datti assalafiy 2 hrs

6
Follow Datti Assalafiy 2 hrs · 'BARAKA DA RIKICI YA KUNNO A TSAKANIN KUNGIYAR BOKO HARAM/ISWAP Naga ya dace mu sanar da jama'a wani sabon baraka da ya kunno kai a tsakanin kungiyar Boko Haram/ISWAP dake wanzar da ayyukan ta'addanci a yankin tafkin Chadi Amma kafin nan, na saurari wani audio da BBC Hausa suka daura a shafinsu na Facebook suka kawo rohoto akan yadda kungiyar Boko Haram ta shafe shekaru 10 tana azabtar da al'ummah, ba laifi, BBC Hausa sunyi kokari akan wannan rahoto Sai dai sun manta ba su fadawa al'umma cewa Boko Haram ISWAP sun canza shugaba wanda yake 'dan Muhammad Yusuf ne na cikinsa ba, wato Habib Muhammad Yusuf (Abu Mus'ab Al-barnawiy), an canza Al- barnawiy tun a watan biyu na wannan shekara (2019) saboda sun zargeshi da neman hadin kai da wata kungiyar ta'addancia Kasar Mali wacce bata dace da tsarin ISIS ba. Manyan kwamandojin kungiyar ISWAP da kansu suka fito daga markazinsu, suka hau jiragen ruwa suka hadu a wani babban sansaninsu dake Kwalaram anan yankin tafkin Chadi suka tattauna, anan ne suka kori 'dan gidan Muhammad Yusuf (Al-barnawiy) daga shugabanci, suka nada sabon shugaba mai suna Abu Abdullahi, rundinar sojin Nigeria ta tabbatar da wannan sabon nadin shugaba da ISWAP tayi, don haka ya dace a rahoto na gaba BBC Hausa ku gyara A yanzu haka halin da ake ciki Boko Haram/ISWAP ta fada cikin wani yanayi na sabon rikici da rarrabuwan kai, yanzu haka suna neman wani babban kwamandan yakinsu mai suna Umaru Leni, 'dan asalin wani gari ne da ake kira Zariyan-Kala-Kala dake jihar Kebbi Umaru Leni ya wawuri wasu makudan kudaden kungiyar da suka tara don daukar nauyin ta'addanci da sayen makamai, sai ya gudu da kudin, ana hasashen ya gudu zuwa kasar Mali ko Chadi, kafin Umaru Leni ya gudu da kudin ISWAP; akwai sahihan bayanan sirri da ya shigo mana a watan da ya gabata cewa duk wani Bahaushe, da kabilar Shuwa-arab, da Fulani wadanda suke cikin ISWAP a yankin tafkin chadi shugabannin kungiyar sun kwace bindigoginsu.. Sai aka bar Kanuri kadai da wata kabila da ake kira buduma da makamantansu, su kuma kabilar buduma rabinsu 'yan Nigeria ne, rabinsu 'yan chadi, zamane ya hadasu a nan yankin tafkin Chadi suka hadu suka samar da kabila shekaru masu yawa, lokacin da annobar Boko Haram tazo da yawansu sun zama mayaka, har ma da manyan kwamandoji To bayan wannan abu ya faru an kwace bindigogi a hannun kabilun da ba'a aminta da su ba a cikin kungiyar, sai kawai aka wayi gari Umaru Leni ya wawure tattalin arzikin kungiyar ya gudu, kuma har yanzu babu tabbacin ga inda ya buya da kudin, haka ya taba faruwa a kungiyar Boko Haram karkashin jagorancin Shekau, Shekau ya taba wawure wasu makudan kudade da suka karba na kudin fansa daga hannun gwamnatin Faransa, yana daga cikin babban abinda ya haddasa tarwatsewar Boko Haram Umaru Leni kwararren 'dan ta'adda ne, kuma babban kwamandan yaki da ake jin tsoronsa, samun hotonsa yayi wahala matuka, kamar shekara 3 da suka gabata jami'an tsaron sirri da 'yan sa kai sun taba bin diddiginsa, an taba ganinsa ya kai sau 2 ko 3, amma da zaran an ganshi cikin lokaci lokaci kankani sai a rasa inda yayi, amma dai muna da cikakken yakini zai fada tarko watarana Mu abinda muke so kenan a samu mummunan baraka da rabuwar kai a tsakanin wadannan kungiyoyin ta'addanci, ita kanta gwamnatin Nigeria ya dace tayi amfani da 'yan leken asirinta wajen kunna wutar rabuwar kai a tsakanin kungiyoyin ta'addancin, hakan zai taimaka wajen murkushe su, akwai hanyoyin da akebi a ilmin tsaro a kunna wutar rikici a tsakanin kungiyoyin ta'addanci da na 'yan bindiga da manyan kungiyoyin barayi, amma wannan yana bukatar sirri

Upload: others

Post on 01-Feb-2022

3 views

Category:

Documents


0 download

TRANSCRIPT

Page 1: Datti Assalafiy 2 hrs

Follow Datti Assalafiy 2 hrs · 'BARAKA DA RIKICI YA KUNNO A TSAKANIN KUNGIYAR BOKO HARAM/ISWAP Naga ya dace mu sanar da jama'a wani sabon baraka da ya kunno kai a tsakanin kungiyar Boko Haram/ISWAP dake wanzar da ayyukan ta'addanci a yankin tafkin Chadi Amma kafin nan, na saurari wani audio da BBC Hausa suka daura a shafinsu na Facebook suka kawo rohoto akan yadda kungiyar Boko Haram ta shafe shekaru 10 tana azabtar da al'ummah, ba laifi, BBC Hausa sunyi kokari akan wannan rahoto Sai dai sun manta ba su fadawa al'umma cewa Boko Haram ISWAP sun canza shugaba wanda yake 'dan Muhammad Yusuf ne na cikinsa ba, wato Habib Muhammad Yusuf (Abu Mus'ab Al-barnawiy), an canza Al-barnawiy tun a watan biyu na wannan shekara (2019) saboda sun zargeshi da neman hadin kai da wata kungiyar ta'addancia Kasar Mali wacce bata dace da tsarin ISIS ba. Manyan kwamandojin kungiyar ISWAP da kansu suka fito daga markazinsu, suka hau jiragen ruwa suka hadu a wani babban sansaninsu dake Kwalaram anan yankin tafkin Chadi suka tattauna, anan ne suka kori 'dan gidan Muhammad Yusuf (Al-barnawiy) daga shugabanci, suka nada sabon shugaba mai suna Abu Abdullahi, rundinar sojin Nigeria ta tabbatar da wannan sabon nadin shugaba da ISWAP tayi, don haka ya dace a rahoto na gaba BBC Hausa ku gyara A yanzu haka halin da ake ciki Boko Haram/ISWAP ta fada cikin wani yanayi na sabon rikici da rarrabuwan kai, yanzu haka suna neman wani babban kwamandan yakinsu mai suna Umaru Leni, 'dan asalin wani gari ne da ake kira Zariyan-Kala-Kala dake jihar Kebbi Umaru Leni ya wawuri wasu makudan kudaden kungiyar da suka tara don daukar nauyin ta'addanci da sayen makamai, sai ya gudu da kudin, ana hasashen ya gudu zuwa kasar Mali ko Chadi, kafin Umaru Leni ya gudu da kudin ISWAP; akwai sahihan bayanan sirri da ya shigo mana a watan da ya gabata cewa duk wani Bahaushe, da kabilar Shuwa-arab, da Fulani wadanda suke cikin ISWAP a yankin tafkin chadi shugabannin kungiyar sun kwace bindigoginsu.. Sai aka bar Kanuri kadai da wata kabila da ake kira buduma da makamantansu, su kuma kabilar buduma rabinsu 'yan Nigeria ne, rabinsu 'yan chadi, zamane ya hadasu a nan yankin tafkin Chadi suka hadu suka samar da kabila shekaru masu yawa, lokacin da annobar Boko Haram tazo da yawansu sun zama mayaka, har ma da manyan kwamandoji To bayan wannan abu ya faru an kwace bindigogi a hannun kabilun da ba'a aminta da su ba a cikin kungiyar, sai kawai aka wayi gari Umaru Leni ya wawure tattalin arzikin kungiyar ya gudu, kuma har yanzu babu tabbacin ga inda ya buya da kudin, haka ya taba faruwa a kungiyar Boko Haram karkashin jagorancin Shekau, Shekau ya taba wawure wasu makudan kudade da suka karba na kudin fansa daga hannun gwamnatin Faransa, yana daga cikin babban abinda ya haddasa tarwatsewar Boko Haram Umaru Leni kwararren 'dan ta'adda ne, kuma babban kwamandan yaki da ake jin tsoronsa, samun hotonsa yayi wahala matuka, kamar shekara 3 da suka gabata jami'an tsaron sirri da 'yan sa kai sun taba bin diddiginsa, an taba ganinsa ya kai sau 2 ko 3, amma da zaran an ganshi cikin lokaci lokaci kankani sai a rasa inda yayi, amma dai muna da cikakken yakini zai fada tarko watarana Mu abinda muke so kenan a samu mummunan baraka da rabuwar kai a tsakanin wadannan kungiyoyin ta'addanci, ita kanta gwamnatin Nigeria ya dace tayi amfani da 'yan leken asirinta wajen kunna wutar rabuwar kai a tsakanin kungiyoyin ta'addancin, hakan zai taimaka wajen murkushe su, akwai hanyoyin da akebi a ilmin tsaro a kunna wutar rikici a tsakanin kungiyoyin ta'addanci da na 'yan bindiga da manyan kungiyoyin barayi, amma wannan yana bukatar sirri

Page 2: Datti Assalafiy 2 hrs

Muna rokon Allah Ya kara jefa sabani da rabuwar kai a tsakanin kungiyoyin ta'addanci a Nigeria, Allah Ka shefa tasirinsu, Ka zaunar mana da Kasarmu lafiya Amin See Translation

Page 3: Datti Assalafiy 2 hrs
Page 4: Datti Assalafiy 2 hrs

https://www.facebook.com/permalink.php?story_fbid=995317890799272&id=100009632104217

Page 5: Datti Assalafiy 2 hrs
Page 6: Datti Assalafiy 2 hrs