bashi kan jingina na jam’iyyar ci gaba ta garin konkorindonawa bisa ga zancen bashi tare da...

7
1 Capitalisation des bonnes pratiques en appui à la production agricole et à la sécurité alimentaire Gabatarwa Mawallafa: Salmou Hassane da Fatuma Dela Sidi Takardar bayyani Nijar Agusta 2012 Bashi kan jingina na jam’iyyar ci gaba ta garin Konkorindo Wannan takadar tana ba da bayani bisa ga husa’ar da jam’iyyar ci-gaba ta Konkorindo wadda a *alla yau da shekara goma (10) ta fara ayyukan bashi kan jingina. A halin yanzu, tana kawo gudunmuwa sosai ga bu*atun manona waùanda wani bi ana mancewa da su bisa tsarin tafiyar da ayyukan karkara da na samun biyan bu*atu ta fanni daban-daban. Jam’iyyar ci gaba tana da cibiyarta a garin Konkorindo, kwamin ùin kiyeshe lardin Dogon Dutsi jahar Doso a jamhuriyar Nijar. An kafa ta a shekarar 2002-2003 bayan wani aikin haùin gwiwa na bashi kan jinjina na hatsi tsakanin *ungiyar manoma ta maza mai suna « Haùin Kai » ta Konkorindo da asusun lamani da a kira Tanadi da ya ba da bashin jikka ùari shidda (600 000 F). Babban gurin shi ne, a samu a yi tattalin cimaka har ta wuce lokacin rani kuma a samu kuùi domin tafiyar da aikin damana ta gaba. Ga da, ana saida cimaka tun lokacin kakar farin, abun da ke sa in rani ya shiga manoma ba su da wata issasar cimaka, bayan haka ba su da wasu kuùi waùanda za su sayen kayan aikin noma, baicin haka, ajiyar nagartaccen iri na shibka ta zama mawuyacin abu, ga shi kuma babu bashi babu wata kafa ta samun kuùi. Game da sakamako nagari da aka samu, Tanadi da kuma *ungiyoyin manoma Hadin Kai da suka tafiyar da ayyukansu tare sun shaida ma *ungiyoyin manoma ma*wabta da irin nasarar da suka ci, kuma suka nemi ra’ayinsu domin ci-gaba da tafiyar da ayyukan bashi kan jingina shekaru masu zuwa. µungiyoyi huùu (4) na manoma suka *aru (Gwala, Kisage, Tsandarawa, Gurguzu), tare da*ungiyar manoma ta garin Konkorindo suka girka jam’iyyar ci-gaba a 2004. A shekarar 2012, kenan shekara takwas bayan kafuwarta, jam’iyyar ci-gaba ta ùaukaka sosai. Ta fuskar *ungiyoyi, yawan *ungiyoyi mamba ya lumka gida goma : daga 5 har ya kai *ungiyar manoma 51 *ungiyar 25 na maza, 25 na mata da 1 ta maza da mata. Sun *unshi gari 36 da mambobi 1150 daga cikinsu akwai namiji 650 da mace 500. A shekarar 2010, ta haùu da wasu jam’iyyu uku don *afa tarayyar *ungiyoyin manoma da ake kiran Fara’a. A fuskar kuùi, jam’iyyar ci-gaba tare da haùin gwiwar asusun kuùi na tanadi sun tafiyar da bashi kan jingina, da ya lumka har so 700 yawan kayan da suka ba da kan, daga jikka ùari shida (600 000 F) bashin ya kai zuwa a *alla miliyon 425 000 000. Ayyuka sai suka yalwata, suka wuce daga bashi kan jingina na fannin maza na hatsi zuwa ga bashi kan jingina na maza ko na mata ko kuma na maza da mata (hatsi, wake, gujiya, gujiyar *uruga, ya*uwa, riùi). Gujiya, noman mata ne, ana noma ta a *ananan wurare, kuma ba sai an sa mata taki mai yawa. Hatsi da wake, da yakuwa da riùi, su ne ke bu*atar wuri mai yawa, maza suke noma su. Waùannan ire-iren noma dukan mutane maza da mata suna tafiyar da su, amma ta girman wuraren kaùai yake bambanta.

Upload: others

Post on 29-Oct-2020

4 views

Category:

Documents


0 download

TRANSCRIPT

Page 1: Bashi kan jingina na jam’iyyar ci gaba ta garin Konkorindonawa bisa ga zancen bashi tare da TANADI. Masu kula da harakokin kuùi na Tanadi, suna tafiyar da ayyuka na ba da bashi

1

Capitalisation des bonnes pratiquesen appui à la production agricoleet à la sécurité alimentaire

Gabatarwa

Mawallafa: Salmou Hassane da Fatuma Dela Sidi

Takardar bayyani Nijar Agusta 2012

Bashi kan jingina na jam’iyyar ci gaba ta garin Konkorindo

Wannan takadar tana ba da bayani bisa ga husa’ar da jam’iyyar ci-gaba ta Konkorindo wadda a *alla yau da shekara goma (10) ta fara ayyukan bashi kan jingina. A halin yanzu, tana kawo gudunmuwa sosai ga bu*atun manona waùanda wani bi ana mancewa da su bisa tsarin tafiyar da ayyukan karkara da na samun biyan bu*atu ta fanni daban-daban.

Jam’iyyar ci gaba tana da cibiyarta a garin Konkorindo, kwamin ùin kiyeshe lardin Dogon Dutsi jahar Doso a jamhuriyar Nijar.

An kafa ta a shekarar 2002-2003 bayan wani aikin haùin gwiwa na bashi kan jinjina na hatsi tsakanin *ungiyar manoma ta maza mai suna « Haùin Kai » ta Konkorindo da asusun lamani da a kira Tanadi da ya ba da bashin jikka ùari shidda (600 000 F).

Babban gurin shi ne, a samu a yi tattalin cimaka har ta wuce lokacin rani kuma a samu kuùi domin tafiyar da aikin damana ta gaba. Ga da, ana saida cimaka tun lokacin kakar farin, abun da ke sa in rani ya shiga manoma ba su da wata issasar cimaka, bayan haka ba su da wasu kuùi waùanda

za su sayen kayan aikin noma, baicin haka, ajiyar nagartaccen iri na shibka ta zama mawuyacin abu, ga shi kuma babu bashi babu wata kafa ta samun kuùi.

Game da sakamako nagari da aka samu, Tanadi da kuma *ungiyoyin manoma Hadin Kai da suka tafiyar da ayyukansu tare sun shaida ma *ungiyoyin manoma ma*wabta da irin nasarar da suka ci, kuma suka nemi ra’ayinsu domin ci-gaba da tafiyar da ayyukan bashi kan jingina shekaru masu zuwa. µungiyoyi huùu (4) na manoma suka *aru (Gwala, Kisage, Tsandarawa, Gurguzu), tare da*ungiyar manoma ta garin Konkorindo suka girka jam’iyyar ci-gaba a 2004.A shekarar 2012, kenan shekara takwas bayan kafuwarta, jam’iyyar ci-gaba ta ùaukaka sosai. Ta fuskar *ungiyoyi, yawan *ungiyoyi mamba ya lumka gida goma : daga 5 har ya kai *ungiyar manoma 51 *ungiyar 25 na maza, 25 na mata da 1 ta maza da mata. Sun *unshi gari 36 da mambobi 1150 daga cikinsu akwai namiji 650 da mace 500. A shekarar 2010, ta haùu da wasu jam’iyyu uku don *afa tarayyar *ungiyoyin manoma da ake kiran Fara’a.

A fuskar kuùi, jam’iyyar ci-gaba tare da haùin gwiwar asusun kuùi na tanadi sun tafiyar da bashi kan jingina, da ya lumka har so 700 yawan kayan da suka ba da kan, daga jikka ùari shida (600 000 F) bashin ya kai zuwa a *alla miliyon 425 000 000. Ayyuka sai suka yalwata, suka wuce daga bashi kan jingina na fannin maza na hatsi zuwa ga bashi kan jingina na maza ko na mata ko kuma na maza da mata (hatsi, wake, gujiya, gujiyar *uruga, ya*uwa, riùi). Gujiya, noman mata ne, ana noma ta a *ananan wurare, kuma ba sai an sa mata taki mai yawa. Hatsi da wake, da yakuwa da riùi, su ne ke bu*atar wuri mai yawa, maza suke noma su. Waùannan ire-iren noma dukan mutane maza da mata suna tafiyar da su, amma ta girman wuraren kaùai yake bambanta.

Page 2: Bashi kan jingina na jam’iyyar ci gaba ta garin Konkorindonawa bisa ga zancen bashi tare da TANADI. Masu kula da harakokin kuùi na Tanadi, suna tafiyar da ayyuka na ba da bashi

2

Hanyar tafiyar da ayyuka

Ta hanyar tafiyar da aiki, jam’iyyar ta kawo wani gyara bisa ga yadda ya kamata a tafiyar da bashi kan jingina. Kuma ta ba da hannu wajen ayyukan bashi (bashin taki da kuma bashin zuwa ga mata), da kuma *arfafa ayyuka masu kawo kuùi, da fama ga ayyukan noman rani, kafa kantin saida kayan aikin noma, da kuma tafiyar da horo bisa da husa’o’in noma.

A halin yanzu, babban guri da jam’iyyar ci-gaba ta sa gabanta, shi ne, ya*i da talauci da kuma *ara taimakon juna tsakanin mambobin, kuma jam’iyyar ta ba da *arfi bisa bu*atun mambobi.

Waùanda ayyukan bashi Kan jngina ya shafa

Masu cin moriyar

Masu amfani da bashin da aka ba da ta hanyar bashi kan jingina, suna iya zama mambobi ne ko kuma ba mambobi ba daga *ungiyoyin manoma 51 na jam’iyyar ci gaba, kuma suna cikin masu matsayi daban-daban na rayuwar jama’a.

� µanana da matsakantar manoma: Samun bashi ta hanyar bashi kan jingina, samun cimaka lokacin rani da manoma ke cema « kaka ta biyu », bada horo ,ajiyar isassun kuùi, domin tafiyar da ayyuka masu kawo kuùi su ne ire-iren amfanin da suka samu ta hanyar bashi kan jingina. Yanzu manoma suna cin amfanin waùannan abubuwa, lokacin da aka soma aikin jam’iyya waùannan abubuwa ba a sa su ciki ba.Ta hanyar bashi kan jingina aka san waùannan abubuwa, kuma aka ba mutane horo daban–daban kansu. Bayan haka sun samu sun tafiyar da yawon buùa-ido a cikin gida da *asashen *etare.

� Mutanen da ba su noma, amma suna sayen kayayyaki domin su ba da a wurin bashi kan jin-gina.

� Manyan <an kasuwa–manoma : Su suka mallaki wuraren aje kaya da kuma manyan kayayya-ki, su ne waùanda suka fi cin amfanin ayyukan noma. Da yake su ke da kaya mahi yawa, su ne kuma za su samun bashi mai ùimçin yawa. Sai su sa ma’azar kayansu haya, a *alla ana ba su dala ishirin ga kowane buhu, su ne, sai yadda suka faùi ckin *ungiyar manoma, wajen tattau-nawa bisa ga zancen bashi tare da TANADI.

� Masu kula da harakokin kuùi na Tanadi, suna tafiyar da ayyuka na ba da bashi kan jingina ga jam’iyyar ci-gaba, tun shekara ta farko. Game da haka, Tanadi tana ùaya daga cikin wadanda suka ci moriyar wannan jarrabawar inda ta samu riba a jimilce ta miliyon 58.000.000 kuma fiye da miliyon huùu (4.000.000) na kuùin aje takardun neman bashi.

Abokan hulùa masu tallafi

� Furoje mai kula da yalwata kayan aikin noma FAO, da *asar beljik ke ùaukar nauyinshi daga shekara (1999-2008), ya ba da gudunmuwarshi wajen girka bashi kan jingina.

� Tsari game da tatallin sani kan da jinsi na FAO, musamman furoje mai kula da tafiyar da nagar-tattun ayyuka da kuma kawo gudunmuwa bisa albarkar noma da tabbatar da kwanciyar hankali a fannin samun cimaka (2009-2012).

� Wanda *asar beljik ke ùaukar nauyinshi, tun sekarar 2010 ya kawo gudunmuwarsa bisa ga abun da ya shahi horon mambobi ta hanyar waye kai, tafiyar da husa’o’i, da kuma kula da hulùa da wasu *ungiyoyin manoma na Nijar da na *etare da kuma sauran masu hannu da shuni.

� Furoje mai kula da *arfafa aikin noma ta hanyar yalwata kantunan saida kayan aikin gona na jam’iyyu. IARBIC, a shekarun (2009- 2013), *ungiyar FAO ta tafiyar da aikinshi, da gudunmu-mar kuùi na haùin gwiyar *asashen Turai, *asar Luksambur, ta Beljik, da ta Espana, da ke ta-fiyar da ayyukansu kan tabbatar da kwanciyar hankali a fannin samun cimaka ta hanyar *arfafa sanin manoma maza da mata ta hanyar (gonar gwaji). Gudunmuwar da furojen ya kawo ma jam’iyyar ci-gaba, shi ne ùaukar nauyin gina kantuna, da ba da taki, da horo ta hanyar *arfafa sanin shugabanin komitocin tafiyar da aikin jam’iyya da bun*asa bashi kan jingina ta hanyar gina mangazozi na aje kayan da za a ba da bashi kan jingina. A shekarar 2010 ne suka fara bada tallafi ta hanyar bashi kan jingina.

Page 3: Bashi kan jingina na jam’iyyar ci gaba ta garin Konkorindonawa bisa ga zancen bashi tare da TANADI. Masu kula da harakokin kuùi na Tanadi, suna tafiyar da ayyuka na ba da bashi

3

� Asusun Ameli : Wannan husa’ar, an tafiyar da ita *ar*ashin furoje kapitalizasiyon da *ungiya mai zama kanta wadda ake kira VIE da turanci da ta samu tallafi daga *ungiyar « Roi Baudin » da turanci, tana taimakawa wajen tafiyar aikin da jam’iyya don kanta da kanta da tallafawa wajen gina wuraren aje kan cimaka ta bashi kan jingina, ba da kayan aikace-aikacen gida na mata, kafa ayyuka masu kawo kuùi, ya*i da jahilci, horo zuwa ga mata.

Hanyar tafiyar da ayyuka

Don ciwo kan matsalolin da suka shafi kare cimaka a lokacin rani, jam’iyyar ci-gaba, tare da furoje mai *ula da taki na FAO, da kuma Kapitalizasiyon da IARBIC, sun tafiyar da aikinsu kan abu biyu :

Ginshi*in al‘adu da tabi’o’i :

Komowa bisa hanyar tabi’o’in dauri a garin Konkorindo, musamman ma amfani da «Rumbun gari » ko kuma rumbun tsimi. Dole, kowane mai gida ya aje wani kashi daga cikin cimakarshi cikin ruhewa ta tarayya a karkashin jagorancin mai gari, ba za ya ùebi komi ba sai lokacin rani. Wannan husa’a ta gargajiya, jam’iyya ta gudanar da ita a lokacin tafiyar da waye kai na farko, don ta sa *ungiyoyin manoma su san, kuma su amince da bashi kan jingina, da ke da ala*a da wannan.

Sau*in *a’idodin samun shiga ayyukan bashi kan jingina : Hanyar taimakon juna da ke ga mutanen karkara ita ta kawo rashin yin bambanci tsakanin mambobi da waùanda ba mambobi ba wajen samun wurin aje kayansu.

Ginshi*i na zama bai ùaya :

Da farko Bashi kan jingina, aiki ne, na maza da aka keçe ma manoma. Sannan aka buùa husa’ar ga mata, don su samu su haùa kayan kuma su samu biyan bashi. Misali, a da, jam’iyyar ci-gaba ita ke tattaunawa wajen neman bashi a wajen masu kula da lamani da yin sauran abubuwa kamar wallafa takardu, tattalin kayan da aka aje mangaza, da kulawa da basussuka) waùanda sun danganta ga *ungiyoyin manoma na maza.Tun daga <an shekaru kaùan ne, jam’iyyar tana *o*arin kawo sauyi game da bashi kan jingina, domin kowa ya ci amfanin wannan abu (manoma manya da *anana, maza da mata, makiyaya…), dangance da haka, jam’iyyar ta yi aiki kamar haka :µarfafa tsarin samun wurin noma na mutum guda ko na jama’a, hanya ce ga matan da ba su da filin noma su samu bashi kan jingina.

� Baza sakamakon da aka samu tsakanin *ungiyoyin manoma na maza da na mata. Kahin a girka jam’iyyar, *ungiyar manoma ta maza na karçar bashin kayan gona ko kuma bashin taki, da suke ba da hanya wajen tafiyar da bashi kan jingina da ke da mahimmaci wajen bun*asa ayyukan noma.

� Don yin aiki da çukatun manoma mata, jam’iyya ta tattauna kuma ta isar da takarda don buùa bashi zuwa ga *ugiyoyin manoma mata.

� Yalwata ire-iren kayan da za a ba da da bashi kan jingina : hatsi, shi ne cimaka ta farko wadda aka fara tafiyar da bashi kan jingina da ita, tsarin tafiyar da bashi kan jingina sun ya waùansu irin cimaka don tafiyar da bashi kan jingina da su misali (wake, *uruga, yakuwa.) Wannan bab-ban abu ne, musamman ga mata.

� Buùa wasu ayyuka da za su *arfafa gaba da baya ayyukan bashi kan jingina. waùannan ayyu-ka sun *unshi noman rani, gonar gwaji, kantunan saida kayan noma, ko kuma yin adashe ta *ungiyar manoma wajen çangaren mata ko kuma wasu ayyuka na taimakon juna da za su janyo kuùi.

� Tafiyar da cikakkiyar hulùa ta so da yarda tare da asusu guda ùaya mai ba da lamani, da kuma biyan bashi dangance da *a’idodin da a aka aza.

� Ingantar da *ungiyoyin manoma na mata domin su isar da labaru bisa bashi kan jigina.

Page 4: Bashi kan jingina na jam’iyyar ci gaba ta garin Konkorindonawa bisa ga zancen bashi tare da TANADI. Masu kula da harakokin kuùi na Tanadi, suna tafiyar da ayyuka na ba da bashi

4

Shekaru Yawan garuruwan da suka samu bashi

Kuùin da aka samu na CFA

2002/2003 1 600 000

2003/2004 5 1 845 000

2004/2005 10 18 783 000

2005/2006 29 85 000 000

2006/2007 23 68 826 650

2007/2008 23 59 480 000

2008/2009 25 80 721 000

2009/2010 14 58 761 500

2010/2011 13 21 747 000

Jimilla 424 017 150

TASIRI

Kusan shekara goma da aka fara gwado wannanhusa’a yawan bashin da aka ba da ta hanyar jin-gina ya tashi daga jikka (600 000F) zuwa miliyon (424 017 150F).

Bashi kan jingina ya sa mutane su bar banzatar da cimakarsu har sai ta kai lokacin da za su amfa-ni da cimakarsu ita biyu. Cimakar da aka aje, ita ake ce ma cimaka ta biyu, dalilin akwai isasshen abinci lokacin rani kuma an yi tanadin irin shibka.

« Kuma zuwa cin rani na maza ya rage dalilin bashi kan jingina da ya ba da damar tafiyar da wasu ayyuka lokakacin rani, misali kasuwanci, noman rani. Da, lokacin rani wata dama ce ta tafiya diga ga matasa. Sabili da bashi kan jingina, samari da yawa a yanzu sun tsaya gida domin tafiyar da ayyuka daban–daban da suka haùa da kasuwancin cimaka, saida kaji… », kamar yadda mai gari ya faùi lokacin da aka tafiyar da wannan rahoto.

Ko da yake, manoma na amfani da kishi shidda bisa ùari (6%) na yawan kayayyakinu da aka sa bashi kan jingina, a shekarar 2010, abun ya kai kashi ashirin da bakwai bisa ùari (27 %) daga yawan mutanen da suka tafiyar da bashi da jingna. A cikin gudanar da wannan aiki, kowane mai gida shi ke kula da tattara kaya da kai su ma’aza a sunanshi. Rabin kayan da aka aje, kaya ne da maigidan da kanshi yake kula da su amma kayan sun danganta da yawan mutanen da suke iya aiki cikin iyali. Ta wani çangare kuma sun danganta da irin *o*arin wasu mambobin iyali misali mata. A lokacin ba da bashin, mai gida yake yanke shawara dangance da kayan da iyali suka noma, ko da mata sun sa hannunsu cikin aikin. Ko da yake su mata kayan da suka noma cikin filinsu ne suke amfani da su.

Sabili da bashi kan jingina manoma mata sun samu sun *arfafa ayyuka masu kawo kuùi, musam-mam ma abun da ya shafi kiwo da, kasuwancin cimaka. Bayan haka suna tafiyar da noman rani, waùannan wuraren noma an same su ta hanyar bashi kan jingina. Manoman waùannan kayayyaki sun samu amfani sosai da ya ba da damar tafiyar da wasu sana’o’i kamar masu kantuna, masu saida kaji, masu noma, noman rani…

Cikin *auye, kamar garin Konkorindo, bayan noman damana, ana iya gane arzikin mutum ta hanyar yawan dabbobi. Ta wannan fannin akwai sauyi mai yawa da aka samu a cikin yankin: A

Amince ma husa’ar

Wannan husa’ar; ta samu amincewar, duka waùanda tsarin ya shafa, sun yarda da babban amfaninta musamman dangane da rishin cimaka lokacin rani da rishin kuùi. Mutanen garuruwa 36 da ke mamba da kuma makwabtansu, da manoma da waùanda ba manoma ba, sun tabbattar da sun samu amfanin wannan jarrabawa ta garin Konkorindo, kamar yadda ka san cewa tsarin ya nuna da kuma *aruwar garuruwa da yawan cimaka.

Page 5: Bashi kan jingina na jam’iyyar ci gaba ta garin Konkorindonawa bisa ga zancen bashi tare da TANADI. Masu kula da harakokin kuùi na Tanadi, suna tafiyar da ayyuka na ba da bashi

5

halin yanzu mata dayawa da ke tafiyar da bashi kan jingina sun mallaki dabbobi masu yawa da suka haùa da awaki, tumaki, shanu mafi yawan manoma kiwon shanu suke yi, garkunansu sun *aru sosai. Ba shakka bashi kan jingina ya ba da damar *aruwar dabbobi masu yawa, abun da ya kawo ci gaban ayyukan tattalin arziki cikin garuruwan. Bashin da aka samu ta hanyar bashi kan jingina na ba mutane damar tafiyar da wasu ayyukkan tattalin arziki, abun da yake sa suke barin kayansu har kuùin kayan da suka aje ya *aru.

Har da *aramcin halin aiki da ya haùa da masu ba da horo, da *aramcin kuùi da jam’iyyar take ciki, jam’iyyar ta samu ta tafiyar da bashi kan jingina kamar yadda ta kamata musammm zuwa ga masu *aramin *arfi, da kawo masu babban sauyi wajen gudanar da ayyukansu.

Sabin canje-canje da ingantattun hanyoyin cim ma nasara

Canje-canje :

� Sa hannu da yarjejeniya ta bashi kan jingina ga mambobi *ugiyoyin manoma : A shekarun farko, jam’iyyar ita kaùai ke sa-hannu bisa ga yarjejeniyar bashi kan jingina ga mambobin *ungiyar manoma, a halin yanzu, an rarraba wannan sa-hannu. A yanzu kowace *ungiyar manoma da masu ba da lamani ke sa-hannu bisa ga takarda.

� Buùa bashi kan jingina ga fiye ga mambobin *ungiyar manoma, na ba manoman da ba su da *arfin biyan tarbace–tarbace da kuma sauran kuùin shiga tsarin *ungiyar manoma da su samu bashi kan jingina. Daga nan, sai su samu kuùin da za ya ba su damar shiga *ungiyar mano-ma.

� Ana iya yin zubin kuùi tun lokaci bai kai ba : *ungiyoyin manoma, sun amince da cewa mu-tane suna iya yin zubi kahin lokaci, zubi na rabi da rabi har a samu a biya, *ungiyar manoma za ta tattara takardun har a yi biyan *arshe zuwa ga Tanadi.

� A kafa kamasho bisa ga kowane buhu. Daga shekarar 2011, an aza dalla arba’in bisa kowane buhu domin ba jam’iya da *ungiyar manoma damar su tafiyar da ayyukan bashi kan jngina kansu da kansu. In da a ce, an tafiyar da wannan kamasho tun lokacin soma bashi kan jingina ne, da jam’iyya ta samu miliyoyi da dama. Wannan turanin ya sa aka aza wannan kamasho.

� Kafa *a’idodin tafiyar da aiki da za su ba masu *aramin *arfi damar shiga bashi kan jingina.

� Yin Amfani da kafofin yaùa labaru da kuma hanyoyin sadarwa na karkara da suka dace: *ofa da *ofa, kabu–kabu, salula, ùan *ira.

Manyan hanyoyin cin nasara :

� Husa’o’i nagari: tun daga shekara 2004 har zuwa yanzu, ba tare da an tsaida ba, kayan da aka aje da kuma bashi suna sauwaya, abun da ke nufin cewa, husa’ar da jam’iyya da *ungiyar manoma suka tafiyar da ta danganta da halin fari, kamar *aramcin abinci na shekarar (2005 da 2011) ko kuma *aramcin kaya daga masu ba da lamani.

� Husa’ar yin aikin sa-kai daga ma’abutan jam’iyyar na gari: (masu gari, mambobin buro na jam’iyya, da kuma jan *o*arin mambobin *ungiyar manoma maza da mata).

� Yin aiki da kayan gari (mangazozin masu kuùi…) Neman hanyoyin samar ma jam’iyya <ancin kanta game da kayan aiki: mangazozi, *arfafa sanin mambobi da yawaita abokan hulùa a fan-nin kuùi da husa’a.

� Yanayi a fannin al’adu: mai kyau ne don ya ba maza da mata damar shiga cikin *ungiyoyi.

� Sauyi a cikin jam’iyya don ba mata damar su samu mukami a cikin jam’iyya.

� Dogon nazari bisa ga ùaukar bu*atun maza da mata a kan matsayi guda.

� µarfin tafiyar da ayyuka, musamman *ungiyoyin manoma mata domin tafiyar da ayyukansu na bashi kamar yadda ya kamata.

Page 6: Bashi kan jingina na jam’iyyar ci gaba ta garin Konkorindonawa bisa ga zancen bashi tare da TANADI. Masu kula da harakokin kuùi na Tanadi, suna tafiyar da ayyuka na ba da bashi

6

� Cikkaken yanayi wajen ba da labaru tsakanin jam’iyya da kungiyar manoma

� Bin al*awulla na tsakanin masu ba da lamani da kuma sauran masu hannu da shuni, abun da ke sa cikakkiyar yarda.

� Ban hannun furoje IARBIC da furoje kapitalizasiyon tun daga shekarar 2011.

Cikas

An samu cikas da dama, amma akwai matakai da jam’iyyar ta ùauka don magance wasu daga cikinsu :

� Damana marar kyau, kamar irin ta shekarar 2011, sabili da *aramcin ruwan sama, da suka hana jam’iyyar tafiyar da ayyukan bashi kan jingina, in ba wasu kaùan daga cikin <an kasuwa da ke da hali ba.

� Yawan mambobin da ba su iya karatu da rubutu ba, maza da mata, na kawo cikas wajen fannin sani da kuma iya rubutawa. A shekarar 2012, an tafiyar da wani tsari na ya*i da jahilci cikin garuruwa uku daga cikin gari 36.

� µaramcin wurin aje kaya na jam’iyyar da kanta: (mangaza 19 daga cikin 22 na yan kasuwa ne alhali, Magaza, abu ce ta dogara da ke kare <ancin jam’iyya. Domin haka, an tafiyar da *o*on bara ta wannan fanni, jam’iyya ta samu magaza shidda.

� µaramcin *arfin noma na mata : A dalilin wasu abubuwa da suka haùa da ayyukan da suka yi ma mata yawa da kuma rishin wurin noma ga mata. Cikin irin matakan da aka ùauka, akwai waye kai daga sarakunan gargajiya don su samu su sa hannu don ciwo kan waùannan matsa-loli. Cikin hanyoyin akwai, samo abubuwan da za su rage ma mata wahala kamar mashin ùin nika da ta surhe da sauransu da kuma turka da take iya kawo masu kuùi domin samun hayar gonakki.

� Rishin amincewa da *ungiyoyin mata a matsayin masu yin ayyukan bashi kan jingina: Don magance rishin halartar mata ga ayyukan bashi kan jingina, jam’iyyar ta yi shawarar aza waùansu gungu uku (na mata, na maza, na jam’iyya). Za a aza komiti mai karçar dala arba’in kan kowane buhu. Kuùin da aka tara za a raba su gida uku. Kishi 50% na kuùin kayan mata da aka tara, sai a ba *ungiyar mata, kishi 50% na kuùin kayan maza da aka tara sai a ba *ungiyar maza. Jam’iyyar sai ta ùauki sauran.

� Kasawar tattaunawa da abokan hulùa masu hannu da shuni ta yadda kowa za ya ci amfanin abun : *ungiyar manoma da jam’iya ce ya kamata su tafi wurin yin jewaya da karçar kuùi, wanda tanadi ya kamata ta yi alhali ko kuùi da riba ba su canza ba. µungiyoyin manoma ya kamata su tattara kuùi su kai ma jam’iyya, ita kuma ta kai ma Tanadi. µungiyoyin manoma ya kamata su tattauna hulùar wannan aiki tare da masu bada lamani game da haka an gudanar da ayyukan ba da labaru da waye kanu a cikin *ungiyoyi mambobin jam’iyya. Jam’iyyar ta samu hanyar ta tafiyar da hulùa tsakaninta da wasu asusun lamani, waùannan an yi masu bayani kan shigar da ayyukan bashi kan jingina bisa fannin tafiyar da ayyukansu.

� Rishin masu tafiyar da horo cikin garuruwa (ma’aikata, horo, da sauransu …) .Gundunmuwar masu hannu da shuni na *etare domin ùaukar mai kula da waye kai, abun da za ya ciwo kan waùannan matsaloli.

� Samun isasshen taki a cikin kasuwannin Nijar : Rarraba taki daga wajen KAIMA, yana samun latti wani bi, ba a samun taki, lokacin saukar damana.

Page 7: Bashi kan jingina na jam’iyyar ci gaba ta garin Konkorindonawa bisa ga zancen bashi tare da TANADI. Masu kula da harakokin kuùi na Tanadi, suna tafiyar da ayyuka na ba da bashi

7

Projet Intensification de l’Agriculture par le Renforcement des Boutiques d’Intrants CoopérativesFAO BP 11 246 Niamey, NIGERTel + 227 20 37 32 [email protected] www.iarbic.net

Projet Capitalisation (FAO Niger)BP 11246 NiameyTel + 227 20 72 33 [email protected]/knowledge/km-gender/capitalisation-bp/fr

Gano *ura*urai

Tasirin da aka samu ta fannin bashi kan jingina zuwa ga masu *aramin *arfi za ya *aru sosai :

� In a ce kowane abokin hulùa ya ba da hannunshi wajen tafiyar da ayyukan bashi kan jingina. Wannan abu, yana bu*atar ba da horo.

� In *ungiyoyin manoma na tushe sun *arfafa halin tattaunawarsu da abokan hulùa masu ba da lamani ta yadda kowa za ya ci moriyar abun, wani lokaci riba da kuùin aje takardu suna da yawa.

� In an samu an ciwo kan matsalolin halayen yanayi bisa ga damana, to ba shakka, husa’o’in noman zamani : inganttacen irin shibka da amfani da taki zamani sun zama hanya ma ‘abuciya

%orewar ayyuka

Wannan husa’a shekara goma da aka san ta a garin Konkorindo, bayan haka ta zama abun koyi ga *ungiyoyin manoma na Nijar da kuma na *asashen waje kamar (Burkina Faso, Mali), lokacin wani taro da aka gudanar a Wagadugu a watan nobamba na 2012.

Jam’iyyar ci-gaba ta karçi fiye da tawaga 10 na <an yawon buùa ido na *asashe kamar su (Benin, Senegal, Mali, Burkina Faso, Ghana, ...) da suka zo domin su ga yadda ake tafiyar da wannan aiki. Dangance da wannan yawon buùa ido *asashe da dama sun amince da tafiyar da wannan husa’a a *asashensu.

Kammalawa

Bashi kan jingina, ya zamanto, aiki ne na jam’iyya wanda ya fi mahimmanci a wurin mutane, maza da mata, masu hali, da marasa hali. Wajen manoma wannan ya zama hanya ta kariyar cimakarsu, wajen masu ba da bashi ta fuskar asusun lamani, wannan ya zama hanya ta çun*asa ayyukansu.

Ta hanyar bashi kan jingina an samu, an *arfafa zumunci tsakanin mace da namiji, dangance da ayyuka daban-daban da ake tafiyar da su, da kuma irin amfanin da ake samu:

« dalilin bashi kan jingina, a yanzu, ina da ayyukan da nike yi (…).ina zuwa kasuwanni dayawa don in saida man gujiya kuma in sayi cimaka , a yanzu , an san ni ko’ina , ina samun ziyara, ana ba ni daraja sosai »; « Ban gadi ba wani filin gona, ta hanyar bashi kan jingina, ina ùaukar <an barema don su yi mani aiki wata manomiya ta garin Gagija.

Sabin ayyukan da aka gudanar da su, bisa ga gudunmuwar asusun Ameli, na taimakawa wajen *arfafa *ungiyoyin manoma na maza, da mata, na jam’iyyar da kuma tafiyar da husa’o’i masu mahimmanci.