Magana: Nazarin Kan Matakan

Magana a Tsakanin Al’ummar Hausawa”. In Harsunan Nijeriya. Centre For

The Study of Nigerian Languages, Bayero University Kano: Volume XXII, Pp.

78-84.

Yakasai, S.A. 2012. Jagoran Ilmin Walwalar Harshe. Sokoto: GarkuwaMedia Services.

Yule, G. 1985. The Study of Language: An Introduction. Australia: Cambridge University

Press.